NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 51-52

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*



*SMALL GIFT TO…*
*MY DALA????…..*



5⃣2⃣&5⃣3⃣


Cike da mamaki Yasmeen ta Bude baki a hankali tana maimaita Kalmar matata’ matata.
Yanzu nadawo Daga kai matata gurin kwalliya’ Yasmeen ta maimaita maganar a fili”
Eh haka nace daidai kikaji’ kinga kidena batamin lokaci Idan bazaki fitoba nizan wuce’ mashkur ya Bata amsa sedai wannan Karan cikin sanyin murya ya fada ganin yadda ta Shiga Wani Hali Dan kawai ya Kira nijlah da matarsa…

Yasmeen Bata qara Magana ba ta saki wayar ta fadi qasa’ nan take wayar ta ragargaje”
Bata bi takantaba ta kife a gurin tana sakin kuka’
Tajima tanayi kafin Daga bisani ta Tashi ta fada toilet.

Tinda mashkur yaji tsinkewar wayar yasan abinda yafaru sedai beyi mamakin Hakan ba sabida yasan Kishin Yasmeen tin kafin kaddaran auren nijlah ta fada masa,,dafe kansa yayi yanamejin haushin Hakan dayayi mata’ Dan Ko ba’a gayamasa yasan Yau Yasmeen bazata Iya Cin komai ba’ Idan kuwa Hakan tafaru to tabbas ya cika Maci Amana Kamar yadda ta kirashi da Sunan.
Rasa mafita yayi Dan haka ya yanke shawaran Shiga ciki koze Iya shawo Kan masoyiyar tasa’ dasauri ya kunna Mota yayiwa get man horn, Yana Bude masa ya Shiga ciki Ko kallan inda baba Mai Gadi yake be Kalla ba haka ya tsayar da motan ya fito Yana tafiyansa me daukar hankali.

Tabe Baki get man yayi Yana cewa’ oh ikon Allah kuduba yadda nake gaisheda mutuminnan yayi kama be gani ba,,kodan ba abin mamaki bane tinda Yana tare da wannan’yar girman Kan Yasmeen yaqare maganar Yana waiwaye alamun rashin gaskiya.

Masha na Shiga yafara qoqarin Kiran layin Yasmeen sedai wannan Karan wayar a kashe ake gayamasa” Rasa yadda zeyi yayi Dan haka ya qarasa kofan falon Yana sallama”
Mama na daki ta fito da sauri tana cewa’wanene?

Mama nine mashkur’
Murmushi mama tayi tana cewa sannu da zuwa Ka shigomana Ka tsaya a waje’ Kan mashkur a qasa ya shiga’ be zauna akan kujera ba ya risina Yana gaida mama,,

Mama ina kwana?

Lafiya qlau mashkur’ yame jiki?
Dasauri harta Samu lafiya an sallamemu’
Kai alhamdulillah naji dadi sosai,,Allah ya kiyaye gaba.

Ameen mama’ mama bata tashiba Saida taqara ba mashkur hakuri akan abinda yafaru nan ta tashi tana cewa ina ita Yasmeen?
Ka Kira wayanta mana’ sosai kai mashkur ya shigayi Yana cewa ai mama wayan ne akashe shiyasa ma na shigo..

Dakin Yasmeen mama ta tafi tana Kiran sunanta sedai mama bata iya cigaba da Kiran ba sabida Jin kukanta” dasauri ta Shiga tana cewa ke Yasmeen lafiya me aka Miki?
Cikin kuka Yasmeen tace’ mama shine wallahi yadena Sona nijlah yakeso.

Girgiza Kai mama tayi tana cewa inji waye? Waya gayamiki?
Allah mama Baya Sona shikenan nayi asaran dakon soyayyarsa danayi shekara da shekaru’ sai yanzu wata Kula baqa Zata zo muyi kasan soyayyarsa da ita.
Ai kinji matsalarki mama ta fada tana Zama a gefen bed tare da janyota a jikinta’ kinga Yasmeen ki tashi ki goge wannan hawayen’ indai mashkur ne gashican Yana jiranki a falo..

Dan Allah mama da gaske?
Kinci gidanku ina Miki karyane?
Dariya Yasmeen tayi tana goge hawayen fuskanta ta tashi ta fada toilet,,tana Shiga mama ta fito tana cewa gatanan zuwa tana can tana shirmen nata.

Murmushi mashkur yayi yakasa amsawa’ har mama takai qofa ta dawo tana cewa’kaga munata magana ban tambaya su mummy ba? 

Murmushi mashkur yayi Yana cewa’suna lafiya tace a gaisheki 

To alhmdllh mama ta fada tana Shiga daki.

Sosai Yasmeen ta zauna ta tsara kwalliya tare da saka wasu Kaya masu shegen kyau turaruka ta feshe jikinta dasu kafin ta fito tana taku  cikin nutsuwa Dan Yasmeen badaga nan ba gurin iya daukar wanka da kalamai masu dadi shiyasa ko sun Sami sabani da mashkur bata Shan wahala gurin janye hankalinsa har yaji ya hakura..

