ƘWAI cikin ƘAYA 8
????ƘWAI cikin ƘAYA!!????
Bilyn Abdull ce????????
BOOK ONE
Shafi na takwas
______________
………..Shigowata soron gidanmu yaɗan sakamin nutsuwa kaɗan, dan yau babu mahaukacin kiɗannan, sai da nai addu’a kafin na shiga da sanɗa tamkar wadda tazo yin sata.
Wata sassanyar ajiyar zuciya na kuma saukewa ganin ƙofarsa a rufe, sannan babu kowa a cikin irin yaransa, sai wasu a tsirarun matan gidanmu dake ƴan aiyuka a tsakar gidan.
Abinda ya bani mamaki yanda duk suka zubamin ido kamar wata baƙuwarsu, ni dai sannu nai musu na wuce ɗakin innar Firdausi kai tsaye.
Sannu Firdausi da inna dake zaune sukaimin, na amsa ina ƙirƙiro ƴar fara’a akan fuskata tare da bin tarin kayanmu da aka jibge gefe da kallo.
Kafinma na tambaya firdausi ta fara min bayani,
“Bilkeesu kayanmu ne baba yace mu kwaso da ga baca mu maido nan, dan babu dacewa zamanmu acanɗin saboda canjin da gidan ya samu”.
Murmushi nayi sosai wanda ya bayyana farin cikina yanzun kam, na zauna kusa da Firdausi ina faɗin, “Amma inna idan mun dawo nan baba fa?”.
“Karki damu kinji Bilkisu, babanku zai cigaba da kwana a bacar shi, kwananku acan babbar barazanace a garemu da mutuncinku, waɗannan yaran sam zukatansu basusan yaren tsoron ALLAH ba, abinda ransu keso kawai suke ji da gani a gaba ɗaya duniyarsu”.
“Hakane inna, babu abinda zance daku nidai a wannan duniyar, ALLAH ya yalwata rayuwarku da dukkan farin ciki har cikin aljanna, kun haska fitila a rayuwata lokacin da tsatona suka kashe domin hana kansu ganin hanyar da zasu riskeni, kuɗin masu zinariyar zuciyace mai haske fiye da ta dayimon (diamond), na…….”
Katseni inna tayi saboda kukan daya sarƙe harshena, ta jawoni jikinta tana bubbuga bayana alamar lallashi
“Ya isa haka bilkisu, kema ɗiyarmu ce tamkar Firdausi, ki daina kallonmu a waɗanda sukai miki alfarma, muna yin abinda ya dace muyine kinji”.
Kaina na jinjina mata ina sharce hawaye.
Kusan tsawon mintuna uku tana lallashina, kafin na miƙe na cire Uniform ɗina naje naɗan watsa ruwa, bayan na dawone na iske Firdausi ta ajiye mana abinci.
Munacin abinci inna na zaune gefe tana ƙullin kayan sana’arta, Firdausi ta haɗiye abincin bakinta tana faɗin, “Bilki akwaifa matsala”.
“Tsayawa nai da ga ƙokarin kai abincin bakina ina kallota a tsorace”.
Inna ta harari Firdausi tana faɗin, “K Firdausi bana son ƙirƙire-ƙirkire fa, ya zaki ɓata mata zuciya? Wannan ai shirmene”.
“Kiyi haƙuri inna” Firdausi ta faɗa a sanyaye.
Kallon Inna nayi nima a raunane, “Inna dan ALLAH karki hana ta sanarmin, da inji a wani waje ai gara naji daga gareku, dama tunda na shigo naga matan gidannan namin wani kallon ƙurullah daya tsoratani”.
Murmushin takaici Inna tayi tana girgiza kanta, “Suma son zuciyane ke ɗawainiya dasu, dan abinda ya shafi kowane a gidane ai”.
“Dan ALLAH Inna miya faru?”.
