BABU SO 65

Cikar burina shine ganin irin wannan ranar
tare da ke gimbiyar mata, kece sirrin ruhuna, nima
inajin raɗaɗi fiye da wanda na gani a cikin ƙwayar
idanunki. I’m sorry! ranarki tana zuwa_*.
Ta haɗiye yawu da ƙyar, da sake maimata
karatun kamar mai bita, dan yayisa ne da yaren
maley ta tabbatar batayi kuskuren karantawa ba.
Zaune takai dan ƙafarta ta kasa ɗaukarta. Ta
cigaba da zaro sauran abinda ke cikin akwatin.
Akwai kashi-kashi na ribbons ɗinta, ta gane
hakanne saboda matuƙar son da takema wasu,
wasu kuwa ta gansu a hotunanta dake cikin albom
ɗin can tun tana yarinya. Sai wani ɗan abunta mai
kamar kwalba cikinsa da taurari da wata suna
yawo, a tsakiyarsu da alkur’ani a buɗe, idan bata
manta ba Mamie ce ta bata shi as gi! ɗin kammala
haddar alkur’anin ta, amma saita nemesa ta rasa a
daga baya duk da kuwa a side drawer na gadonta
yake. Har kuka tayi na rashinsa, kai tsaye kuma ta
zargi mai aikinsu ce ta fasa amma ta ɓoye. Mamie
ce ta kashe wutar a lokacin ta sake saya mata wani
sai dai yasha banban da wannan ɗin dan haka
taita mitar batason sa har sai da Abie ya shiga
zancen ya lallasheta. Ashe Yaya MM ne ya sacesa.
Ta cigaba da kallon abubuwa da dama nata, kuma
masu muhimmanci a gareta data nemesu ta rasa a
lokuta mabanbanta, wanda a iya tunaninta ta rasa
mai ɗaukar mata su, duk da har su Amrah yaran
aunty mimi tasha zarga. Book ɗin ta ɗauka saboda
ji a ranta shima ya shafeta. A shafin farko sunanta
ne da rubutu kamar haka.
*_Juwairiyya Anaam! kece matar aurena kuma
uwar ƴaƴana da izinin UBANGIJINA. Ni kaɗai aka
haifawa ke, zan kuma rayune domin ke insha
ALLAHU._*
Ta buɗe shafi na biyu zuciyarta na tsitstsinkewa.
_Da ace wani bawa nada damar tsara labarin
rayuwarsa da wanzuwarsa, zan tsara nawane
kawai domin ke kaɗai a wannan duniyar. Ina
roƙon UBANGIJI ke ɗin karki zama a cikin
ƙaddarar abinda ALLAH bazai mallakamin ba,
zuciyata bazata iya ɗauka ba, ya rabbi ka zama
gatana akowane hali_.
Haka ta cigaba da karanta abubuwa dabandaban akan rayuwarta da tasa daya dinga
rubutawa tamkar labarin littafi. Mafi ƙololuwar
ruɗa tunaninta da saukar da hawayenta shine a
gaɓar da Mommy ta takura masa auren watanta.
Duk wani tashin hankalinsa ya zanashi da fargabar
karta suɓuce masa. Zuwanta Nigeria da sunan
hidimar ƙasa mafi girman sassauci dajin ƙwarin
gwiwar yin biyayya da cusa son Fadwa a ransa
matsayin sadaukarwa ko UBANGIJI zai masa
tukuyci da samun Anaam. Kukanta ya ƙara ƙarfi
jin cewar ya kwanta jiyyane akan jin za’a aurama
waninsa ita ba shi ba, harda barazanar kamuwa da
ciwon hawan jini daya nema shafar lafiyarsa.
“Innalillahi…” ta shiga ambata da kifewa jikin desk
ɗin nasa ta shiga raira kuka, wani al’amari mai
girma na ratsa dukkan magudana da jijiya ta
jikinta. Sai da tai kuka sosai harta gode ALLAH
kafin ta ƙarasa ganin wasu zane-zane da yayi
wanda duk fuskartace ya zana, kai kace tana
tsayene a gabansa yay zanen. Da kyar ta miƙe ta
tattare komai ta maida masa yanda yake ta maida
a drawer ɗin sannan ta fice jikinta a saɓule.
Aysha dake zaune a falo tana aikin nata na
tiktok data koya gun Fadwa ta bita da kallo. Ganin
zata wuce bedroom batare data tanka mata ba ta
riƙo hanunta da sauri. Juyowa tai tana kallonta,
hawaye masu ɗumi na sauka mata a kumatu, sai
kuma ta rungume Ayshan tana saki wani marayan
kuka da ita kanta bata gama tantance na minene
ba.
Hankalin Aysha ya ƙara tashi, ta ɗagota da sauri.
“Ya ALLAH blood wai miya farune? Yaya ne ya miki
wani abu?”.
Kanta ta girgiza mata.
