NOVELSUncategorized

KUNGIYAR ASIRI 5-6

REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)

????5-6

             Dafe bango tayi da ƙyar tare da riƙe handle na ƙofar tana jijjigaw amma yaƙi buɗe wa!,bayanta inda ta bugu in  banda zugi babu abunda yake mata. Duk da haka ƙarfin hali kawai take domin ta samu mai kawo mata ɗauki.



Sosai ta galaɓaita kafin wani lokaci ta zube ƙasa tana fidda nishi sama sama saboda azaba!, can taji alamar buɗe kofa ana shigowa…,innalillahi zee ina kika shiga near?”muryan mijinta ta jiyo”.

Saboda tsabar galaɓaita ko ƙwaƙwarar motsi bata iya wa bare har ta kai ga mashi alama da zai gane tana rufe cikin ban ɗakin.

Wani sabon hauka ne ya kama ki saboda rashin hankali kin yi kache kache da ɗaki haka?,shiru ba amsa, ya shiga duba ko ina cikin ɗakin har cikin closet da ƙasan gado bai ga kowa baa.

Wuri ya samu gefen gado ya zauna yana tunanin ko guduwa tayi ne bayan fitar su?,sosai yake nazarin ɗakin ganin ko ina broken glass mirror near,window a buɗe.

Hankalin shi bai tafi ban ɗaki ba kawai ya fito harabar gidan ranshi a ɓace ya nufi wurin mai gadi…,bubbuga ƙofar ɗan ɗakin yayi a zafafe!

Ganin yanayin mai gidan nashi da yamman nan yasa ya sha jinin jikin shi sai ga bugun ƙofa kuma.

Ranka ya daɗe barka da fitowa!, kai ina matata ta tafi bayan fita na?

Ranka ya daɗe wallahi tunda ka fita babu wanda ya shigo ko fita daga gidan nan…

Maganar banza kenan”ya katse shi cikin ɗaga murya”,idan bata fita ba muje ciki ka nuna mun inda take ko?.

Allah huci zuciyar ka mai gida wanan ai ba hurumi na bane shiga turakar gida. Kasan da haka kake wasa da aikin ka?, infact ko ka fitar mun da matata ta ko in hananta wa hukuma kai a yanzu!.

Ranka ya daɗe ka dubi girman ALLAH ka mun rai wallahi banga fitar uwargida ba, tunda ka fita ina bakin aiki banga fitar kowa kamar yadda na faɗa a farko.

Mami ya hango ta nufo inda suke tsaye tana kwasar dariya!…

A hanzarce ya nufi wurin,yana isa ya tsugunna akan gwiwar shi tare da riƙo hanunta”meya hana ki bacci mami nab?”.Daddy  me yasa kai ma baka yi bacci baa?.

Banga mummyn ki bane,tunda muka dawo nake dubata shiru!

Ai nasan inda take!, da gaske kike mami?, eh daddy muje ka gani…”ta riƙo hanunshi zuwa suna tafiya”.

Basu tsaya ko ina ba sai ɗakin baccin su ta nufi ban ɗaki tare da murɗe handle ɗin ƙofa ya buɗe, zainab ce kwace shame shame kamar matatta!

A hanzarce ya nufe ta tare da rugumo ta yana jijjiga ta..,idanun shi suka sauka kan bayanta daya jiƙe sharaf da jini  ”subhanallah wa nene ya aikata maki wanan ɗanyen aiki zee?,don Allah ki tashi kada ki mutu ki barni ba zan iya rayuwa ba tare dake ba” cikin ɗaga murya yake magana!.

Ko gezau bata yi baa,ya shiga ƙoƙarin ɗaukar ta da nufin zuwa asibiti idanun shi na fitar da ƙwalla!…,mami ta dube shi cike da tausayawa ganin halin da ya shiga”daddy ina zaka kai ta?”.

Asibiti zamu tafi mami idan mummyn ki ta mutu asirina ya tono a duniya!.

Bazata mutu ba daddy ka ajiyeta zata buɗe ido kafin safe.

Tsuru tsuru yayi ya rasa mafita domin kanshi ya ƙulle,mutum na cikin jini ko motsi bata yi ace zata tashi ba tare da an bata wani taimakon gaugawa baa?.

Dafa kafaɗan shi tayi,ka yadda dani daddy zata tashi lafiya lau kamar komi bai faru baa!.

A’a mami ba zan iya haƙuri ba saboda idan ta mutu ba zan yafe wa kai na baa,kinga a dalilin abunda muka mata ta shiga wani hali har ta illata kanta.

Cikin ɓacin rai ta daka mashi wani irin tsawa!”bibiyar rayuwar suke yi na rantse da Allah da ka fita da ita daga gidan nan ƙarshenta yazo!,rayuwar suke nema domin cikar burina ya zama dole in nisanta kai na daku daddy!”.

