Bola TinubuLabarai
Tinubu Ne Kawai Zai Iya Gyara Najeriya – Inji Gwamnan Legas


Rahotanni daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar ya bayyana cewa Jagoran APC Asiwaju Bola Tinubu ya san matsalolin Najeriya kamar tafin hannunsa kuma shi kadai zai iya gyaran su.
Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a jihar Legas yayin taron hadin kan yan majalisa dokoki da yan majalisar zartaswar jihar kan zaɓen Siyasar 2023 dake tafe Aminiya ta rawaito.
Ya ce Tinubu ya sadaukar da kansa wa al’ummar Legas lokacin mulkinsa matsayin Gwamna da kuma Najeriya gaba daya. Yace: “Gaskiya lokaci yayi da zamu biyashi da goyon bayanmu. Ko shakka babu shine wanda ya cancanci aikin. Ya san matsalolin kasar nan kamar tafin hannunsa kuma yana da asirin gyara ta.”
“Saboda haka, lokaci yayi da za’a tura dan Legas birnin tarayya.” “Shiyasa nake kira gareku mu tabbatar da cewa mun yi duk mai yiwuwa don taimakawa Asiwaju Bola Tinubu ya zama shugaban kasa.”
[ad_2]