HAUSA NOVELZYNAH Hausa Novel

ZYNAH Hausa Novel

Kafin ta yukura ta tashi, bakura ya isa gunta, dukawa yayi a gabanta yana mata dariya, haďe da shafe cikin, yana faďin babyna, kina lafiya?”.

Au babynka kaďai zaka tambaya, ban dani ko?”

Ohh!!! Srry baby, tunda so kike na gaidami miko hannu kiga”.

Taimaka mata yayi ta tashi tsaye, yana rungume da ita suka shiga cikin ďaki, yana faďi nina isa? my mata tana fushi dani, yau kaina zai kwana a wiyata”.

Suna shiga a bakin gado ya zaunar da ita, sannan ya duka a gabanta yana faďin yanzu zan gaisa da matata”.

Yanayin yadda mata maganar ne yasa zynah yace kamar yaya?”

Ido ya kashe mata, ba tare daya jira ta sake magana ba, hannu yasa ya kwamtar da ita, a lokacine zynah taji kamshin turaren jikinsa,  tana buďe baki zatayi magana, da sauri bakura ya tashe mata baki da nasa”.

Bayan suci suyi sallah, mai make-up tazo tayi wa amarya da kawayen amarya, sannan aka yiwa iyayen ango da kawayenta”.

Daga amare har su hjy da kawayenta duk su shirya bakura kawai ake jira, gashi su malah da sauran abokansa suyi ta kiran wayarsa bai daga ba”

Da shike bakura ne kawai yasan bakura yana da mata, hakan yasa ya fara tunanin ko can yaje, ina zuwa kawai yace ma sauran abokan, ciki gida ya shigo gun hjy Khursum,  gefe suka koma a nan ne yake sanar da ita, tun daya suke kiran bakura amma bai daga ba”.

Nan hjy tai takirasa nan be daga ba, gani haka yasa hjy daukar mayafi, tace wa malah zo muje”.

Gida bakura suka nufa, suna isa kai tsaye suka shiga har ciki, da shike yabar kofar a buďe, a falo suna tsaya, malah ne ke sallama”.

Dai-dai lokacin bakura yana fitowa daga wanka, towel ne kawai daure a kugunsa, daya towel ďin kuma yana goge jiki dashi”.

Ji sallama a falo yasa shi fitowa ďan gani mai sallamar, yana fitowa da bakura ne sukayi ido biyu, gefe kuma ga hjy, suna haďe ido da hjy da sauri ya daure fuska kamar ba shib, itama wani irin kallo banza tayi masa haďe da qwafa, ba tare datace komai ba, ido kawai yasa ya fahimci abinda take nufi”.

Da sauri ya koma ciki, dai-dai zynah na fitowa daga nata wanka, tambayarsa tayi da waye?”

Hjy ce tazo”..
Da sauri zynah tace lafiya?”
Eh lafiya qlau, guna tazo, yanzu ma ni take jira, akwai inda zamu, amma komai dare zan dawo”.

Doguwar riga tasa haďe da hijab, da sauri yace ina zaki?”

Zanje na gaida tane”
A’a, ki bari kawai”.
Duk bakura yana maganar ne yanasa kayansa, yana gamawa kamota tayi tayi mata kiss sannan ya fice”.

Ido kawai zynah ta bisa dashi, tana me girgiza kai”.

Tun daga falo hjy ta fata zazzaga masa masifa, inda take fita ba nanne tashi shiga, shidai shiru kawai yayi, malah ne ke bata hakuri”.

Ko kafin su isa, har hjy Ashe su wuce da amarya, da kawayen amaryan”.

Kai tsaye ďakin su Yah-na hjy ta shiga dasu, wasu tsofaffine su uku zaune ďakin daga ganisu kakanninsa ne”.

Suna shiga hjy ta fita, sannan kanwar hjy Khursum ta shigo, ita tasa nakura ya duka gwiwa bibiyu, nan tsofaffin suka ďibi wani abu me kama da lalle, suka fara shafa masa, sunayi suna kawa, *yau ka fita cikin sahun samari, Allah yasa yadda mukazo biki kafin shekara muzo suna haka* amma duk da barbanci sukeyi, suna gamawa daya daga cikinsu ta rangaďa masa guďa akai, a lokacine zuciyar bakura ta karye, fashewa yayi da kuka, gani haka yasa sukaci gaba da yi masa tsiya”.

Saida sukai masa wanka da ruwan turare sannan kanwar hjy ta dauko masa riga da wando ta mika masa, toilet ya shiga yasa sannan ya fito, yana fitowa da kanta ta sanya masa malum-malumn wa gambari light blue, nan suka sake wani guďan, sannan aka bashi izini fito”.

Amarya kuwa har ta gaji da zaman jira, gashi ance kada ta sake ta fito daga cikin motar idan ba ango ya iso ba,  tun tana game har bacc ya fara daukar ta, kamar daga sama taji ance idan kiga daga ki fito muje”.

