NOVELSUncategorized

KWAI CIKIN KAYA 9

????ƘWAI cikin ƘAYA!!????


                    Bilyn Abdull ce????????

              BOOK ONE
                     Shafi na tara
______________
…………Tun ƙarfe huɗu na maraice garin ya fara haɗa gagarumin hadari, wanda alamominsa suke nuna zai zubda ruwa mai yawa.
        Duk da yana a office hakan bai hanashi fahimtar canjin da garin ke cikiba, miƙewa yay zuwa jikin window ɗin Office ɗin ya leƙa, tabbas hadarine mai ɗauke da alamomin iska kuma, ya kalli
agogon dake a tsintsiyar hannunsa yana huro iska a bakinsa, yana da sauran ayyuka, gashi bayason ruwannan ya samesa a waje.
     Barin Window ɗin yayi ya koma gaban desk ɗinsa, wasu takardu ya haɗa waje ɗaya kafin ya fito da ga office da hanzarinsa irinna masu cikakkiyar lafiya.
         Kai tsaye Office ɗin Sir Ahmad ya nufa, dan tun kusan mintuna goma baya ya aiko kiransa, bai fita bane saboda wani ɗan aiki da ya sakashi yakeson ƙarasawa ya kai masa gaba ɗaya.
       Sallama yay a ƙofar Office ɗin kafin ya shiga, su uku ya iske a office ɗin, gaba ɗayansu kuma suna cikin manya-manyan ƴan sanda, gaisuwa yay irinta girmamawa a garesu, ya miƙama Sir Ahmad takardun yana faɗin, “Sir gasu na kammala, kayi haƙuri da lattin da nayi, na ƙarasa aikinne”.
     “Babu damuwa Jay, dama tunanina ya bani hakan shiyyasa ban damuba, duk da kuwa jiranka muke”.
         “Sorry Sir’s” Jawaad ya faɗa yana maida kallonsa ga sauran mutane biyun dake zaune .
         Ɗaya a cikinsu ne yay magana fuskarsa sam babu walwala, cikin tsare Jawaad da idanu yace, “Jawaad Abdul-aziz ko?”.
          Cikin girmamawa Jawaad yace, “Yes Sir!”
       Zama wancan ya gyara sosai yana fuskantar Jawaad, ya fara magana cikin dakiya da kuma tsuke fuska.
         “Jawaad kai ɗan sandane, ɗan sandanma (SAS) ƙwazonka da ƙwarewar aiki ke ƙara maka ɗaukaka ga kowa dake a cikin hukumarnan, kamar yanda muka baka yarda a baya yanzunma munason ƙara baka a kan wannan aikin, dan tabbas inaji a jikina zaka iya, saboda kanada NAGARTA irin ta jami’an tsaro na ƙwarai, bamason wannan case ɗin ya wuce sati biyu, ya kake ganin zaka iya kuwa?”.
        Jawaad dake tsaye a tsume fuska sam babu fara’a yay ajiyar zuciya yana sake tsuke fuskarsa, “Sir insha ALLAHU ina fatan hakan, sai dai bazan zama mai alƙawari akan abinda bani da ilimin sanin gaibu a kansa ba, ina dai muku albishir da koda ƙasa da kwanakin da aka banine zan iya yin hakan, alfarma ɗaya zuwa biyu nake nema a gareku, dan hakanne zai bani ƙwarin gwiwa akan nasarar da kuke fata daga gareni…”
        “Wace alfarma ce wannan?”.
      Ɗayan a cikin baƙin yay tambaya yana kallon Jawaad.
           Gyara tsaiwa Jawaad yayi yana satar kallon Sir Ahmad, Sir Ahmad da shima ke kallonsa ya jinjina masa kai alamar ya faɗa.
