FARHATAL-QALB

FARHATAL-QALB 5

LAST FREE PAGE: 5
(SHAFIN KARSHE NA KYAUTA!)

××××××

   “Haba Sa’adatu, Wannan ba girman ki ba ne wallahi.” Najan Isubu ,  Ta fadawa Inna Sa’adatu haka.

“Yo ai gaskia ta fada.. Me sunan Malam kana jinta ko kayi kunnen uwar watsi?”

“Kiyi hakuri Marka… Ke waheeda baa ta hakuri.” Malam NaLado ya tsawatar wa Waheedah.

Ita dai Umma Hadiza bata ce komai ba. Tayi zugum a gefe kanta a kasa.

      “Ummaaa kafaata, Umma kafata. Kafata ummah ..Wayyo, wayyo ” Najibu ya shigaa maimaitawa yana mai dartse hakoran sa 

Marka taja tsaki, Umma hadiza ta miqe da sauri ta koma cikin daki wajen su Najib.

“Haba wannan wahala har ina? Ga wannan ga wannan. Gaskia da sake ” Marka ta fada tana mai hararo dakin su Najibu

“Kai Marka ki dena cewa haka. “

“Kinga Naja ki fita idanu na. Ni dama tun da na kyalla ido na hango shigowar ki, Nasan tabbas wani katsalandan dinne ya kawo ki..”

“Kiyi hakuri Marka. Da yardar Allah komai ya kusa wucewa. Lokaci ne, Idan Allah ya nuna mana wucewar da sai kiga tamkar ba’ayi wannan tashin tashinar ba.” Naja ta karasa fada idanuwanta akan Marka dake faman cin magani.

Can ta sake sakin wani dogon tsaki tana karkada kafafu.  Cikin kufulewa tace,

“Kin isheni da zubar lallami Najaatu. Har kina wani lankwashe kai kina jin haushin Sa’adatu. Yo ai gaskia Sa’adatu ta fadi. Yaran Sa’adatu babu abunda zamu ce da su agidan nan sai san barka da fatan samun nasarar Allah akan dukkanin lamuran su. Zainab da suke kusan sa’anni daya da wahidin ne sau uku mai nemanta ya kawo mana kayan abinci ga su nan idan karya nayi.”

“Zancen ki haka yake Marka. Domin wainar yar tsalan jiya ma zainab ce ta sayo.” Cewar Sa’adatu hade da kecewa da dariya.

“Wannan duk ba abun damuwa bane Marka..”

“Babbar damuwa kuwa Naja. Natsani safiya tayi dare ya maye idanuna su sake dora ganin su akan Hadiza da ahalinta. “

“Kash. Assha Marka. Ki bar cewa haka. Babu fa bawan da ya tsara rayuwar sa haka fyace wadda Allah ya rubuta. Kuma menene yan uwantakan da zumuncin idan har dan uwanka baya kyautata maka?”

“Ke Naja. Duk abubuwan da zaki fada ba tasiri zai yi a zuciyata ba don in gaya miki…”

“Kibar cewa haka Marka…”

“Dole na fada. Kinga wuya. Nan inda abu ya tokare mun yaki tafiya. ? Ba komai bane fyace bakin cikin da Hadiza da yaranta suke samun. Nagaji idan da gaban gajiya nayi…”

“Ya SubhanAllah! Ki dubi girman Allah Marka ki dena cewa haka, Dukkanin yaran nan fa jikokine. Haka kuma Allah yaso acikin jikokin naki zaa samu biyu marasa lapia “

“Marasa lapia? Nakasassu zaki ce. Masu tattare da kunci da ‘dacin rayuwa.”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Marka!! Marka!! Ki dena cewa haka. Malam ka saka baki. Wannan ba dede bane.”

“Ba ze saka ba Najaatu. Idan kin gaji da ji ki tattara ki fice mana daga gidah .”

“Kiyi hakuri Marka. Kawai dai gani nayi wannan maganganun dik basu taso ba.”

“Dole ne ayita. Shi ya saka nace wallahi kwayar hatsi nawa hadiza dasu Najib ba zasu sake ci ba. Su dan kinibibi sunyi shabe shabe ga nakasassu da baza su fita su nemo ba. Ita kuma uwar tasu ta daure musu gaba ba zata tursasu ba. Kullum dan tsagwarar munafurci suna daka suna sakin numfarfashi. Ita kuma ta faake kullum tana gefen su ba zata fito cikin mata tayi shiqa ba ta samu kudin batarwa. Ragowar me lapiar kuma ta tsiri boko ba kakkautawa.  Ba zeyiwu ba wallahi. Su tunda maza ne suje can su karata ita kuma tinda macece dole ne a aurar da ita. Baqin jini ya mata katutu maza basa zuwa. An samu kuma Na’Ateeku yace yaji ya gani zai aure akan wane dalili zamu fasa? Bayan idan ta aure shi kakarmu ta yanke sa’a . Ita kanta Hadizan sai tafu jin nutsuwa da kwanciyar hankali… Wahala zata ragu. “Marka ta karasa fada tana gyade kai.