“Karki tada hankalinki Bilkisu, baƙon gidanmu ne ya tara taro ɗazun bayan fitarki makaranta, ya kafa sharuɗa ne a gidan, wai bayason hayaniya, sannan kafin ya tashi barci a share tsakar gidannan a wanke tare da bayi, lokacin da zai fito kuma karyaga kowa sai…….”
Tai shiru cikin haɗiye wani takaici daya zame mata ƙululu a maƙoshi.
Cikin ƙaguwa da tsorata nace, “Inna sai me?”
Shiru tai ta kasa bani amsa, sai Firdausi dake sharar hawaye tace, “Wai sai mu ƴammatan gidan kawai, kece zaki ringa masa gyaran ɗaki, ni kuma kai masa ruwan wanka, su Aina’u ma kowa da aikinta, kinsan miya bani takaici Bilkisu?”.
Kaina na girgiza mata saboda hawayen da suka fara gudu a kumatuna. Ta goge nata itama tana cigaba da faɗin, “Bayan wannan dokokin harda sharaɗi mai barazana ga duk wanda yace zai bar gidannan ko zai sanarma hukuma, wai amma dukda wannan ruɗanin sai su Zee ke murna, harma suna ƙokarin yin kwarkwasa a gabansa”.
Kasa cewa komai nayi, sai tsame hannuna danai daga abincin da mukeci na koma gefe, hakama Inna da Firdausi kowa yay shiru yana cuɗawa da kwance abinda yakeji a ransa.
★★★★★★★
Kamar yanda Jazuga ya kafa dokoki a gidanmu haka kowa ke bi, ba komaine yasa hakanba sai tsoro, dan ba gidanmune kawai ke tsoron Jazuga ba, gaba ɗaya layinmu a tsorace suke dashi da yaransa, babu wani mai sukuni, dan yaran Jazuga sun addabi kowa a anguwar, gashi sai ƙara jan yara matasa ya keyi masu rauni cikin tawagarsa.
Abinda zai baka mamaki Police kansu tsoron shigowa anguwarmu sukeyi, ballema muyi tunanin zasu iya kamashi ko ƙwatar mana ƴanci daga mulkin mallakarsa.
Tun ina damuwa da bautar gyaran ɗakinsa har abin ya zame min jiki, ƙa’ida kullum sai na gyara sau uku, safe, rana, yamma.
Abinda kawai ke damun rayuwata dashi shine kallo, duk motsina a gidan idonsa na kaina inhar yana gida, duk da kuwa a koyaushe cikin Hijjab muke ni da Firdausi inhar zamu fito tsakar gida.
A cikin ƴammatan gidanmu kuwa wasu sai dai addu’a, dan kuwa sosai ake zargin Jazuga na lalata dasu yana basu kuɗi, hakanne ke ƙara tada hankalin iyayenmu.
Muna cikin wannan halin ne kuma saiga ɗan uwansu Firdausi wanda yake matsayin zaɓin iyayenta yazo daga can asalin garin su Firdausin, canjin daya tarar a gidanmu ne ya tayar masa da hankali, dan haka ya roƙi baba akan kawai a saka musu ranar aure.
Na taya Firdausi murna, sannan na taya kaina kuka, dan kuwa koba komai itakam ALLAH ya tsameta, niko da ko saurayi ban taɓa yibafa? Kunsan samarinma sunfi son ƴammatan masu ƙyale-ƙyale, niko bani cikin jerin masu shi, wadda suturar sakawa bata wadaceta ba ina taga kayan ƙyale-ƙyalen burge saurayi.
Saurayin Firdausi bai bar garinba sai da aka tsaida maganar aurensa da Firdausi wata biyu kacal..
Rayuwa a gidanmu ta cigaba da tafiya a ƙuntace, komai yabar mana daɗi saboda su Jazuuga, abu mafi ɗagamin hankali shine saka idonsa a kaina fiye da kowa a gidan, wani salon iskancima da ya ɓullo dashi shine danaje gyara masa ɗaki shima zai shigo ya zauna yana kallona kamar wata tv, narasa miyake kallo tare dani, ni dai sam baza’a sakani a jerin ƙyawawa ba, dan kuwa baƙace ni, bani da dogon hanci, bani da kayan ƙawa na ado da zasu fidda ƙyauna ga kowa. Shiyyasa lamarinsa ke ban mamaki da al’ajabi.