         Kai Jawaad yaɗan ɗaga masa, kafin ya maida hankalinsa sosai garesu yana cigaba da faɗin, “Alfarma ta farko itace inason a dawomin da abokan aikina tare dani, ina magana ne akan, Hafeez Umar, Aliyu S marwa and Jabeer Abdul-razaƙ. sai alfarma ta biyu kuma kununa ma abokan aikina cewar kun cireni da ga wannan case ɗin, a ɗora Qaseem Ali matsayin jagora, nikuma zanyi nawa aikin ne ta ƙarkashin ƙasa tare da abokan aikina ba tare da kowa yasan muna tareba”.
       Shirun da yayne ya basu damar fahimtar ya kammala magana, hakan yasa su duka suka sake zuba masa ido tamkar wani baƙonsu, kusan minti ɗaya da rabi kafin ɗaya a cikinsu ya miƙe, kafaɗar Jay ya dafa yana murmushi da fadin, “Jawaad tunaninka mai ƙyaune, kuma hakan yamin ɗari bisa ɗari, abu ɗaya nake tsoro da shakku akan dukkan bayananka”.
        Cikin izza da jin yakai jarumin na gaske ya ɗago kai yana kallon boss ɗin nasa, sai kuma ya sake wani lallausan murmushi da ya saka kumatunsa duka biyu loɓawa, “Sir! Miyasa kakejin shakku?”.
        “Gudun rashin samun nasara, ina gudun yazam ba’ai nasaraba akan tsarinka Jawaad, dan rashin nasara a aikinnan tamkar zubewar mutuncinmu ne, samun nasara kuwa kimace a garemu, sannan kowannenmu kuwa ribace a gareshi, kuɗi zasu jiƙamu, sannan zamu ƙara nagarta a idon duniya harma da shugaban ƙasa”.
       “Hummm” Jawaad ya faɗa a can ƙasan maƙoshi, kafin ya kallesu gaba ɗaya cikin takaici, “Insha ALLAHU zamuyi nasara, domin inaji a raina da NASARA AKE FARAUTO NASARORI a rayuwa, insha ALLAHU a karon farko da nake hangen samun damar farko zan sadaukar, badan komaiba sai dan farauto nasara ta gaske, abinda kawai nake buƙata a gareku goyon baya”.
     “Mun baka kuwa Jay”
Sir Ahmad ya faɗa fuska ɗauke da murmushi.
      Ƙamewa Jawaad yay tare da yin Salute nasu baki ɗaya.
         Sun bashi izinin tafiya, duk da kuwa maganarsa ta ƙarshe tai musu tsaye a zuciya, sam sun kasa fahimtar komai a kanta, domin dai hausace cikin hausa yayi.
           Da tabbaci na dawowar abokansa uku garesa a safiyar gobe ya fita, koba komai ransa yay masa daɗi idan ALLAH ya kaimu gobe iyanzu yana tare da aminansa, ƙashin bayan jarumtarsa.
          Duk bin ƙwankwantonka baka isa fuskantar yanayinsa ba, dan fuskarsa jarumar fuskace ma’abociyar adana komai, Office ya koma, cikin hanzari ya haɗa komansa. 
        Yana fitowa Gimba ya ƙaraso gareshi, jikkan hannunsa ya amsa suka nufi mota.
         Kowa yasan Jawaad mutumin kirkine a hukumarsu, sannan jajirtacce akan aiki, sai dai sam baya ɗaukar wargi, yakanyi wasa da dariya da mutane idan yaso, amma kaɗan daga aikinsa ya birkice ka kasa gane kansa cikin ƙanƙanin lokaci.
         Gimba ya buɗe masa baya ya shiga, sannan ya koma ta ɗayan ɓarin ya ajiye masa jikkarsa a gefensa, mazaunin driver ya koma  yay bismillah tare da tada motar suka fice daga station ɗin.

