Labarai

Ƴan Sanda Sun Cafke Malamin Makarantar Da Ya Kashe Amininsa Ɗan Sibil Difens Ya Jefa Gawarsa Rijiya A Katsina

Ƴan Sanda Sun Cafke Malamin Makarantar Da Ya Kashe Amininsa Ɗan Sibil Difens Ya Jefa Gawarsa Rijiya A Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Rundunar yan sanda ta jihar Katsina ta yi nasarar cafke malamin makaranta, Laminu Saminu mai shekara Ashirin da tara da haihuwa dake Bakin Kasuwa a karamar hukumar Mani ta jihar Katsina, da ake zargi da kashe abokin karatunsa a Kwalejin Horas Da Malamai Ta Gwamnatin Tarayya dake Katsina kuma jami’in Tsaro na farin kaya (NSCDC) ASC II Sanusi Bawa har Lahira.

Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya bayyana haka a cikin wata takardar manema labarai, inda ya ce a ranar 26 ga watan Nuwamba na wannan shekarar, ya yaudari abokin na sa zuwa wani kango dake karamar hukumar Mani, ya umurce shi da ya ajiye motarsa kirar Golf a wajen kangon, inda ya ba shi hura da guba a Ciki, wanda sakamakon shan fura ya fita hayyacinsa, inda ya cigaba da bugun kansa da icce har sai da ya rasu kuma ya jefa gawarsa cikin rijiya kuma ya bi da yashi duk da ya sace ma shi Mota.

Alhaki ya sa ya kira matar abokin na sa da ya kashe yana buƙatar da ta ba shi takardun motar, jamian tsaro su kai ta bibiyarsa har suka samu nasarar cafke shi kuma ya amsa laifin kashe abokin.

An samu jikka ledar guba da katon iccen da ya dunga buga masa a kai da motar kuma ana cigaba da Bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button