BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 50

Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

50

……….Tasirin maganganun Gwaggo ya hanata sukuni, ta kasa zaune ta kasa tsaye ta kuma gagara basu fassarar data dace. Gwaggo dai uwa ce a gareta, domin mahaifiyarta haihuwarta kawai tai da shayar da ita. Dan tun daga yaye da Gwaggo ta ɗakkota bata sake waiwayen gidan mahaifinta ba sai da yawo. Ita ɗin tarbiyyar Gwaggo ce kuma rainonta. Ta samu gata irin wanda alƙalami bazai iya zanawa ba a takkada da ga gareta, domin kuwa a zamanin ƙuruciyarta kosu Muhammad (Daddy) dake ƴaƴan MB Shareff na cikinsa basu kaita jin daɗi ba a hanunsa. Gwaggo wata irin mutum ce da gane zuciyarta sai ALLAH, hakan yasa har Umma Hajarah tabar duniya bata taɓa hankaltuwa da wacece Gwaggo ba. Ba Umma Hajarah ba hatta su Daddy a yanzu basu fahimci kaso talatin cikin ɗari ɗin halayen Gwaggo ba sam, duk wannan faɗi tashin nasu akan zumincin da suke tada jijiyar wuyan ganin bai salwance ba. Tai gajeren murmushi da sauke ajiyar numfashi mai nauyi, dan tabbas mafitar data kasa nutsuwa ta samo akan wannan auren da bazata taɓa yarda da tabbatuwarsa ba tana wajen Gwaggo. A ganinta miya rage? Kawai ta kwantar da hankalin nata bisa shawarar tsohuwar ta kuma bita daki-daki domin cimma nasara. Sai dai a sanin datai mata kota tunkareta a yanzu bazata samu abinda take buƙataba dan haka zata barta har zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu……