      Luff Jawaad yay kwance jikin kujera, ƙwaƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ne kawai ke faman aiki a lokaci ɗaya, hakan yasashi barin duniyar mutane ya koma zuwa wata duniyar ta daban.
                    Tun a shigowarsu farkon Layinsu ya buɗe idanunsa, da motar ɗaya da ga cikin kawunansa ya fara cin karo, ya tsurama motar ido tamkar yaune ya fara ganinta.
      Har aka wangale musu ƙaton gate ɗin family House ɗin suka shiga bai daina bin motar da kalloba.
           Sashin su Jawaad yana daga can ƙarshen gidan, hakan yasa saiya wuce dukkan sashin kawunansa kafin yaje nasun, umarni ya bama Gimba akan ya tsaya inda Kawu Nasiru yay fakin.
        Kusan a tare suka fito da ga motocin, fuskar kawu Nasiru washe da murmushi yana kallon ɗan ɗan uwan nasa.
       “A’a Jawaad har an taso aikin yau da wuri haka?”.
      Guntun murmushi Jawaad yay yana ɗan shafa kai, ya rissina a gabansa yana faɗin, “Eh kawu mun dawo, ina yini”.
       “Lafiya lau, Ja’iri kai dai kayi wuyar gani, muna a gida ɗaya amma sai mutum ya jera wasu kwanaki bai ganka ba”.
      “Ai min afuwa kawu, aikin namune sai addu’a, a koda yaushe mutum bashi da lokacin kansa, ni kaina inason kasancewa a cikinku a koda yaushe, amma hakan bai samuwa”.
        “ALLAH sarki karka damu, ai ka cancanci uziri ga kowa Jawaad, amma dai a rinƙa daurewa ana shigowa kaji, musamman ma tsofaffinnan kullum zancensu na gareka, a daure ana zagayasu akai-akai”.
         “Insha ALLAHU kawu zan gyara, zuwa anjima duk zan shiga na gaishe da kowa”.
      “To Alhmdllh, ka gaishe da baturiyar matar taka mai cika mana gida da kiɗa”.
       Murmushin kan laɓɓa kawai Jawaad yay yana miƙewa, ya buɗe mota da kansa ya shiga, Har gaban sashensu Gimba ya tsaya da motar, yazo da sauri ya buɗema Jawaad motar ya fito.
       Sai da ya rakashi da jakarsa har gaban ƙofar falonsu sannan Jawaad ya amsa yana ɗaga masa hannu ya shige.