“To minene? Ko dai maganar aurence dai har
yanzu? Da zaman wannan gidan?. Dan ALLAH ki
kwantar da hankalinki Anaam. Ki saurareni a
wannan gaɓar na buɗe miki kanki ta yanda wlhy
sai Yaya Share” ya dawo tafin hanunki ta hanyarsoyayya da bin dokokin ALLAH. Na fahimci rashin
sanin minene kishi da rayuwar gidan malam
bahaushe ke sakaki tafiya a haguggunce a wannan
gidan har Fadwa ke jan akalarki da makirci. Ki
nutsu ki saurareni Please”.
Bataƙi ta Ayshan ba, suka koma suka zauna cikin
hikima da basirar da ALLAH ya bama Aysha. Da
kasancewar ta tashi a rayuwane ta cikin gidan
yawa dama salon kishin Mommy da Aunty Amarya.
Ga karance-karancen littatafan nan na hausa duk
tana taɓawa ta shiga warware mata abubuwa
masu yawan gaske. Anaam irin mutanen nanne
masu saurin haddace abu idan an faɗa musu,
musamman akan abinda ke wahalar da su, ko
wani abu da basa ƙaunar a kaisu ƙasa. Hakan ya
bata matuƙar gudunmawa wajen fahimtar Aysha
daki-daki babu kuskure. Sosai taji daɗin bayanin
dan haka ta rungume Ayshan.
“Na gode blood, nagode, irin godiyar da babu
alƙalamin dazai iya rubutawa. Sai dai ki sani duk
abinda kikaga inayi a gidan nan kamar mara wayo
ba rashin wayo bane sarai ina lure da komai da
binsa daki-daki, sannan akan sani nake aikatawa
saboda wasu dalilai nawa. Idan banyi hakaba shi
kansa bazan gama fahimtar halayyarsaba balle ita.
Tabbas nasan bazan taɓa iya kaiku wayon zama a
irin rayuwar da kuka tashi ba, sai dai koba komai
ina shigowa cikinku nima ina ganin wasuabubuwan. Daliline ya sakani zaɓar yin duk abinda
nakeyi. Sai dai a yanzu kalar rubutun zai sha
banban da kalar takardar. A yanzu lokacina ne,
kisa a ranki lokacin Juwairiyya Usman MD Share”
zai fara a gidan Al-Mustapha Muhammad MD
Share”. Nayi alƙawarin bazanyi abinda zai cutar
da kowa ba, sai dai zan nunama kowa kowacce
mace da ilimin zaman gidan aure UBANGIJI ya
halicceta, kuma ko wacece ita ko’a ina ta tashi zata
rayuwu, ta kuma riƙe kambunta na ɗiya mace. A
kwanakin da nayi biyar a gidan nan, na karanci
abubuwa masu dama a cikinsu, zan kuma fara
sharar fadata da su domin samun damar shimfiɗa
mulkina batare da wani datti ya sha gaban cikar
burina ba”.
“Woow vary interesting my blood. Haka nake
sonki dan ALLAH. Ki haukata mana Yaya Share”, ki
kuma dawo mana da Fadwa hanya tabar bin
karatun su Mommy, ta zama mai ra’ayin kanta”.
Anaam ta ƙyalƙyale da dariya, zuciyarta fes
tamkar an sauke mata dukkan wani nauyi da
ƙuncin da takeji a yau a yanzu yanzu. Basai
amfaɗa ba, da ni da mai karatu duk zamu fahimci
hakan nada nasaba da abinda taci karo da shi
wannda a baya bashi take kallo a fuskar Share”
ba. Sun ƙara tattaunawa sosai akan wasu
abubuwan da dama da Aysha kafin ta miƙe ta
koma sashen Share” domin gyarawa bisashawarar Aysha.
Bata jin daɗin jikinta saboda ɗinkin da akai mata
na sakata jinta tamkar a takure, ga tafiyarta har
yanzu bai zama normal ba kamar da. Amma haka
ta jure a daddafe na rashin sabon da wahala ta
gyara ko’ina na sashen nasa, sauƙin ma babu datti
mai yawa. Sai da ta tabbatar ko’ina ya mata da
kamshi sannan ta rufe ta fito. Baki ta saki tana
kallon yanda Aysha ta ƙara gyara sashenta itama.
Ta saki murmushi da harar Ayshan dake tsaye tana
karanta mata taje tayi wanka ta ɗauki ado dan
Yaya Share” na gab da dawowa. Akwai tsoro
tattare da ita na abunda ya faru, amma gargaɗin
likita akan Share” ya bata ƙwarin gwiwar
tabbatarma kanta babu wani abu tunda ko dai
baya cikin hayyacinsa ai baya nema wani abu daga
garetaba zaren ɗinki na a jikinta. Da wannan
tunanin ta faɗa wanka. Koda ta fito tsareta Aysha
tai wai sai ta mata kwalliya. Badan taso ba dole ta
tsaya kuwa Aysha ta zaneta tsaf dasu jaja leɓe da
barbaɗa kumatu na zamani. Turare kuwa har ji
take yana hawa mata kai dan khumras nata sun