HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 9

 

Halin Girma    9

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb

***

Yana jin sanda motar ta tsaya, ya juyo da sauri ya kalle shi, hankalin sa na kan wayar sa yana dannawa, fuskar sa a hade tsaf babu alamun wasa ko kadan, tsoro ne ya sake shigar Khalil din sosai, yaji kamar yayi ta kurma ihu yana neman taimako, amma kuma ya san babu wanda zai taimaka masa musamman idan aka zo aka ga wanda yake tare dasu. 

  Ji yayi an murda handle din bangaren sa, yayi saurin matsowa sai gashi a tsakiyar motar, daf da Moh, wani banzan kallo ya watsa masa da ya sakashi saurin komawa inda yake zaune.

“Come ou!” Wani murdadden soja yace matsa bayan kofar ta gama budewa, idanu ya soma rabawa tsakanin Moh da sojan fuskar sa ta nuna matukar tashin hankalin da ya shiga

“I said come out!” Ya daka masa tsawa da ta saka shi saurin fitowa

“Dan Allah Oga kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da rashin hankali, duk abinda na farfada ba wai har zuciya ta bane wallahi.” 

Ya hau magiya yana kallon Moh da yayi kamar baya wajen, damtsen hannun sa sojan ya kama ya shiga jan sa har zuwa wata kofa in da ya hangi sojoji sun fi su ashirin suna tsalle tsalle a wajen.

“Oga dan Allah ka bawa oganku hakuri Dan Allah!”

“Kasan waye oga kuwa?”

Da sauri ya girgiza kansa

“Ban sani ba wallahi, rashin sani ya jawo nayi masa abinda nayi amsa amma dan Allah na tuba yayi hakuri.”

Dariya sojan ya saka sosai

” Baka da hankali amma, ka zo har nan wajen kayi tunanin zamu kyale ka, ka tafi free? Nah sai mun dan sassamaka yadda gobe ba zaka kara ba. ”

” Dan Allah nace fa? Ka tayani bawa ogan hakuri. ”

” Naka wasa ne. ”

Yayi gaba yana rik’e dashi, yanayin rikon da yayi masa da yanayin jikin Khalil din zai baka dariya sosai, dama bashi da wani jiki sosai gashi kuma a hannun manyan maza, wani daki ya kaishi sannan ya sake shi yana masa dariyar mugunta

“Zaka kwashi kashin ka hannu yau, wallahi Oga zai iya sawa a batar da kai a k’asar nan, kasan waye kuwa? Tab.”

Jawo masa kofar yayi ya rufe ta har da key yana kwasar dariya.

  Chan karshen dakin yaje ya tsugunna yana jin dana sanin barin zancen da yayi, dama a maida baya da ya goge duk abun da yace ma Muhammad din cikin rashin sani. Ji yayi cikin sa na kara alamar ya lalace, ya tabbatar bala’in tsoro da firgicin da ya shiga ne ya saka cikin nasa lalacewa. Mikewa yayi da sauri ya hau zagaye a dakin yana maimaita 

“Innalillah wa inna ilaihi rajiun.”

Ji yayi ana murda key din dakin, ya tsaya yana kallon kofar cikin tsoro. Captain Moh ne ya shigo sojoji biyu na biye dashi a bayan sa, daya rik’e da kujera yazo ya ajiye masa ya zauna yana wa Khalil murmush

“Alhaji Khalil barka da warhaka.”

“Dan Allah dan Allah kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da yarinta wallahi amma ba zan sake ba.”

“Haba Khalil, so soon haka? Ka sani ko sojan gona ne ni, kasan fa talaka da samun wuri.”

“Wallahi ni dai ba zan sake ba, kayi min rai, mahaifiyta da ni ta dogara, dan Allah.”

“Calm down magana zamuyi, ka nutsu ka saurare ni, warning ne me hade da dokoki, ina fatan zaka bud’e kunnuwan ka kaji ni sosai.”

“Ina ji wallahi.”