         ★Jin kamar motsinsa yasa ta bar wajen da sauri, ruwan ta ɗakko ranta duk a dagule na rashin ƙwaƙwaran hujjar ya ganta ko bai ganta ba. Sai dai wani gefe na zuciyarta na ƙarfafata akan ta dake ta fuske kawai, (haba sai kace ba Anaam ba! karki bada mata mana). Da wannan kurarin ta dake ta koma bedroom ɗin, inda ta barsa nan ta samesa, sai dai yanzu ya warware lap-top ɗinsa a saman stool ɗin mirror daya jawo gabansa alamar aiki zaiyi. Ganin yana ɗan kusa da side drawer na gado saita ɗaura anan, sai faman riƙe rigar take da hannu ɗaya duk da a yanzu ba’a ganin komai jacket ɗin ta rufe ruf. Duk yanda taso zuciyarta nutsuwa ta gagara, ta ɗan saci kallonsa, hankalinsa gaba ɗaya yana ga aikin da yakeyi, hasken screen ɗin laptop ɗin ta haske fuskarsa. Gani tai ya ƙara mata wani ƙyau da kwarjini, ta haɗiyi yawu da ƙyaƙyƙyafta idanu domin abinda take son faɗa mai nauyi ne, sai dai gaskiya bazata iya jurewa ba gara dai ta tabbatar.
    Murya a noƙe tace,  “Yaya MM!”.
“Uhhyim”
Ya amsa mata batare da ya bar abinda yake ba. Sai da ta sake juya maganar a ranta kafin ta furta kamar zatai kuka.
      “Dan ALLAH in tambayeka zaka gayamin gaskiya?”.
Karon farko ya ɗago ido ya ɗan kalleta, tai saurin sauke nata idanun ƙasa. Idanun nasa ya sake maidawa ga aikinsa. Harta fidda rai da amsawar tasa ma.
     “Malama kiyi maganarki kai tsaye”.
  Baki ta tura gaba da ɗan murguɗawa kaɗan harda masa ƙaramar harara, zuciyarta sai ƙwaɓarta take amma wata na ingizata kuma. Cikin in ina da tsantseni ta cigaba da magana. “Dan ALLAH ɗa..zun da ka shi…go k…a…ga..n..ni k..o?”. Ta ƙare maganar kamar zatai kuka.
       Cak ya tsaya da ga danna keyboard ɗin laptop da yake yi, ya ɗago idanunsa da suka canja launinsu tun ɗazun ya kalleta. ɗan ƙara tsuke fuska yay tamkar abinda take maganar a kai bashi ke neman hanasa sukuni ba, murya a dake ya bata amsa kai tsaye…
     “Kina min talla na ƙara gani ne?”.
Babu shiri ta ɗago da sauri, sai ko idanunta cikin nasa. Ta zabura baya tana zagaya hanunta ta saman kanta “God forbid! Sai kace wata ƴar iska?. Kuma nidai ALLAH ya gani ai tambayarka nayi, dan zuciyata ta kasa nutsuwa nasan ka iya fuskewa da mazuranka bayan kuma k..k..k…..” ta kasa ƙarasawa saboda kallon da yake jifanta da shi mai matuƙar yawan aji-aji na fassara.
     “Ni dai naji, shike nan sai da safe. Dan ALLAH a dinga knocking idan za’a shigo”. Ta ƙare maganar da zagayawa bayansa da hayewa gado tana murguɗa baki. Zaune ta tashi da sauri, muryarta na rawa kamar zatai kuka, “Ni Juwairiyya, nifa kamarma cakai ina maka talla ka ƙara gani!, kenan ka gani ɗin fa? Wayyo Mamie na, ki roƙamin gafarar ALLAH Yaya ya fara komaw……”
        Muƙut ta haɗiye zancen ganin ya hawo gadon, ta zabura zata wulƙita ƙasa ya damƙota. Gaba ɗaya idanunta sukai wiƙi-wiƙi tamkar an kama tsohon kwarto a ɗakin surukarsa. Duka hannayenta ya maida baya ya riƙe da hannu ɗaya, ta shiga girgiza masa kai cikin magiya da roƙo muryarta na rawa tabbacin kuka na gab da zuwa. Ƙafafunta da take turzawa ya sa ƙafarsa ya danne, ya kai ɗayan hanunsa kan igiyar rigar tata, ja ɗaya yay mata ta warware dama ɗaurin zarge tai mata. Rigar ta buɗe, ƙara ta fasa masa, babu shiri ya kai hannu ya rufe bakin. Muƙutt ta haɗiye abinda ya rage bai fito a bakin nata ba, idanunsa da suka ƙara canja launi ya watsa mata, “Ba haka kike so ba na buɗe na gani”.
       “ALLAH ya kiyaye wlhy”. Ta faɗa da sauri tana son motsa jikinta ko yaya amma yayi mata riƙo na gaske.
    “Idan wannan bakin naki ya sake cewa (tak!) saina yage ɗayar ma silly girl”. Ya ƙare maganar hannunsa na sauka saman wuyan rigar da gaba ɗaya ya bayyana ƙirjinta saboda girmansa, rabin jikin nata ma duk a waje suke gashi ta kamata tsam kasancewar roba ce sannan copy lass mara nauyi.
     Fashewa tai da kuka na tsananin borin kunyar daya jefa rayuwarta a ciki, dan ita harga ALLAH bada tunanin komai tai tambayar ba. Sai da ya tabbatar ya firgita ta sannan ya saketa, wani irin kwakusa ta kaima duvet ta ƙudundune har kanta…
         Ƙara danne abinda ke hargitso masa brain yay da ƙyar ya koma ya zauna. Robar ruwan data kawo masa ya ɗauka, batare da yabi takan kofin ba ya ɓalle murfin ya dasa a baki. Tass ya shanye ruwan yay wurgi da robar yana rumtse idonsa da jijjiga kai tamkar mai girgije ruwan cikin suma. Ture stool ɗin da laptol ɗinsa ke kai yayi yana jan wani bahagon tsaki, toilet ya nufa cikin sassarfa kai kace ingizashi ake da remote.
       Anaam da bata san yanai ba na maƙure cikin bargo tayi luff takaicin kanta da kanta ya gama dabaibayeta. Ji take tamkar ta ciji kanta dan haushi. A gaba ɗaya abinda ya faru sai yanzu take iya lissafa rashin wayonta, mima ya kaita masa tambayar? Ta cije lip da ƙarfi tana kaiwa gado mugun mintsini tamkar shine ya mata laifin.. Jin shirun ɗakin yayi yawa ta ɗan leƙo kanta kaɗan, wayam babu shi a ɗakin, jitai wani farin ciki ya ratsata, ta miƙe da sauri ta dire a gadon, ƙofa taje ta sakama key duk a tunaninta fita yay a ɗakin. Ranta fess ta juyo tana karkaɗa keys ɗin da faɗin, “ALLAH na gode maka daya fita azababbe, sai iya fassara mutum akan abinda ba haka yake ba, kuma ban yafe ba ganinmun jiki da akai da way……”
      Numfashinta ya tafi zuuu ta haɗiyeshi tare da yawu, da ƙyar ta iya ɗago ido kaɗan ta kalla abinda taci karo da shi. Shine ɗin dai ba wani ba, zirr! Zirrr! Zirrr!! Haka jininta ke gudu a cikin jijiyoyinta yana kaima zuciyarta da ƙwaƙwalwa rikitattun saƙwanni masu tabbatar da firgicin mutum a cikin idanu. Miya rage? Kawai ta kwasa da gudu tabar ɗakin nan. Zuciyarta ta ayyana mata cikin ƙarfafawa domin ta tabbatar babu makawa yaji abinda take faɗa ɗin.
     Hannu ya miƙa masa alamar ta bashi keys ɗin. Cikin langaɓe kai da girgiza shi, hannunta ɗaya na tattare da rigarta da taketa faman kare ƙirji. “ALLAH bafa da kai nake ba, kayi haƙuri zan maka bayani yanda zaka fahimta…”
           “Nazo na amsa da kaina kenan?”.
   “A’a wlhy, ni dai ba sai kazo ba, daga nan ma zan maka bayani”.
   Yunƙurin matsota yay, da sauri ta jefa masa keys ɗin ya cafe. Cikin aljihun wandonsa ya zurasu da nuna mata gado. “Wuce ki kwanta”.
      Hankali tashe ta buɗe baki zatai magana….
   “Idan kika furta (A) sai na miki fata-fata a ɗakin nan. Idan kuma kinji ƙarya bismillah”.
     Summ summ ta wuce hankalinta a matuƙar tashe. Ya raka bayanta da wani shegen kallo tamkar idanun nasa zasu wantsalo waje……..✍

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button