Yan Sanda Sun Budewa ‘Yan Shi’a Wuta A Garin Zaria Hotuna

Yau Juma’a 29/4/2022 Ƴan shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun yi zanga-zanga da suka saba duk Juma’ar karshe a watan Ramadan, sun yi wannan zanga-zangar ne a garin Zaria da sauran garuruwa na sassa daban-daban na kasar nan.
A garin Zaria dai Ƴan shi’ar sun fito kwan su da kwarkwatan su Inda suka fito mazansu da matan su manya da yara domin nuna wa duniya irin damuwan su akan kisan da Isra’ila takeyi wa Al’ummar Falastine tare da kwace masallaci da uku a daraja wato masallacin
Kudus
Ƴan Shi’ar dai sun dauko Muzahharar tasu ne tun daga masallacin juma’a na kwata dake kasuwan sabon gari Zaria, suna tafiya suna faɗin Free Palastinu, hannayen su dauke da tutoci kalar tutar Palastine, tasowar su keda wuya ƴan sanda suka buɗe musu wuta inda suka harbi wasu tare da jikkata wasu da yawa.
Wannan dai zanga-zangar lumanar sun sabayin ta ne duk shekara domin nuna goyon bayan su ga al’ummar Falasɗinawa da Isra’ila ke musu kisa ba dare ba rana tsawon shekaru, Mabiya mazhabar shi’ar dai suna kiran wannan zanga-zangar ne da Muzahharar Qudus.
[ad_2]