AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 69-70

??69 and 70??

Via OHW???? ww

Hilal yagane number da sauri ya fizgi wayar, ameelah kamar tamasa kuka, ya danna yadauki kiran, ya kara a kunnen sa,

Ya gazgata muryar sosai muryar daya jice ranar nan,

HMM yace “beauty, beauty, keko acikin mayaudara bakowa bace, ni nafi karfinki, sama da sati daya ina cikin garinku kuma ke nazo nema, wlh wlh wlh duk ranar da mukayi ido hudu dake sai nayi ajalinki”

Razana na hango kaka a fuskar ameelah domin speaker hilal yasaka wayar,

Zuciyar hilal tayi matukar daukar zafi, cike da bacin rai yace “kai dan akuya ka rabu da ita matar aure ce “

Wani irin ihu da hmm yasaka kamar zai fita ta wayar, ameelah saida taja baya saboda tsoro, duk da hilal namiji amma saida yaji razana a zuciyarsa,

Cike da hargowa hmm yace “karyane wlh, beauty zaki mutu, wlh saina kasheki, … kai kuma idan kacika kazo kasameni Honal Hotel sabon gari, sai nayi ajalinka “

Ranar hilal yayi matukar baci yatashi tsaye cike da zafin zuciya yace “gani nan zuwa “

Yana gama wayar yajefa wayar saman gado, ya juyo ya kalli ameelah wacce tuni idonta yafara fitar da hawaye,

Kauda kansa yayi yanufi hanyar fita, dasauri ameelah ta mike tashiga gabansa, tana kuka tace “karkaje hilal, dan Allah karkaje”

bangajeta gefe yayi, ya murza kofar yafita,
Dafe kai tayi tabi bayansa,
Kiran sunan sa take amma shi ko juyota baiba, motarsa yashiga, yakunna yatafi,

Saman hanya yake yana tsala uban gudu, zuciyarsa ta rufe gaggawa yake yakai unguwar sabon gari,

Gudu yakeyi a kan tati kamar zai bar duniya, mutum ya hango yana kokarin tsallake titin karrrr yayi kokarin taka birki, amma ina saida yakai garesa, kimiss ya ture mutumen dake gabansa,

Mutum ya burma ihu yafadi nan take jini yafara fita a jikinsa,

Hilal yafito daga cikin motar a gigice, tun kafin yakaraso mutane suka taru wurin,

Cikin jini aka dauki, mutumen aka sakashi cikin motar hilal, suka wuce dashi asibiti,

Da gudu yakarasa asibitin, idanuwansa sunyi jajir,

Dauko mutumen sukayi suka shiga dashi asibitin, nan take likitoci suka kawo musu taimakon gaggawa,

A emergency room aka sakashi,

Su hilal suka tsaya a waje shida mutumen daya taimakesa suka kawo wadda yakade asibiti,

Hilal duk ya fita hayyacinsa,

Kusan mintinsu talatin suna zaune suna jiran fitowar likita amma shiru,

Mutumen da sukazo tare ya mike tsaye yace “ga wannan wallet din a aljihun wadda kakade yafito, kirike nizan wuce gida” ya mikawa hilal wallet din ,

Hilal yasa hannu yakarba,

Mutumen ya wuce, cike da tsoro hilal yafara bude wallet din, sunan mutumen daya kadene yaci karo dashi dakuma photonsa a makale agefen sunan,

Sunan yafara karan tawa kamar haka “AFHAM SIDI ABUJA” Hilal yaji gabansa yafadi, sunan yakara maimaita a zuciyarsa “Afham !!!….

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button