             Idanunsa ya rumtse da ƙarfi saboda su Shahudah dake baje a falo ita da ƴammatan gidan, ga mahaukacin kiɗa na tashi a sifiku, wasu na rawa wasu na zaune wasu kuma a kwance cikin kujera.
      Sam babu wanda a cikinsu yaji sallamarsa balle motsin buɗe ƙofa.
         Taku yake a hankali har gaban kayan kiɗan yasa hannu ya kashe, tsitt falon yayi.
          Gaba ɗayansu a firgice suka maido kallonsu gareshi, kafin kace mi an fara ƴar reran gudu ta ƙofar kichin, wasu kuma ta ƙofar falon.
         Shahudah da ke kwance ta ɓata fuska tana masa kallon takaici.
       Koda suka gama fita baice mata uffanba, kallo ɗaya yay mata yay hayewarsa sama inda zai iske ɗakinsa.
           Tundaga hawowarsa step ɗin farko ya fahimci Batool ko Nabeelah wani yazo yay gyara, hakan saiya ɗan rage masa fusatar da yayi.
      Ɗakin barcinsa ya zarce kai tsaye, yana shiga ya maida ƙofar ya rufe tare da murza key dan karma Shahudah ta shigo.
     Ɗakin yay ƙal saboda gyaran da ya samu, sai ƙamshi mai daɗi ke tashi ga iskar hadari da ke bada ƙamshin ƙasa.
        Tamkar jira ake ya zauna ruwa ya fara sauka a hankali.
          Yana zaune a bakin gado yana zame takalminsa yakejin bugun ƙofar da Shahudah ke masa, baiko kalli ƙofarba balle tasamu darajar kulawa yay shigewarsa bayi bayan ya cire komai na jikinsa, sai ƙaramin wando da ya bari.
           Gaba ɗaya yarasa wane irin mataki ya dace ya ɗauka akan Shahudah ne ta dawo hankalinta, shi yama fara tunanin ko bata da isashshen hankaline, dan sam baiga abubuwan masu hankali tattare da ɗabi’unta ba, ko ada can yasan bata da kirrki sam, amma zaman watanni bakwai da sukai a tare ya sake fahimtar dashi sanin da yay mata a baya ƙaramine ashe.
         Rai a ɓace yay wankan harya gama ya fito, baiji motsinta ba, hakan yasashi gane tayi fushi, ya taɓe baki irin na rashin damuwa da hakan.
       Zuwa yanzu ruwa ake zugawa sosai, hakan yasa yay sallarsa ta magriba a ɗaki, bayan ya idar mai makon ya zauna tunani sai ya ɗauki Qur’an ya hau karatu cikin nutsatstsuyar muryarsa.
     Bai matsa a gunba har sai da aka kira isha’i, har sannan kuma ruwan saman ake zugawa.
       Wayarsa dake ring tun yana salla ya ɗauka, ganin Umma Bara’atu ce sai yay murmushi (Umma Bara’atu ƙanwar mahaifiyar Jawaad ce, karku manta a labarinsa ya nuna mana tana da ƙanne har uku duk mata).
       Cikin girmamawa ya gaisheta, da ga can ta amsa masa cike da kulawa.
        Bayan sun gama gaisuwarsu take tambayarsa koya ga abinci?.
       Murmushi mai sauti yayi, wanda har tana jiyosa, ya kwanta rigingine a gadon ƙafafunsa na ƙasa, “Yanzu nan Umma bazaki daina walar da kanki wajen aikomin abinciba kamar wani ɗan primary ”.
      Dariya tayi daga can, cike da son tsokanarsa tace, “Yo miye banbancinka dasu Jawaad, ni a gurina ai tamkar tata kake, bama ni na aiko da abincinba, ƴar uwarka ce tayisa shine tabama Nabeelah da taga zatazo tace ta kawo maka, sai kuma Nabeelar ta iske bama ka gidan ka fice”.
          “Ayya, ALLAH sarki Sister, na gode mata kuwa, ALLAH ya bata miji na gari wanda zai kulamin da ita, wlhy kiran gaggawa na samu da ga Office Umma shiyyasa na fice bata iskeniba”.
        “Aini wannan aikin naka dan banda yanda zanyine, amma da ga ni har Auta da Amina bama sonsa sam, sai dai muna maka fatan alkairi a cikin, tunda kullum baba shi baya ganin laifinka”.
      Guntun dariya Jawaad yayi, da gani kasan hirar ta sakashi nishaɗi, dan a ransa ji yake tamkar yana magana ne da mahaifiyarsa, “Karku damu Umma’s ɗina, addu’arku ita nafi buƙata, harma kinsa na tuna da Tsoho, insha ALLAH da safe asubanci zan masa naje shan saurar furarsa”.
          “Ja’iri, zaka fara ko? To sai anjima”.
      Sosai Jawaad ya ƙyalƙyace da dariya, ya shiga faɗin, “Haba Ummana karmuyi haka dake, tsaya kiji……”
      Ƙitt ta yanke wayar da ga can itama tana ƙyalƙyata dariya.
         
