AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 71-72

??71 and 72??

Via OHW????

Hilal yayi Jim yana nazarin sunan, jiya keyi kamar yasan mai sunan,

hoton yatsaya yana kare kallo guy din yahadu, yafada a zuci sai yaji yanason zama da afham,

Wane gefe a cikin wallet din yakara budewa anan yaci karo da layin sim a ciki, dauko sim din yayi yana kallonsa mtn ne,

Wayarsa yaciro acikin aljihunsa, bude marfinta yayi ya cire sim dinsa yasaka wadda yagani a wallet din, a tunanin sa kozai sami number iyayen afham, domin yasanar dasu halin da yaron su yake ciki,

sannan ya kunna wayar,

Bayan wayar ta bude,
Contacts suka fara loading, a lokacin ya shiga contacts din yana bincike, 6ter aneesah itace number daya fara cin karo da ita,

A hankali yashiga kiran number , Ring wayar tasoma yi amma akaki dagawa harta tsinke, yakara kira a karo na biyu still ba a daga ba, saida yayi kusan five miss call ba a dagaba sannan yabar kiraran yashiga tura text , kamar haka “idan kinada alaka da mai wannan lambar wato afham, kuzo gombe domin yasamu hatsari yanzu haka yna asibiti” ya tura mata,
Yayi ajiyar zuciya,

yayi kamar zaicire marfin wayarsa yacire sim din saikuma yafasa, wata zuciyar take cemasa ” kakara bincika contacts din ko zaka same number mahaifinsa”

Haka kuwa akayi hilal yashiga bincike cikin numbers din afham,

by mistake hannunsa yayi rolling zuwa alphabet Z numbers na kasa gabaki daya,

Tundaga Z yafara yin sama yana duba numbers , wata number yagani an rubutu mata ZABINA.

Number yashiga kamar xai kira sai kuma yatsaya yana tunanin yasoma gane number daga ina tafito,
Number yake karewa kallo, yaji gabansa yafadi, “number Ameelah” yafada bakinsa na rawa, sai kuma ya girgiza kai, yace “ina bazai samu number ameelah ba, saidai idan mtn ne sukayi mistake gurin yin number”

Zuciyar hilal cike da sake sake, “a zuci yace bari nakira naji”
A fili kuwa danna number wayayi yafara dailing nata ,

Cikin sa a kuwa wayar tashiga, saura kiris ta tsinke, aka dauka,

Ihu yaji yafara fitowa a cikin wayar hadi da kuka saida hilal yarazana, muryar ameelarsa yajiya sak,

Ameelah tana kuka tace “zai kasheni, wlh zai kasheni ” sautin duka yaji yafito bayan tagama maganar, a gigice hilal ya mike yana fadan “ameelah waye zai kasheki” cike da hargowa saida hankalin mutunen da suke gurin kallonsu yadawo kansa,

Tunanin Kwakwallarsa yafara dawowa ya tuna da HMM kuma da ikirarin da yayi nacewa saiya kashe ameelah ” kara manna wayar a kunnesa yace ” ina zuwa ameelah” jiyakeyi kamar yabi ta wayar yakarasa gida,

A gudun tsiya yafita daga asibitin yaje ya shiga motarsa, gudu yake zabgawa akan hanya kamar zaitashi sama,

Daidai bakin layin shiga unguwarsu yataka wani irin wawan birki, saida kura tatashi, bai damuba yaci gaba da rusa gudu harya karasa bakin kofar gidansa,

A dai dai bakin kofar yaci karo da wani mutum yafito daga cikin gidansa da gudun tsiya fuskarsa rufe da mayafi, gabansa yaji yafada, dasauri yayi parking na motar, kamar zaibi mutumen saikuma yatuna da ameelah, yanufi cikin gidan, yana huci,

A kwance yasami ameelah cikin jini, a firgice yake kiran sunanta harya karasa gurinta yana magana amma bata amsa masaba,

Rungumota yayi yana laluba jikinta, yana kuka, daf yaji hannunsa yataba wani abu kamar karfe a gefen cikinta,

Cike da gigita yadaga riganta,
Wuka yagani, saura kiris takarasa shigewa cikin cikin ameelah,

Hannunsa narawa ya fizgi wukar daga gefen cikin ameelah, duk da ameelah a some take amma zafin fitar wukar yasa ta sandara wata irin wawuyar ihu,

Hannunta yasoma motsi, 

Hilal duk ya fita hayyacinyasa yadago hannun yana cewa “ameelah baki mutuba”

Ameelah takasa magana tirgar nunfashi kawai take , duk jikin hilal yabace da jini,

Daukar ameelah yayi yana sambato kamar mahaukaci, yafita da ita waje,

A daidai lokacin hajan zata shigo gidan, domin ameelah takirata,

Ganin yadda hilal yadauko ameelah yasa taji gabanta yafadi,

Hilal ko kokuluta baiba yasaka ameelah a mota , ya kunna motar yakoma asibitin,
Asibitin da yakai afham acen yakai ameelah…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button