Babban abinda na riƙe shine addu’a, dan itace babban makamina a gareshi.
Yauma kamar kullum na tashi da wuri saboda zanje makaranta, dukkan abinda ya dace muyi ni da firdausi munyisa, hatta da aikinta da Jazuuga ya bata nakan tayata, saboda ni nawa saiya tashi barcinsa na ƙaddara da ko sallar asubahi bana tunanin yanayi.
Shirin makaranta nayi, na dawo ƙofar ɗakinmu na zauna tamkar yanda sauran ƴanmata gidan suka fito, wasu sunci kwalliyarsu saikace wasu matansa, sai binmu da kallon banza suke, dan a ganinsu bamukai matsayin haɗa kafaɗa dasuba.
Sukan bani dariya da mamaki, dan inda son samunanema wlhy ni namu aikinma duk ya haɗa ya basu.
Banfi mintuna goma da zamaba sai gashi ya fito, kamar yanda ya saba da ga shi sai gajeren wando, kallo ɗaya nai masa na duƙar da kaina.
Shiko inajin yanda idanunsa ke yawo a jikina tamkar kullum.
Hazbilannahu wa ni’imalwakil na shiga ambatowa a kan laɓana, kamar yanda na fahimta a duk sanda nake karantata ko kallona yake saiya kauda idonsa sai naga yanzu ma yazo ta gabana ya gitta.
Inajin yanda su Aina ke masa gaisuwa cike da kwarkwasa da salo, tausayinsu ya kamani, dan kuwa ni nafi ɗaukarsu a jerin masu karancin tunani, da wannan takaicin na miƙe na nufi ɗakinsa, kamar yanda na saba a gaggauce na shiga gyarawa, dukda nasan bazai shigoba sai yay wanka, kafin lokacin kuma insha ALLAHU na gama nama fice abina zuwa majaranta.
Abinda na gani a ɗakin yauma ya tayarmin da hankali, dan haka na fice jiki na rawa ko shara banyiba, saboda tsantsar tsoro da firgici dake sake tasirantuwa a gareni game da tsagerancin Jazuga.
Ranarma dai ko’a makaranta daka ganni kasan babu nutsuwa a tare dani, haka dai aka tashi na nufo gida, ashe nabar baya da ƙura akan rashin shara da banma Jazuga ba…….????
____________
JAWAAD
____________
Izinin shigowa aka bashi, ya turo ƙofar ya shigo, cikin risinawa irin ta girmamawa yake faɗin, “Sir! Ƴan jaridar nanne suka sake dawowa”.
Shiru Sir Ahmad barewa yay yana kallonsa na tsawon sakwanni, kafin ya sauke numfashi da masa alamar yaje.
Bayan fitarsa ya maida kallonsa ga Jawaad dake kallonsu ba tare da ya fahimci komai ba.
“Jay! Rayuwa na bani mamaki, bansan miyasa a duk lokacin da case irin wannan yazo ba hankalin duniya yafi tashi akansa, shiyyasa talakawa har abadan bazasu daina ƙalubalantar manyan ƙasa ba komai gaskiyarsu”.
Murmushi Jawaad yayi irin na takaici, yaɗan lumshe ido yana faɗin, “Kuskuren daga mu yake Sir”.
“Jay miyasa kace haka?”.
Murmushi ya sakeyi mai ciwo, “Abun a bayyane yake muma mun sani sir, mubar wannan maganar kawai bata da muhimmanci a yanzu”.
