FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Ad
_____
[5/21, 3:27 PM] Oummu ฦahirah: ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
FAMILY DOCTORS
๐ฉบ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ
NAFEESAT RETURN
๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
ุจุณู ุงููู ุงูุฑุญู ู ุงูุฑุญูู
โ
FEENAH WRITER’S ASSO๐
”’ยฎฦaya tamkar da Dubu๐ชโ”’
JIKAR LAWALI CEโ๏ธ
Wattpad: UmmuDahirah๐
\F.W.A๐/
Thanks be May God bless everyone, peace and blessings be upon our leader Prophet Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, may God bless you and grant me the ability to write this book, may God grant me the ability to write what will benefit the nation ameen.
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ษaya. GOMA’S FAMILY.
LITTAFAN MARUBUCIYAR
NAFEESAT.
BARRISTER IBRAHIM KHALIL.
LABARIN DEEBIZAH.
MALAMA LADI.
JARUMAI
LUBABATU (ฦดar ฦwallon ฦafa).
.
EPISODE One
Doctor ” Al’ameen Abubakar Khabeer Cindo ” and his wife ” Prof. Nafeesa (Baby) Isma’il Audu, ” as you know in the story of * NAFEESAT * They live in Kaduna, and they still live in the city, owned by their five children.
1_ DOCTOR NOOR (LAWAL AL’AMEEN ~YARON UMMEE NAFEESA~) Wanda a yanzu ake kiran sa Big Dady, matar sa ษaya Hajiya Asiya (Hajiya) ฦดa ga Muhsina, yaran su uku, Doctor Usman, sai Doctor Zainab ~yanzu haka tayi aure,~ sai kuma Yusra.
2_ HAJIYA RABI’ATU AL’AMEEN (IKRAM) ~WANDA A YANZU TANA AURE A GARIN KATSINA~ tana zaune da iyalan ta acan.
3_ DOCTOR ABUBAKAR AL’AMEEN ~WANDA YANZU AKE KIRAN SA DA ABBA~ matar sa ษaya Doctor Fatima (Hajja Fatu) ~ฦดa ga Abokin Doc. Al’ameen wato Haidar da ฦanwar sa Ihsan,~ yaran su Biyu, Doctor Al’ameen (Baffa), sai ฦanwar sa Shakira.
4_ DOCTOR AL’AMEEN AL’AMEEN (ABBU) Matan sa biyu, ~Bilkisu (Umma) ฦดa ga Baseera,~ yaran ta uku Doctor Zulaiha ~tayi aure,~ sai Fadila da autan su Fadil. Sai matar sa ta biyu A’ISHA (AUNTY AMARYA) yarinyan ta ษaya ”’NAFEESAT”’ suna kiran ta da ฦahira.
5_ HAJIYA LAILA AL’AMEEN yanzu haka tana aure a Kano, ta auri babban Yaron WALID. Suna zaune da iyalan su can.
Waษannan familyn yanzu haka suna zaune ne a gida ษaya kowa da part ษin shi, sai dai akwai Babban parlour’n da ya haษa su, yanzu haka Doc. Al’ameen Wanda a yanzu suke kiran sa da KAKA ya kai shekaru 89years. Tuni ya ajiye aikin sa sakamakon yana fama da ciwon ฦafa wanda a halin yanzu yana zaune ne a wheel chair, matar sa Prof. Nafeesa (Baby) Shekaru uku kenan da Allah ya amshi abin sa.
Za kuyi mamaki idan nace muku duk ka familyn Doc. Al’ameen gaba ษayan su DOCTORS ne, wannan shine burin sa kuma Allah ya cika masa.
Babban asibitin da ya gina ya ฦara haษษaka shi wanda a halin yanzu Five Block ne, kuma sosai asibitin me suna (AL’AMEEN FAMILY HOSPITAL) tayi fice a ฦasar Nigeria, gaba ษaya familyn suna aiki ne a Hospital ษin.
Yanzu haka a halin yanzu an shirya yin babban Walima don taya Doc. ฦahira(Nafeesa) Al’ameen Al’ameen, Doc. Shakira Abubakar Al’ameen, Doc. Yusra Noor Al’ameen, da Doc. Fadila Al’ameen Al’ameen. Murnan kammala karatun su na likitanci, wanda za su soma aiki ne a ranan da a kayi musu waliman tare da sabbin ma’aikata da za’a ษiba a ranan.