Najan isubu ta numfasa kafin tace,

“Kowane bawa da yadda Allah ya kadarta masa rayuwar sa, Wala dadi wala akasin haka. Rayuwar hadiza da yaranta haka Allah ya rubuta mata tata jarabawar. Sai dai fatan Allah yaba su ikon cinyewa yasa jinkirin alkhairi ne Aamin . Zancen nauyin dake kanta da yardar Allah yazo karshe. Domin na samo mata aikin wankau da yan kaude kaude a layin manyan can na shurah. Saboda haka zata sauke nauyin wasu abubuwan . Haka zalika itama Waheedan akwai abunda zaa sama mata ta dingayi bayan su Najeebu sun ji saukin jikin su. Don haka Marka ki ajiye zancen Na’Ateeku agefe yanzu.”

“Na ajiye na zuba mata idanu ina kallonta? Ba dan mashinshini a kusa sai zuryar boko? To bokon yaci uwatas.”

“Kiyi hakuri. Insha Allah kwanannan samari zasu fara zuryaa a kofar gidan nan. Komai lokaci ne. Mijin ta na nan kusa da yardar Allah. Wanda zai share hawayen ahalin gidan nan kai dama na kusa da ku baki daya. Insha Allahu. Kice Aamin Marka..”

Umma hadiza dake daki hawaye suka shigaa zirara a idanunta. Tabbas Najan Isubu aminiyar kwarai ce data san dattako take kuma yi musu madaukakiyar kauna marar misaltuwa.

“Marka, Sa’adatu, Malam baku ce Amin ba.”

“Aamin Najaatu.” Malam Nalado ya fada yana sosa keyar sa.

“Uhum…. Inji me ciwon baki.”Cewar Sa’adatu hadi da yin kwafa ta juyar da kanta gefe.

“Aamin inda gaske ne hakan zai kasance ba karairaki bane da wucewar zance.”

“Insha Allah Marka… Na’Ateeku abunda yasa ki kaga na kauda zancen  maganar sa akan irin lalurar su Najibu ce. Ta sikila da ake cewa amosanin jini.”

Marka taja dogon tsaki tana kauda kai gefe.

“Ke wallahi Najaatu kin iya samun waje kiyi ta sakin ta.”

“Allah ba karya nake ba Marka.”

“Wohoho ni lauya zan ce ne banaso wallahi. Na’Ateeku ban taba gani ya kwanta ciwo ba. Zaki jajiba masa.”

“Marka abunda nake nufi shine. Shima ai yanada iyali dake dauke da irin ciwon su Kamal. Ba wai ina nufin shine mai ciwon ba. Amman yana dauke da wasu sinadarai na ciwon wanda idan ba’ai gwaji ba kafin aure shine zakiga anata hayayyafan yara masu dauke da ciwon. Yanzu kai ya waye Marka… Sai anyi gwaji kafin ayi aure saboda gudun ‘barakar ciwuka. Hakan yasa na ce miki ki bar zancen Na’Ateeku da Waheedah. Domin kulla auren su kan iya haifar da illoli da yawa astagfirullah. Ba tsumi babu dabara. Maganin kar ayi kada a so ma “

“Keda Naja kinada kale kalen balai wallahi. Allah shi kyauta “

“Wannan shine tushen gaskia Marka. Ba Na’Ateeku ba. Ko wani ne daban yazo neman auren Waheedah ko zainab dole ne kafin ayi auren suje suyi gwaji. Wannan shine babbar shawara da ma’aikatan lapia suka kafa. Don gudun bacewar rana. Azo ana danasanin auren.”

Marka ta tabe baki hade da jan karamin tsaki.

“Gidan aikin da zataje ina fatan nima inada nawa kason acikin albashin nata.?”

“Duk ba zai gagara ba Marka. Kuma insha Allahu tare daku duk zamuje taron nan ayi mana gwajin.”

“Uhm..” cewar Marka.

“Bari na tafi. Allah ya kiyaye gaba.”

“Toh Najaatu. Agyada gidah.”

“Gidah yaji.”

“Ke kuma tashi kafin na hamb’are ki. “

Takarasa tana mai wurgawa Waheedah harara. Gaba daya maganganun Najaatu sai shawagi sike mata akai. Ta kaikaice kai ta hango ledar taliyar kakkaryawa da tumatirin gwangwani. Na’Ateeku ya sake fado mata arai. CikiN zafin nama ta mike ta shige kuryar daki .

Waheedah ta mike jikinta a sanyaye ta shigaa dakin su Kamal. Umma hadiza kuma ta tafi ta yowa Najaatu rakiya. A soro Najaatu ta sake kwantar da hankalin umma hadiza. Da karfafa mata gwiwar ta zage damtse ta fara aikin nan da karfin ta. Ko zata kwatowa kanta da yaranta yanci a idanun su Marka ………

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button