Labarai

Ɗalibai na barazanar zanga-zanga idan ba a saki Aminu Muhammad nan da awa 48 ba

Ɗalibai na barazanar zanga-zanga idan ba a saki Aminu Muhammad nan da awa 48 ba

 

Kungiyar Daliban Najeriya ta NANS ta bai wa jami’an tsaron kasar wa’adin kwanaki biyu, awa 48 kenan, da su saki dalibin nan da ake zargi ya ci mutuncin matar Shugaban kasa a shafinsa na sada zumunta.

 

Kama Aminu Muhammad ya haifar da cece-kuce musamman a kafafen sada zumuntar kasar, inda da dama ke ganin rashin kyautawa da yi wa doka karan tsaye wurin tsare dalibin ba bisa ka’ida ba.

 

BBC Hausa ta rawaito cewa anjima kaɗan a ke shirin gurfanar da Muhammad.

 

Wani kusa a kungiyar ta NANS Bashir Limanci, ya ce za su shirya zanga-zanga idan har aka ki sakin shi.

 

Aminu mai shekaru 23 na karatu ne a jami’ar tarayya da ke Dutse, inda ake shirye shiryen fara jarabawa.

 

Kawo yanzu babu martanin hukumomin tsaron kan gargadin na NANS, in ji BBC.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button