“Babu kai babu abinda ya zama mallaki na, Ina nufin Fatima, ko a hanya ka hadu karka taba nuna ka santa balle har magana ta hada ku, a da nayi niyyar barka ka gwada sa’ar ka akanta, amma kuma a yanzu na gama yanke wa, baka kai na nemi abu tare da kai ba, dan haka ko son ta zai kashe ka sai dai ka hakura… ”

” Na biyu, a yau ba sai gobe ba zaka wuce in da ka fito, ba tare da ka bud’e bakin ka kace wa kowa komai ba, ina nufin, bakin ka ya zama kanin kafar ka, kar naji zancen a wajen kowa ciki har da ita yayarta ka da bata tsoron Allah. ”

” Last but not the list ka koma bakin aikin ka, ka rik’e mutuncin ka sannan bakai ba wulakanta kowa. ”

” Duk abinda ka fad’a wallahi zanyi, nayi alkawari, ni dai kar ka raba ni da mahaifiyata wallahi bata da kowa sai ni. ”

” I’m done with you, gashi nan take him back, ku tabbatar ya bar Kano kafin karfe shida na yamma. ”

Juyawa yayi cikin wani irin taku ya fice daga wajen, yana fita sukayi kansa

” Ai wallahi ba zaka shigo nan a banza ka fita bamu ci ladan ka ba. ”

Wani soja yace yana kai masa rankwashi.

” Tashi kayi frog jump. ” Dayan ya daka masa tsawa yana zaro belt dinsa. Da sauri ya hau yi yana hada zufa su kuma suna tuntsura dariya, sai da suka gajiyar dashi sosai sannan suka fito dashi suka sashi a mota suka maidashi har kofar gidan suka ajiye sannan suka tafi.

***Abba na zaune yaji text message ya shigo wayar sa, tunanin sa ma ko alert ne ya bud’e sai yaga sako daga bakuwar number da be sani ba, bud’e message din yayi ya soma karantawa

_” Dr. barka da warhaka, ya aiki? Allah ya taimaka. Dama wata magana nake son yi akan fatima, ina rokon alfarmar daka saka ido sosai akan abinda yake faruwa a cikin gidan, in sha Allah zaka gano wani abu da ya dade yana faruwa ba tare da sanin ka ba. Sai anjima a huta lafiya. “_

   maimaita karanta sakon ya dinga yi yana kokarin daidaita tunanin sa waje guda, waye ko wace wannan? Me sakon yake nufi? Me ya faru da Fatima din? Duk wadannan tambayoyin ne suka shiga yi masa yawo aka, be san me yasa ba, kawai sai yaji hankalin sa ya kasa kwanciya da abinda ya karanta. Tashi yayi ya fito zuwa falon gidan, ya k’wala kiran Iman din. Zeenat ce ta fito

” Ina Ummi? ”

” Ina ga tana wajen Gaji. ”

” Je ki kira min ita. ”

Fita tayi shi kuma ya cigaba da tsaiwa awajen har suka shigo a tare.

” Ki same ni a daki na. ” Yace yana juyawa tabi bayanshi, dariyar mugunta Zeenat tayi a tunanin ta wani laifin Iman din tayi dan sosai yanayin Abban ya nuna bacin rai.

A gefen gadon sa ya zauna, ta samu chan gefe daga kasa ta rakube tana tunanin dalilin kiran.

” Kina jina Uwata? Kina da wata matsala wacce ban sani ba? ”

Girgiza kanta tayi

” A ah Abba babu. ”

” Kalle ni nan, ni ne mahaifin ki, baki da wanda yafi ni bayan mahaifiyar ki, ki fad’a min gaskiya idan akwai wani abu da yake damunki.”

Zuciyar ta ce tayi rauni, taji kuka na taho mata, ta k’asa rike shi kawai ta fashe da kuka. Dafe kansa Abban yayi, ya shiga tunanin me yake faruwa? Wanne irin abu ne haka da har shi ya kasa ganewa? 

“Fatima…” Ya kira ainihin sunan ta a karo na farko a rayuwar ta 

“Na’am.” Ta amsa cikin muryar kuka

“Kowanne bawa da irin yadda rayuwa take zuwar masa, kiyi hakuri zanyi bincike, sannan akwai shiri da nake yi na kaiki wajen mahaifiyar ki da zarar maganar bikin ku ta tabbata, nayi mata alkawarin kai mata ke da zarar lokacin auren ki yayi, mahaifiyar ki na son ki fiye da yadda take son kanta, ki rik’e wannan.”

” Tashi kije kinji, ki daina kukan haka.”

Tashi tayi bayan tace

” Nagode Abba.” Ta fice ya bita da kallo yana jin kamar be kyauta mata ba.

Dakin su ta wuce ta tarar da Zeenat na waya har da shewa, juyawa tayi zuwa store ta zauna a gefen katifar ta, tayi kuka sosai har sai da taji babu abinda yayi saura a zuciyar ta. Tsawon lokaci ta sauka a ciki har sai da taji maganar Mama tana fad’a a waya anan ta gane ta dawo dan dazu bata gidan. Tashi tayi ta fice ta kofar baya bayan ta gyara fuskar ta a sink din kitchen.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button