Kai Sir Ahmad ya jinjina kawai yana cije baki, sai dai acan ƙasan ransa maganar Jawaad tai mugun sukarsa, ba komai ya sa hakanba sai sanin tsantsar gaskiyar Jawaad, amma wasu dalilai bazasu bar muryoyinsu ɗaguwa ba har suyi kururuwar da duniya zataji, ta gaskatasu cikin jerin jami’an tsaro masu gaskiya da son shinfiɗata..
Ya sauke numfashi mai zafi yana maida hankalinsa ga Jawaad, “Jay waɗanan ƴan jaridane, tun safe suke jera mana kira domin sonjin mi’ake ciki, inaga yakamata kaje garesu”.
“Okey Sir”
Jawaad ya faɗa yana miƙewa, gaba ɗaya fuskarsa ta canja launi, sam babu ɗigon fara’a ko sauƙi a cikinta, sai tsumamman fushi mai gauraye da takaici irin mai zafafa zuciya.
Harya fice Sir Ahmad na binsa da kallo, yana ƙaunar yaron saboda nagartarsa, duk da mahaifinsa yay suna irin na zama wani shi sam baya alfahari da hakan, ko yaushe tunaninsa akan talaka yake, da ace yanda Jawaad keda zinariyar zuciya haka sauran jami’an tsaro suke da tuni ƙasar ta canja daga yanda take yanzu.
Koda Jawaad ya fito sai ya samu Qaseem tare da ƴan Jarida, kallon ido cikin ido sukaima juna. Jawaad ya janye nasa yana sakin wani lallausan murmushin daya soki zuciyar Qaseem.
Office yay wucewarsa, ransa na susa akan shirmen Qaseem, baisan miyasa sam jininsu bai haɗuba.
Cikin kujera ya shige yana mai lumshe idanu da faɗawa duniyar dogon tunani.
Damuwa tai masa ɗaurin gori, saboda sabgogin aiki, ga matsalar gida na halayyar matarsa da taƙi ta zama irin kowacce mace, waje zafi, gidansa ƙunci, babu uwa ko uba da zasu fuskanci matsalarsa kai tsaye balle su taimakesa koda da shawarane.
Ina zaiga mahaifiyarsa? Shin tana raye ne kokuwa shiɗin marayane gaba ɗayansa? Wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro a kumatunsa, bai damu daya sharesuba, haka ya barsu suna kwarara. (Haka yake dama, aduk lokacin daya tuno iyayensa yakanyi kukansa ya ƙoshi).
Ya rabbi ka gafartama iyayenmu baki ɗaya????????????.
Sai da yasha kukansa ya more sannan ya share hawayensa.
Nutsuwa yay ta musamman domin yin nazari akan wannan case da aka damƙa a hannunsa, dolene idan yanason aikinsa ya tafi dai-dai sai ya nemo abokansa, aminansa sun dawo kusa dashi, kuma insha ALLAH zaiyi komai da kula yanda bazai ƙara bada wata ƙofa da za’a farraƙasu ba koda na a awoyine.
Bai ɓata lokaci ba a take ya rubuta takardar neman izini tare da shawarar da yay alƙawarin badawa kamar yanda sukai da Sir Ahmad……………✍????
https://www.youtube.com/channel/UCl9IGLUXrqUtta-Tjmhoo7Q
MANHA HAUSA NOVEL’S takuce, maza garzaya domin bada gudunmawarka, danna Subscribing domin nuna ƙaunarka garemu????, kuyi shiri na musamman domin samun daɗaɗan shirye-shiryenmu tare da nagartattun labaran novel’s masu daɗi da ma’ana nan da lokaci ƙanƙani, MANHA HAUSA NOVEL’S ta shirya tsaf domin baku farin ciki insha ALLAHU, ku garzaya kada ƙuda ya rigaku????, Bilynku ma har taje tayi subscribing tun farar safiya, goyon bayanku shine ƙwarin gwiwarmu????????????????.
MANHA HAUSA NOVEL’S
(Ƙyautar ALLAH).
Ku isa da hanzari domin samun ƙyautar kuma, dan ALLAH a danna subscribing????????.
Ga link ɗin can a sama????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????