Jin wanan maganganu na fita daga bakin ta ai bai san lokacin daya saki zainab a ƙasa ba!,da rarrafe ya nufi gaban mami tare da yin zaman dabas. 
Su wanene ke bibiyar rayuwar mumyn kibbutz?,wani buri nake  ne ba zai cika ba idan kina tare damu mami!?, a wahalce yake furta magana saboda tsabar tashin hankali daya shiga.

Juya mai baya tayi tana sharar hawaye..,bana nadamar shigar ɗaya daga cikin ku mawuyancin hali saboda akan cikar buri na babu abunda ba zan iya aikata wa ba lokaci kawai nake jira kuma da yyi zaku nme ni ku rasa!.

Juyo wa tayi tare da murmusawa,mu bar maganar a yanzu daddy dare yayi ka tafi ka kwanta nayi maka alƙawari mummy zata tashi da sauran kwanan ta a gaba.”tana kai nan ta wuce ɗakin baccin ta zuciyar ta fal farin ciki burinta na zama shugabar yar
ƘUNGIYAR ASIRI ya kusa cika nan bada daɗe wa baa.

Allaahumma ‘innee ‘abduka, ibnu ‘abdika, ibnu ‘amatika, naasiyatee biyadika, maadhin fiyya hukmuka, ‘adlun fiyya qadhaa’uka, ‘as’aluka bikulli ismin huwa laka, sammayta bihi nafsaka, ‘aw ‘anzaltahu fee kitaabika, ‘aw ‘allamtahu ‘ahadan min khalqika, ‘awista’tharta bihi fee ‘ilmil-ghaybi ‘indaka, ‘an taj’alal-Qur’aana rabee’a qalbee, wa noora sadree, wa jalaa’a huznee, wa thahaaba hammee.

Allaahumma ‘innee ‘a’oothu bika minal-hammi walhazani, wal’ajzi walkasali, walbukhli waljubni, wa dhala’id-dayni wa ghalabatir-rijaal.

Sune addu’oin da ya rinƙa maimaitawa a bayyana…(anaso idan bawa ya shiga cikin wani mawuyancin halibut,ƙuncin rayuwa,damu wa ko wani abu ya shige maka duhu ka rinƙa maimaita wanan addu’a safe da yamma).

Wani irin natsuwa ya shige shi cike da ƙwarin gwiwa ya sake cicciɓan zainab zuwa ban ɗaki a tsanake ya cire rigar dake jikinta wanda ya ɓaci da jini,famfon ruwan zafi ya kunna har ya taru daidai yadda ba zata cutu ba ya shiga watsa mata a hankali yana danna wuraren data samu raunuka da hand towel a hankali…,sai daya kusa gamawa da ruwan taɗan zabura jin raɗaɗi ga ruwa zafi na ratsa jikinta.

Hamdallah yayi tare da gode wa ALLAH cikin zuciyar shi,zubar da ɗan sauran ruwan yayi tare da taro wasu yana yunkurin ƙara wa ta riƙe hanun shi a wahalce ta furta”ciwo nake ji sosai don Allah ka barni haka nan”.

Tausayinta yaji dole ya haƙura a hankali suka dawo cikin ɗakin ta kwanta ruf da ciki sai sannu yake mata a jere….
Rub ya ɗauko mai kyau ya shiga shafa mata tana kuka  a wahalce,sai sannu yake mata har ya gama sanan yaja bargo ya rufe mata rabin jikinta inda babu rauni domin ba maganar saka kaya.

Miƙe wa yayi zai sauka daga gadon ta riƙo hanun shi”kada ka tafi ka barni ni ɗaya zasu kashe niagara!”.

Dawo wa yayi ya zauna cike da tausayin ta domin tun lokacin data fara bashi labarin abubuwa na faruwa tsakanin ta da mami bai taɓa gasgatawa ba sai a yau!,tabbas wani mumunar al’amari na shirin tunkaro su nan gaba.

Ba inda zan tafi,dama zan tattara ɗakin ne mu kwanta.

Girgiza mai kai tayi,”ka bari kawai har da safe ba kyau sharar dare”.

Shike nan barin sauya kayan jikina mu kwanta tau….,don Allah kada ka barni!.

Babu yadda ya iya dole tasaya shiga jero addu’in kafin kwanciya bacci kamar haka;suratul iklas(3x),suratul falaq(3x),suratul nasa(3x),ayatul kursiyyu(1x),amanar rasul(1x) sai;Bismika Rabbee wadha’tu janbee , wa bika ‘arfa’uhu, fa’in ‘amsakta nafsee farhamhaa, wa ‘in ‘arsaltahaa fahfadhhaa, bimaa tahfadhu bihi ‘ibaadakas-saaliheen(1x),a’uzubikalmaatullahi tammat min sharri ma kalaƙa(3x),Bismillahi ayanaa waa amut.

Bayan ya tufa ya shafe masu jiki duka  ya miƙa hannu ya kashe masu wuta tare da rage ƙarfin fanka.

