NOVELSUncategorized

A GIDANA 7

*Haske Writers Association*馃挕

*Shafi na bakwai*

聽 Idanunta Zainab ta kalla tace “Nabila!”

 Nabila ta mike da sauri tace “ba abinda na sani, kawai dai maganar ce tazomin.”


 Zainab ta kalleta, da sauri ta shige daki ta maida kofar ta rufe.

 Shiru Zainab tai tare da zubama kofar ido, kafin ta mike ta nufi daki, agoggo ta kalla taga karfe 4, computee dinta ta dauka ta koma falo ta zauna.
聽 Wajen karfe biyar ta mike ta shigo daki ta kalli Adam dake ta baccinsa, kusa dashi ta zauna sannan ta dan tabashi, tace “Honey a daure atashi aje masallaci.”

 Batare da ya bude idansa ba yace “bacci nakeji, nayi anjima.”

 Hannu tasa ta jashi ta zaunar dashi akan gadon, a hankali ya bude idanunsa yace “Honey Allah bacci nakeji.”

 Fuska ta hade tana kallansa batace komai ba.
“Na tashi shikenan?” Ya fada tare da bude idanunsa sosai, sakeshi tai sannan tai murmushi tace “ko kaifa.”

 Yake ya mata, gira ta daga mai ta nuna mai toilet da ido.

 Ajiyar zuciya yai sannan ya mike yai alwala yana fitowa ta mikomai jallabiya ya saka yana ta dan zumbure zumburenshi kai kace yaro ne aka kwacemai alawa.

 Fitowa yai daga gidan ya nufi hanyar masallaci.
 Suna idar sa sallah shine na farkon mikewa ko addu’a bai tsaya ba ya fito, ganin Nazifi a masallacin yasashi saurin bi ta baya, dan bacci yakeji bashida lokacin tsayawa magana.

聽 Daga kungun da zai shiga kwanar gidansu yaji motsi, cikin tsananin tsoro ya matsa da sauri tare da zaro wayarsa ya haska fitila yana cewa “waye nan?”

 Ganin ana kara buyewa ne yasashi kara matsowa gun yana haska fitilar duk da tsananin tsoron da yakeji.

 Yana neman karasawa daf da mai boyewar aka saki kwalin da ake boye fuskar dashi.
 A tare suka saki wani kara, yaja da baya da sauri, bayan sun gama karar ne ya haska fitilarsa a tsorace.

 Tsayawa yai cak yana kallan ta, haska kansa yai hakan yasa ta gane shi.

 Kallanta yai yace “bake bace ta dazu? Me kike anan?”

 Kanta ta saukar kasa tace “komai na wa an sace kuma makaranta nazo, gashi bansan kowa ba, banko biya kudin hostel ba.
To me kike anan kina mace?

 Bansan ya akai na ganni anan ba, shiru yai yana kallanta kafin yace “bakisan kowa ba a kano?”

 Kai ta daga alamar eh, shiru yai yana kallanta kafin yace “to ki koma garinku mana in safiya tayi?”
“Ban isa komawa ba inba haka ba mijin mamanmu dukana zaiyi.”

 Shiru yai yana kallanta bai fahimceta duka ba, kamar yace ta biyoshi kuma yafi kowa sanin matarsa, da sauri yai gaba bai kara waigowa ba ya shige gida.
 Yana shiga yai ajiyar zuciya yace ” ashe dai inada tausayi.”

 Kai ya girgiza da sauri ya shige ciki.

 A zaune ya taddata a falo taba kan sallayabga laptop dinta a gefe, da sauri ya wuce daki.
 Ta fahimceshi wato kar ta mai magana shiyasa ya shige, yana shiga ya kwanta, kan kace me bacci yayi gaba dashi.


***********

 A bangaren Khalid kuwa bayan yabar gidan cafe ya wuce ya duduba aiki, sai wajen magrib sannan ya nufi gidan kawu.

 Sam ya tsani zuwa gidan dan yana shiga layin yaci karo da babbar ‘yarsa mace, anci uban kwalliya a gaban mota itada saurayinta.
 Yi tai kamar bata ganshi ba shima ya dauke kai.

 Ji yake kamar karya shiga gidan, ya dade a tsaye a kofar gidan yana tuno bakincikin halayensu daya sha farkon zuwansa, harya juya da niyyar komawa danbatta inyaso da sassafe sai ya dinga fitowa yaji ance “Khalid?”

 Juyawa yai, dan ya san wanene, Kawu ina wuni?

 Abinda yace kinan yana rusunawa, Kawu ya dafa kafadarsa yace “ina zaka da?”
Muje muje, ya jikin Baban naka?

 Da sauki, ai naso kara komawa sai dai bana zama ne nima.

 Khalid dai baice komai ba, haka suka shiga ciki inda suka wuc falansa yasa a kira matan nasa.

 Su uku ne suka shigo kowa sai yace “khalid yau kaine a nan?”

 Bayan ya gaisu ne Amaryar ta kalleshi tace “da alama an dace an samu aiki kenan.”

 Kawu yai saurin cewa “haba?”
 Khalid yai murmushin yake kawai, nan ya zauna sukaci abinci tare bayan sunyi sallah, nan ya fito ya wuce bangaren maza, yaran gidan sam basu da tarbiyya suna ganinshi fa amma kaf dinsu ba wanda yamai magana, kowa harkar gabanshi yakeyi, sai shine yace sannunku, kawai ya wuce dan dakin da yake zama, shi da Annur wanda yake karami ne shekarar sa 15 yanzu, Annur shima baya nan, jikinsa ne yai sanyi badai shima harya shiga sahun su ba?