A yadda bakura yayi mata maganar ta dauka mafarki takeyi, gani ba mafarki bane, shine ďin dai, dole yasa ta fito”..

A sanyaye ta fito, gani duk idanu jama’a yana kansu yasa bakura rike mata hannu har zuwa heght table, nan wasa ya tashi zanga-zanga, gidan uwa da uba su nuna masu gata sosai,  wasa bai tashi ba sai aroud threeAM sannan suka tashi”.

Gidan hjy aka sake meda amarya, shi kuwa ana isa gidan sa ya nufa, yana isa gida, gani zynah tayi zaune tana game a wayarta, daga fuska da zasuyi suka haďa ido da bakura, take taji gabanta yayi mummunar faďi”.

Da sauri ya kariso kan gado, kallo ďaya tayi masa yasata cewa, wannan kayan kuma fa, daga ina kamusu kamar wani ango?”

Bakura yayi kamar baiji abinda take ba, hannu yasa ya amshi wayar dake hannunta ya ije agefe, sannan yace my zynah magana nakeso muyi dake amma da sharaďi”.

Zynah tace sharaďi kuma?”
Eh sharaďi”.

Saida ta tattara hankalinta gu daya haďe da zuba masa ido, sannan cewa ina sauraronka”.

Saida da ya mike ya cire malum-malum ďin dake jishi sannan ya dawo ya zaune, suna kallo juna hannu yasa ya kamo mata nata, shiruuuuu yayi na ďan wani lokaci, yana tunani ta ina zai fara mata bayani, kuma idan ya faďi mata, yaya zataji, gata da tsohon ciki, gashi nasha ji ana cewa ba’aso a rinka faďi masu abinda zaita masu da hankali”.

Kodai na bari har Allah ya sauketa lafiya ne, saina faďi mata? To idan tazo taji a wajan wasu kuma fa? Kai gara kawai na faďi mata da kaina zafi sauki da ace wanine ya gaya mata”.

Maganar zynah ce ya dawo da bakura daga tunanin da yakeyi, tace ina sauraranka”.

Dan Allah zynah inaso kiyi wa magana ta kyakkyawar fahimta, wlhy nima kaina dan babu yadda na’iya ne, kinsan duk abinda akafi karka akai dole kayi hakuri, kuma nasan ba komai yasa su hjy da daddy sukayi min haka illa sabida abinda na aikata ne,amma nidai dan Allah inaso ki fahimceni dan Allah my zynah”.

Nasan ba lalla bane kiyi amanna da abinda zai fsďi maki, amma ni nasan har ga Allah gaskiya ne, kuma har cikin zuciyata”.

Zynah kin riga kin zama wani sashi, ko nace reshe a cikin jikin rayuwata, wanda nake gani idan ba dake ba, a gaskiya zan samu nakasu, ki fahimceni wlhy Allah ma sheda ne, banyi haka dan ci maki fuska ko wani kanci ba, nima kaina Allah ya gani tirsasani akayi”..

Cikin sojin da lilin da yasa yake jiro mata wannan zancen tace, babu komai daka ka damu”.

Saida yayi shiruuu na ďan wani lokaci sannan yace, ina ranar dana sallameki, zan tafi gida maiduguri ďin nan?”

Eh”.
To maganar gaskiya duk abinda abinda na faďi maki ba gaskiya bane, maganar gaskiya shine, tun ranar da daddy ya dawo, hjy tayi masa magana akan aurenmu, shine daddy yace, tunda nayi abinda dakeso,dan haka suma bazan hanasu abinda suke soba, akan yasa suke yanke shawarar auramin er’kanwa hjy”.

Zynah ban masu musu ba, sabida nasan idan har naki yarda to karshenshi nasan zasuce sai dai mu rabu dake, ni kuma Allah ya gani, bazan iya rabuwa dake ba, kinji dalilin amincewa ta kenan”.

Amma dan Allah kiyi hakuri ki yafe min, na boye maki da nayi,plss”.

Duk da zynah najin babu daďi a zuciyarta,amma gani halin da mijinta ke ciki yasa ta ďanne nata damuwar,cikin nuna rashin damuwa tace ďan dan wannan shine duk zaka damu kanka?”

Da sauri bakura ya daga kai yana kallonta”.

Idan sabida nine kada ka damu, babu komai, nina kaina nasan mu tafka kuskure domin bamu kyauta ba,shi isa duk abinda hjy tayi bani gani laifinta, domin ba hjy kadai ba, kowaye ďansa yayi masa haka, ba zaiji daďi ba, musamman ma idan kayi la’akari da babbacin dake tsakanina dakai, kai ďan wanine, ni kuma ba er’kowa bace,bakura nikaina nasan kai ba sa’ar aurena bane, wlhy harga Allah nayi nadamar abinda muka aikata”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button