Chakumar shi tayi tana faɗin,ka kuna wutar tsoro nake ji bana son ganin duhu!.

Hannu ya kai makunin wutar ya kunna,haske ya gauraye ɗakin…,Ya isa haka nan da iznin Allah babu abunda zai faru dake kuma ina tare dake,”yake furta mata ƙasa ƙasa cikin kunen ta,hanun shi na shafa gashin kanta”.

Shiru ya biyo baya na ɗan lokaci ko wanne da abunda yake tunani cikin zuciyar shi….., ɗaga kai tayi ta kalli tafkeken agogon dake manne a bangon ɗakin,”ƙarfe goma sha biyu dai dai na dare”.Ina mami?

Nan take yan hanjin shi suka kaɗa,tana bacci ya bata amsa a takaice.

Shiru ya biyo baya babu wanda ya sake magana. Yana son tambayar ta abunda ya faru a gidan bayan fitar su,amma yana jin tsoro kana wani abu ya sake faruwa!.,tana son faɗa mashi abunda ya faru da ita amma bakinta yayi nauyi kamar wacce aka rufe wa baki komi ya ƙwace mata sam ta kasa cewa komi kuma.

Suna a haka hatr bacci ɓarawo ya sace su…,duk abunda ya faru a kan idanun mami domin tana laɓe taba saurare har taji shiru sanan ta buɗe ƙofar a hankali ta tsura masu idanu har zuwa wani lokaci sana ta kaɗa kai tana jin soyayyar iyayen ta na ratsa ko wane sassa na jikinta!. Sai dai kash bakin alƙalami ya riga ya buge ba zata iya haƙuri da cikar wanan buri nata ba akan su,ya zama dole ta nisanta kanta dasu ko don tsiratar da rayuwar mummynta daga shiga haɗari!.

Abun shara ta ɗauko a kitchen a hanzarce ta gyara ko ina sanan ta kashe masu wuta ta kom ɗakinta.

Washe gari basu farka da wuri ba sai kusan takwas na safe saboda rashin bacci da basu yi da wuri baa,haka yasa suka makara sallar asuba.

Cikin ikon Allah koda suka farka jikinta sumul kamar babu abnda ya same ta a jiyan domin ko tambo babu, ga ɗaki a gyare tsaf!

Batawani yi mamaki ba domin ba yau bane rana na farko da irin haka ke faruwa da ita, shi dai yana son yin tambaya akan wanan lamari amma tsoro ya hana haka dai suka gabatar da sallar asuba a gagauce ta nufi hanyar kitchen nan suka yi kichibis da mami a palo.”ina kwana mummy,ya daren ki”?, lafiya lau ta furta idanunta ƙur akan koshin mami data buga mata a jiya ya tashi sumbul.

Ina daddyna?”ta katse shirun nasu”, muje kitchen zai fito bada jimawa baa.

Har sun kama hanya sai ta tuna da abubuwan da suka faru a jiya kawai ta canza shawara;ahm mami kin gyara ɗakin ki ne?,a’a mummy!.

Amma mena faɗa maki akan gyaran ɗaki idan kin tashi daga bacci?, turo baki tayi,ni mantawa nake yi kuma ai nace ma daddy ya samo maki mai aiki amma kinƙi yadda,kedai mummy komi naki daban dana mutane!.

Cikin rarashi tace,yanzu dai kiyi haƙuri ki gyara kin ji yan mata na,kefa babbar yarinya ce wacce zata shiga jss1 ace bata iya gyara ɗakinta?,ai sai friend naki su maki dariya idan suka ji.

Wuri ta samu saman hanun kujera ta zauna domin anzo inda take muradin ji..,dariya tayi sosai har sai da zainab ta tsorata domin kwata kwata ta tsani taji mami na irin wanan hatsabibin dariyar wani faɗuwar gaba ke ziyartar zuciyar taa.

Riƙo hanun mumynta tayi zauna kiji wsni labari abunda nayi ma yan school namu kowa ke tsoro na;wata yarinya kafila kullum idan muna class sai ta rinƙa kallo na,ai kuwa wata rana muna fita na bita a baya idanun nan nata da take yaan kallo na au na soka mata pencil a ciki!

zaro idanu zainab tayi cike a tsoro domin ta tuna lokacin da abun ya faru,babu yadda baa yida mami ba tace bata san zan cenba.

Sanan kuma ummulkhairi….

Dakata haka nan bana son jice kawai!.

Ji tayi ba zata iya wani dogon girki ba kawai ta ɗaura ruwa zafi da niyyar haɗa shayi….,mijinta ya fito cikin shirinshi tsaf  suka gaisa ya ƙare mata kallo,daga bisani yace idan mun gama breakfast ku shirya zamu wurin su hajia.

Da sauri ta kalle shipl,sanin zata shiga wni hali yasa ya fice daga kitchen din.

Wani tashin hankali ta shigadomin ta tsani zuwa gidan surukanta saboda wani dalili nata wanda ta barwa kanta sani.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button