KU BIYO NI DON JIN LABARIN WAฦANNAN FAMILYN
Zaune suke su Huษu a Babban katafaren parlour’n gidan da ya’amsa sunan sa a haษuwa da ฦayatarwa, da shigowan ka parlour’n Babban Hoton Prof. Nafeesa (Baby) zaka soma cin karo dashi, wanda tayi sa ne lokacin da ta zama Professor, tana sanye da baฦar abaya me tsananin kyawu da burgewa, wanda duk da kasancewar ta baฦa ba ฦaramin kyau yayi mata ba, sai tayane kanta da Milk Colour ษin Veil, kyakykyawar fuskarta yalwace take da murmushin da ya ฦara fito da tsantsan kyawun ta tare da Dimpul ษin ta, a tsaye take ta riฦe ฦugu da hannu biyu tare da ษan ษage kanta, da alamun sanda akayi hoton bata san ma za’a yi sa ba. kusa da hoton kuma wani tanฦamemen hoton ne da a cikin sa Al’ameen ne tare da ita Babyn, suna zaune manne da juna sun saka ankon shadda me ruwan powder, gefe da gefen su kuma Noor ne tare da Ikram jingine da jikin su, duk kan su dariya suke yi time ษin da aka ษauki hoton, sai gefe kuma sauran hotunan ฦดan gidan ne kowa da iyalan sa, sannan sai aka ษau guda ษaya wanda su kayi gaba ษaya familyn, shi wannan ba’a daษe da yin sa ba, don gab da rasuwan Prof. Baby akayi sa, gaba ษaya idan ka kalle su sosai suke kamanceceniya da juna, sai dai banbancin launi da ya raba su.
Doc. Al’ameen wato KAKA tare da yaran sa maza su uku zaune cikin parlour’n suna tattauna yanda za su gudanar da Waliman yaran su kamar yanda suka saba a duk sanda yaran gidan suka gama karatun su na likitanci.
“Kai takwara yaushe matarka zasu dawo ne? Kasan jibi ne walima, ya kamata su dawo don itama Matata (yana nufin ฦahira kenan) ta sami damar shiryawa yanda Ya kamata”. Kaka dake zaune saman wheel chair yake wannan maganan
ABBU yace, “insha Allahu Dady zasu dawo zan sake tuntuษan su inji, sabida mahaifin A’isha (matar sa Aunty Amarya) jikin ta yayi tsanani ne shiyasaka suka jin kirta”.
Kaka yace, “to shikenan Allah ya dawo da su lafiya”.
Gaba ษaya suka amsa da “ameeen”.
Sannan ya kalli Big Dady yace, “Kai kuma da yaushe ne Usman yace “zai dawo?”
Big Dady yace, “Allah ya taimaki Dadyna! na yi masa magana amma yace “in ba ka haฦuri ba zai samu daman zuwa ba sabida aiki sun yi masa yawa”.
Cikin nuna alamun fushi Kaka yace, “wai yaushe Usman yabzama me taurin kai ne? Ko don yana tunanin na ba shi dama ya zauna acan yayi aiki shine yake son ษata min rai? To, ka gaggauta kiran sa ka faษa masa umarni nake ba sa; dole ne ya zo wannan taron Waliman da za’a yi, ko me yake yi ya’ajiye sa ya halarci taron nan”.
Gaba ษayan su su kace “Allah ya huci zuciyar ka Baba”.
“Insha Allahu zan sanar masa Dady kuma zai zo”. Cewar Big Dady kenan
Gyaษa kansa Kaka yayi kana yace, “za ku iya tafiya na sallame ku, Allah yayi muku Albarka”.
Gaba ษayan su suka amsa da “ameen” kana suka tashi suka fice.
Shi kuma Kaka janyo Remote yayi ya sauya tasha zuwa African t.v yana sauraron wa’azi
Da sallama Fadil ya shigo parlour’n, wanda ya kasance shine ฦaramin gidan don shekarun sa baza su wuce 14yrs ba. zama yayi kan kujeran da ke kusa da na Kaka ya saka hannu ya ja gemun Kakan da ya kasance fari fat, yana dariya yace, “Kakus kana hutawa ne?”
Kaka bige hannun sa yayi yana faษin, “ฦaniyar ka Fadil, kai ma ka koyi jan min gemun ne yanda Matata take min?”
Dariya ya tuntsire da shi yace, “to ai hakan ya fi dace wa da kai Kakus, don me baza ka aske gemun ba ka bar abu sai faman lilo yake yi, wlh watarana kana barci zan silalo in cire maka kowa ya huta”.
Dariya shima Kakan yayi yace, “lallai ka raina ni da yawa amma ina da me maganin ka, ka jira ya dawo zan faษa masa duk abinda kake min”.
Zumbur Fadil ya miฦe yana waro ido waje yace, “afwan Kakus kaima ka san ba mu haka da kai, wlh yau ne kawai nace bari in ษana Amma baran sake ba, Kar kasanar masa don Allah kaji Kaka na”. Yaฦarike maganar nasa yana me marairaice fuska kamar zai yi kuka
“Shaฦiyin yaro ashe kana da tsoro har haka?”
Waro idanu Fadil ษin ya sake yi yace, “iyyee Kaka taya bazan ji tsoro ba bayan kana son ka haษa ni da Zakin gidan mu? Ni dai ka ga tafiya na don tunda ka’ambato shi bazan iya zama anan ba”. Yana ฦarisa maganar ya ruga aguje yabi hanyar part ษin su
Da dariya Kaka yabraka shi, kana ya girgiza kan sa aran sa yana cewa, “lallai Usman ka koya ma yaran gidan nan tsoron ka, ba ka a cikin gidan ma shekara da shekaru amma har yanzu tsoron ka be bar cikin ran su ba”.
Ad
_____