Labarai

Najeriya Ba Ta Taba Dacen Shugaba Mai Nagarta Kamar Buhari Ba —Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce Najeriya ba ta taba samun shugaba kasa mai nagartar Muhammadu Buhari ba.

Masari ya ce tun da  turawan mulkin mallaka suka hade Kudanci da Arewacin Najeriya a shekarar 1914, Najeriya ba ta taba dacen shugaba nagari kamar Buhari ba Aminiya ta rawaito.

Ya yi wannan furuci ne a yayin da ya ke jawabi a gaban wani gangamin cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na tabbatar da daidaito a wajen rabon albarkatun kasa ranar Asabar a Katsina.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da suke shan matsin lamba daga hare-haren ‘yan bindiga da satar shanu.

Sakamakon kamarin da matsalar ta yi ne ma, wani lokaci a baya gwamna Masari ya ce lamarin ya fi karfin hukumomin tsaron kasar nan, inda ya yi kira ga al’ummar jihar da su dauki makami don kare kansu.

Dubban mutane ne dai ‘yan bindiga suka kashe, ko suka sace  su don karbar kudin fansa a Katsina da sauran jihohin arewa irin su Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Kaduna, Neja da sauransu.

 

 

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button