Tinda ta fito ya zuba Mata Ido Yana Yaba kyan surarta’ a haka harta qaraso kusa dashi’
Jitayi kama ta rungumeshi sedai bazata iya hakan ba nan ta zauna Kan hannun kujeran da mashkur ke zaune tana kashe masa ido’ a hankali tasa hannu ta zagaye jikin kujeran tare da kwantar da kanta Kan hannun kujeran daidai inda hannunsa ke Kai.

Ido ya zuba Mata Yana zancen zuci’ wai me yarinyarnan take nufi kadafa ta susutani sabida alokacin yafara Jin wani irin Abu na tsirgawa a cikin jikinshi..

Baby fishi kake dani? 

Kallanta mashkur yayi Yana girgiza mata Mai Yana kallanta cike da soyayya’ to Amma shine zaka sani kuka,,yanzu Dana hadiye zuciya na mutu ya zakayi?

Hakan ma baze taba faruwa ba,,sedai yanzu kema kin chanza Hali shiyasa Nima nakesan chanza nawa kema kiji inda dadi.

Baby ni kuma me nayi?

Au Bama ki sani ba’ ko?

To kayi hakuri bazan qaraba’
Kallanta kawai yake Yana mamakin shagwabanta,,da kyar ya bude baki Yana magana Yana kallanta”

Allah yasa’ 

Da ameen Yasmeen ta amsa tana qara narke masa.

Babu Wanda ya qara magana kusan minti guda daga Baya Yasmeen tace’
Baby wai har lokacin biki yayi? Ni gaskiya sonake adan qara lokaci kaga’
Kinga dakata banasan wannan shirmen zancen naki,,sai ana magana na arziqi saiki tsiro da shirme, wanne irin daga biki?

Nan fa mashkur ya rikice Mata Yana fada a cikin nutsuwa tare da Nuna Mata bacin ransa.

Murmushi Yasmeen tayi tana dariya tare da yimasa gwalo tace’ yeeeeee naji ta bakinsa,,Dama sonake naji kadena dokin bikinmu ko haryanzu kanayi?

Ba qaramin sanyi mashkur yaji ba Dan  yau har saida yakai hannu da niyyan bigeta ta goce,,daganan suka cigaba da hira,, mashkur be bar gidansu Yasmeen ba sai bayan sallar magrib yamata sallama ya tafi gidan abokinsa jabeer….

Tinda nijlah ta kwanta bacci ya gagara daukanta Banda juyi babu abinda take,,tin tanajin ciwo kadan kadan harta fara riqe cikinta tana yamutsa fuska,, ahankali a hankali ciwon ya riqa sauka a cikinta tare da riqemata bayanta da mara,,tin tana kuka a hankali harta fara me sauti tana Kiran sunan Allah..

A haka bacci yadan fara daukanta,,tana cikin bacci taji fitsari me shegen zafi na damunta’ dakyar nijlah ta tashi zaune tanasan Shiga toilet sedai wani abun mamaki qafan yaqi daguwa ga wani irin ciwo dake damunta’Banda kuka tana kallan kofa babu abinda nijlah take..
Dakyar ta iya safka da rarrafe ta sauko akan gadon tana kuka ta rarrafa ta Shiga toilet..

Mummy dake zaune a falo tana kallo yayinda Maryam me aiki ke tsaye a kitchen tana fere doya taji suka ji kukan nijlah’ tsaki mummy tayi tana kwana Kiran Maryam” 
Maryam ke Maryam kina ina zoki budemin dakin wannan shegiyar yarinyar Naga abinda take,,aini bansan tana gidanba nake zaune a falo,,to Allah ya kareni daga daukan Corona virus a jikinta,,nasan babu inda qafanta be kaiba’ dariya Maryam ta gumtse tana tsoran Kada tayi mummy ta hauta da fada…

Dagowa mummy tayi taga Maryam tsaye tana sunne Kai’ 

Ke kuma ya haka zaki tsayamin aka saikace mara hankali’ 
Dasauri Maryam tayi qasa da Kai tana cewa mummy kiyi hakuri..

Niba wannan na tambayeki ba,,jeki duba dakin auta kiga me wannan yarinyar takewa kuka Kada muna nan zaune ta hadamana gobara bamu sani ba,,kafin mummy ta qarasa magana nijlah ta saki wani wahalallan ihu tana Kiran Kaka..

Da gudu Maryam ta qarasa dakin tana cewa ke kina ina’

Nijlah da qarasawanta toilet kenan ta cire pant da niyyan zatayi fitsari taga jini nabin jikinta  pant dinta yayi kaca kaca da jini gashi jinin hadda guda guda..

Wayyo Allah na jama’a Ku taimakamin wallahi Bari nake.

Dasauri Maryam ta Shiga toilet tana janyo nijlah jikinta,,jinin data gani ne yasata sakin salati tana cewa’ ke dama cikine dake?

Eh wallahi Dan Allah ki taimakamin Bari nake nijlah ta fada a galabaice Dan zuwa yanzu magana ma a hankali takeyinta.

Mummy dake zaune taji nijlah na ambatar bari’ bata Ida tsinkewa ba Saida taji Maryam na cewa Dama ciki gareki?mummy bata jira Jin amsar da nijlah Zata ba Maryam ba ta miqe tsaye tana tafa hannu tare da sakin kuka tana cewa…….




Kuyi hakuri inada mara lafiya shiyasa kukaji Shiru…



Comment & share






*Momn sultan ce*✍✍✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button