 Ajiye yar jakarsa yai sannan yace “bazan iya zama anan ba, daga gobe gwara na dinga zuwa daga danbatta da safe, kwanciya yai yana jin haushin amsar aikin nan dayai.

 ********

 Haryai bacci baiga Annur ba sai da safe daya tashi ya ganshi yana bacci, tashinsa yai yace “sai a tashi a shirya ko?”

 Annur yana mikewa ya rungume Khalid yace “ya Khalid.”

 Khalid ya tureshi yana dariya yace “mutum dai ya tashi kafin ya makara.

 Annur yana dariya yace “jiya kawai na dawo naganka?”

 “Kana ina har wajen 11?”

 Annur yace “muna can muna hida da friends din mu.”

 Kamar Khalid zai sake magana sai ya fasa, shiryawa kawai yai ya dau jakarsa da niyyar zai dawo ya fita.

 Mota ya hau ya nufi gidan.

聽 Karfe bakwai da minti takwas tamai a cikin gidan, tsayawa yai a waje suka dan fara hira da mai gadin.

 A ciki kuwa Zainab ta gama shiryawa dan dama bata koma bacci ba, tana fitowa daga daki taga goggo ta fito tana murza ido, Zainab ta gaishet tana cewa “Goggo adan dai rage kallan nan, kamar yana yawa.”

 Tana fada ta nufi kitchen, Goggo tsayawa tai ranta yai mugun baci, harara ta bita dashi tace “wannan yarinya da ace ta hada jini da Ado da bamusan yana zata kareba, to sai kuma kikai sa’a bakuda hadi dashi yar kwal……”

 Ganin Zainab ne yasa ta kalleta ta saki dariya tace “Gwara dai ki tafi da ko dan shayin ne, amma ace mutum ko abincin safe baya ci?”

 Zainab tace “na wuce.”
“To adawo lafiya, dan Allah ki tahomin da goro.”

 To kawai tace ta fita, tana fita Goggo ta tabe baki tace “a haka dai, an kasa bani jika sai feleke kamar, kamar.”

 Ta kunna socket ta zauna tana cewa “dole nasha ruwan tea dan sam jiya ranta ya baci dasu Nusaiba suka dafa macaroni, haka tasha kunu ta kwanta.”

 Zainab na fita ta ganshi suna magana da mai gadi, agoggon hannunta ta kalla, bakwai da ashirin, sam bati tunanin ganinshi ba, ta fitone ta fara aiki a cikin mota kafin ya karaso.”

 Tsayawa tai a bakin kofar, yana ganinta ya nufo inda take, kusa da ita yaje ya mika mata hannu, kallansa tai tace “no am okay, zan iya dauka.”

 Ta fada tare da dauke kai, “no ina nufin key.”

Da sauri ta kalleshi, haushin kanta ya kamata, rikemin, ta fada tana mikamai tea din, ya amsa ta juya ciki, tana shiga ta fito, mikamai tai ya mika mata tea din sannan ya amsa ya wuce ya bude motar, wani irin kallo tamai sannan ta wuce ta shiga.

 Sun fara tafiya taga anzo kwana, kafin yai magana tace “nan zakai.”

 “Na gane hanyar.”
Juya kai tai dan dama batasan ya fara mata zancen left da right din nan ne yasata yin magana dan ba karamin haushi taji jiya ba.

 So take ta tsaya ta sai biscuit dan na office dinta sun kare, kallansa tai tace “Excuse me dan gangara gefen titi nan.”

 Neman gangarawa yake ta kara cewa “Excuse me daga dan can.”

 Karasawayai yai parking, ta fita daga motar, tana fitar tai murmushin jin dadi tace “kaji ko da dadi.”

 Shikam sam bai kawo komai ba, harta dawo ta shiga.

A cikin tv station din yai parking, ta kalleshi tace “zaka iya zuwa ka dawo, in ina bukatarka zan nemeka.”

 Okay.

 Shiru sukai sannan ta daure ta mikamai wayarta tace “zan kida Adam in na kusa gamawa.”

 Okay 
Ya kara cewa, fitowa tai ta shiga ciki.

 Tana shiga bakin gun ta hade fuska tamau, ko ina ta wuce gaisheta akeyi tana amsawa, kayanta kawai ta ajiye ta dawo ta hau aikinta.


***********

 Karfe sha daya ya farka? Mika yai sannan ya fito daga daki, yana tafe yana hamma, a falo yana goggo tana ta maka dariya, kallanta yai ya girgiza kai, ya matso yana cewa “wlh Goggo jin dadinki yayi yawa.”

 Kallansa tai tace “kai kuma fa? Wai kai dan Allah bakajin kunya? A matsayinka na namiji kullum a gida?”

 “Kedai kiyi kallanki dan ni ba kunyar da nakeji, ina wadancan yan rigimar?”

 Suna kitchen dan wulakanci sai yanzu suke abincin safe

 Dariya ya mata yace “to ai da ke kinyi Goggo ni me kikeyi ne a gidan?”

 Tace “amma in basa nan ai inayi, in suna nan kam bazan ma katti abinci ba.”

 Kai ya girgiza, ya mike yana cewa “Goggo ta tv ni wai kina kallan shirin sirikarki ma?”

 Tace “ina kallo mana, ba gwara ni ba kai sai karyar kana kalla bayan haryau bansan a inda kake kallan ba.”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button