Wata Uwa ta kona hannun ‘yar ta mai shekaru 5 saboda ta cinye mata Kifi na siyarwa
Tina Idoroyen wacce ta ke a titin Gregory, unguwar Ikot Ansa a karamar hukumar Calabar ta jihar Cross River.
Matar mai sayar da kifi ta ce, ta shirya kifi guda 19, domin sana’arta, sannan ta fita, amma sai kifi guda daya kawai ta tarar bayan ta dawo.
Ta gano cewa ’yarta mai shekara 5 ta cinye kifin, domin haka ta hukunta ta ta hanyar tsoma hannunta cikin ruwan zafi, in ji Guardian.
Counsel to Basic Rights Counsel Initiative (BRCI), kungiya ce masu zaman kansu, kuma wadda mai kula da sashin yara, Mista James Ibor, ya yi zargin cewa, mahaifiyar ta yarda cewa yarinyar ba ta ci abinci ba kafin ta ci kifin, wanda hakan ya nuna cewa da alama yunwa ta ke ji.
Ya ce:
“Mahaifiyar ta yi zargin cewa, ‘yarta ‘yar shekara biyar ta sace kifin ta, domin haka ta tsoma hannunta a cikin wani ruwan zafi mai tsananin gaske, haka ta mayar da martani kan zargin satar.
Matar ba ta da komai, mahaifin yaron ya yi watsi da su shekaru biyu da suka wuce, kuma har yanzu ta na da wata ‘yar shekara takwas.
Mista Ibor ya ce ba a kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda ba, saboda yarinyar na bukatar tallafi da kulawar mahaifiyarta yayin da ta ke asibiti ta na jinya.
Ibor, wanda ya bayar da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba za a mika wanda ta aikata laifin ga ‘yan sanda, domin gurfanar da ita, ya kuma bayyana cewa an dauke yarinyar daga wani asibiti mai zaman kansa zuwa babban asibitin Calabar, inda kwararru ke kula da lafiyarta.
Daga DalaFmKno
[ad_2]