       Sumbatar wayar Jawaad yay a hankali yana kuma faɗaɗa murmushin fuskarsa dajin ƙarin ƙaunar ƙannen mahaifiyar tasa, masu ƙoƙarin share kukansa a koda yaushe._________
BILKEESU
________


        Naji daɗin shigowa gida na iske su Jazuga basa nan, ɗakinsa a rufe.
     Firdausi kawai na iske a ɗakinmu, Inna ta fita maƙwafta yin barkar haihuwa.
        Tagumin da Firdausi tayine na janye, ta ɗago a firgice tana kallona, ganin nice sai ta sauke sassanyar ajiyar zuciya.
      Murmushi nayi ina faɗin, “Matsoraciya kin zata waye da?”.
          “Ƴan ta’addan gidanmu mana, wlhy wannan rayuwar ta fara gundirata Bilkisu, nifa yanzu ko shakkar banzan nan banayi balle tsoro, dan nakula ibilis ne kawai ya rikiɗa a mutum ya shigo mana gida”.
      Ido na zaro waje ina waige-waige, a tsorace nake magana ƙasa-ƙasa, “Firdausi bar irin maganarnan dan ALLAH kar wani yaji”.
           Baki ta taɓe tana miƙewa tsaye, “Ai kunji tsiyar, wannan tsoron naku shike ƙara masa karsashi da jin ya isa, wlhy inhar a haka za’a cigaba da tafiya to lallai akwai babbar matsala, dan kuwa sai kunkoma bayinsa tamkar a ƙarnin farko”.
        Tsayawa nai kawai ina kallonta, dan na fahimci ranta a ɓace yake, hakan yasa nai shiru, sam banason zancen yay tsawon da har wani zaiji, duk da Jazuga baya nan za’a iya samun wani ɗan neman gindin zaman a gidan namu ya sanar masa.
         Itama jin nayi shiru sai taja tsaki ta fice ta barmin ɗakin, murmushi kawai nayi ina girgiza kaina, na cire kayana sannan na ɗauki abincinmu da nasan Firdausi bata ciba tana jirana na fita, nasan bazata wuce tana soro ba zaune.
          Ilai kuwa acan na isketa, dan haka na zauna kusa da ita ina ajiye kwanon tasar abincin a gabanta.
      Cikin sigar lallashi nake faɗin, “Haba dai tawan, wai fushi kikayi? To kiyi haƙuri kinji, taho muci abinci, dan da gaske da yunwa na dawo mai katse ƴan hanjin ciki”.
         Hararata tayi tana ƙokarin matse dariyar dake neman kufce mata, (haka muke sam bamu iya dogon fushi da juna).
          Munacin abinci muna ƴar hira jefi-jefi, sai ƙokarin kauda firar da Firdausi ke ɗakkowa ta Jazuga nakeyi gudun kar’a samu matsala, a haka har muka gama na sake ɗaukar kwanon abincin na maida cikin gida.

           ★★★★★★★

    Kwanaki huɗu kenan cif Jazuga baya gidan, da alama dai yayi nisan kiwo, kallo ɗaya zakaima gidanmu ka fahimci akuyoyin ɗaure sun samu sake, dan harmun fara sakin jikinmu muna rayuwarmu tamkar ta baya.
          Sai dai kash a ranar cikon ta biyar murna ta koma ciki, ɓeraye suka koma wasan ɓuya da kuliya????, dan kuwa da yammaci kwatsam saiga Jazuga da zugarsa sun dawo, tsit kakejin gidan ya koma tamkar mala’ikan mutuwa ya shigo.
          A ƙofar shigowa soro ya tsaya, sai da ya karema gidan kallon kamar yau ya fara shigowa, sannan ya tako zuwa ciki, tafiya yake kamar zai tsinke saboda rashin ƙiba
         Dan sam Jazuga bashi da jiki, gaba ɗaya wiwi ta gama kalace dukkan wata tsokar jikinsa sai ƙashi data bar masa da fata
           Amma a hakan akejin tsoronsa tamkar mutuwa, ga jiki duk yabi ya zane da tatu, daka gansa kaga ainahin hatsabibi mai matuƙar haɗari da rashin imani, dan tsaf zai iya tsarwatsa kwalwar kanka da bindiga ba tare da ya damu ba……………..✍????
ALLAH ka gafarta.a iyayenmu????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button