NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 38

*_NO. 38_*


…………Ɗif wutar data haska falon ta ɗauke saboda tasowar hadarin daya gauraye garin, Ummukulsoom ta fisge hannunta jin ya sassauta riƙon da yay
mata saboda laluben waya da yake zai kunna fitila, ƙokarin barin falon tayi, dan haka ta fara laluben hanya zata gudu, cikin sa’a ta taɓa ƙofar, sai dai kamar an saita da maido wuta.
     Hasken daya mamaye falonne yasata juyowa jin yana takowa inda take yana dariya.
     “Yaya Zaid?!”. ‘Ta faɗa cike da mamaki da tsantsar ruɗani tana binsa da kallo, gaba ɗaya idanunta sun firfito saboda tashin hankali, mi hakan ke nufi?’.
     Bakinta na rawa tace, “Yaya Zaid kana nufin kaine Abdul-Waheed ɗin?”.
       Murmushi yayi tare da ɗaga mata facemask ɗin daya cire daga fuskarsa.
    Takuma waro idanu tanayin baya tamkar zata faɗi, ALLAH dai ya bata sa’a tai azamar dafe bango, da baya baya ta ringa tafiya har ALLAH ya bata nasarar buɗe ƙofar ta fita da gudu zuwa cikin gida hawaye na ƙwarara a kan fuskarta.
      Dafe kai Zaid yayi yana sauke nannauyan numfashi, ya zube a saman kujerar dake kusa dashi saboda wata hajijiya da yakejin tana neman kwasarsa ƙasa.

        Ummukulsoom na shiga ta faɗa jikin Bily dake falo zaune ta kuma fashewa da sabon kuka, gaba ɗaya Bily ta rikice, sai tambayarta lafiya? Takeyi, amma sam taki magana.
      Motsinsu Maman Ahmad taji dan haka ta fito daga kicin a hanzarce.
     “A’a, Ummukulsoom lafiya kuwa? Yaya da kuka haka?”.
     “Wlhy nima bansan mi akai mataba Aunty, haka ta shigo tana kuka”……
     Shigowar Zaid ce ta katse musu maganarsu, dukansu suka kallesa har Ummukulsoom ɗin dake hawaye, ta miƙe zumbur zata bar falon yay saurin shan gabanta.
       A tsawace tace, “Yaya Zaid baka da abin faɗa mini, a zatona idan kaga wani zaimin hakan haushi zakaji, amm…..”
     Hannu ya ɗaga mata alamar dakatar da ita, “Ummukulsoom ki tsaya ki saurareni, sam ba yanda kike tunanin baneba, bani bane Abdul-Waheed, shi daban ni da ban wlhy kinji na rantse miki”.
     hawayenta ne suka tsaya cak daga zirarowar da sukeyi, ta tsira masa idanu alamar neman ƙarin bayani.
    Da hannu ya nuna mata wajen zama, kamar bazata zauna ba sai kuma Bily ta kamo hannunta ta zaunar, shima zama yayi, Maman Ahmad da Bily suka barmusu falon.
         “Kiyi haƙuri Ummukulsoom banso ɓata miki rai ba sam, nayine dan kawai na gwadaki akan soyayyar da nake miki, dan nasan kin fahimci ina sonki amma kike zillemin, wlhy sam banine Abdul-Waheed ba”.
       “To wanene?”.
Murmushin takaici yayi yana miƙewa tsaye, ta bisa da kallo ranta na ƙara ɓaci, sai da yay taku biyu zuwa uku sannan ya juyo yana fuskantarta.
     “Zuwana na ƙarshe gidannan na fahimci baƙon al’amari daga gareki, na karkatar hankalinki ga wanina bayan Umar kuma, hakan yasani bincikar wayarki ba tare da kin saniba harna samu Number Abdul-Waheed, har office ɗinsa na samesa tareda kora masa gargaɗin ya rabu dake, inba hakaba komi ya biyo baya yay kuka da kansa, naga alamar damuwa a garesa ƙarara, dan har roƙona yayi akan dan ALLAH kar nai masa haka, shi sonki yake tsakaninsa ga ALLAH. kuma aurenki zaiyi, shiyyasa ya barkima ki nutsu a karatunki, har saikin gama yafara fuskantarki. Sam ban sauraresa ba, nakuma ja masa dogon gargaɗi nabarosa, tundaga wannan lokacin nafara tunanin ta hanyar da zanzo miki, saina fahimci kinason Abdul-Waheed sosai, wannan yasani amfani da wannan damar nazo miki matsayin shi saboda maganar aure da baba yay mana, na kiraki yafi a ƙirga muyi magana kinƙi saurarena, saina bincika ta hanyar Bily ba tare da itama tasan manufar hakanba, ita ta sanarmin kina shirin bama Abdul-Waheed dama fa, hankalina ya tashi sosai dan kuskuren danayi shine ban saka Abdul goge Number kiba, kekuma ban goge a nakiba, namanta koda namasa katanga da zuwa wajenki dolene zaku cigaba da mu’amula ta waya fa, kiyi haƙuri Ummukulsoom Please, nasan ni mai laifine a gareki”.
     Wani ƙududun takaicine ya maƙale numfashin Ummukulsoom, dama yaya Zaid ne yay ma Abdul-Waheed katanga da zuwa wajenta? Bawan ALLAH tanata zarginsa da wasa da hankalinta ba tare da ta sani ba, da gudu ta shige ɗakinsu ta barsa nan tsaye ko waigowa batayiba dukda kiran da yaketa ƙwala mata kuwa.
      Attahir dake tsaye bayansu ya kafe Zaid da ido yanason gano gaskiyar zancensa, Zaid dayaji motsi a bayansa ya waiyo suka haɗa ido da Attahir, ƙasa yay da kansa na jin nadamar abinda ya aikata.
     Attahir ya girgiza kansa yana faɗin, “Ya maka ƙyau Zaid, ƙanwarka zakazo kana ma wasa da hankali ko?, ashe dama tun jiya ka shigo lagos amma kamin ƙaryar yaune zakazo ko?”.
      “Kayi haƙuri yaya, nayi kuskure, amma nayi nadama, tunda bata sona kuma na barta”.
    Ƙala Attahir bai ce masaba yay gaba zuwa ɗakin su Ummukulsoom.
    Sai da yay sallama suka amsa sannan ya shiga, Ummukulsoom na kwance jikin maman Ahmad tana kukan takaicin Zaid.
      Bakin ƙofa ya tsaya ya tsura mata idanu, kafin ya saume numfashi ya ƙarasa takowa cikin ɗakin sosai, saurin tashi Bily tai ta basa stool ɗin mirror ya zauna.
        “Ummukulsoom tashi zaune”.
    Babu musu ta tashi zaune tana share hawayenta.
     “Wanene Abdul-Waheed ɗin?”.
     Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta bashi labarinsa, Attahir dake saurarenta sai jinjina kai yakeyi, “Ummukulsoom kin tabbata kinason Abdul-Waheed a matsayin mijin aure?”.
      Ƙasa ta kumayi da kai alamar jin kunya, hakan ne ya saka Attahir fahimtar tana son nashi.
    Yaɗan murmusa yana miƙewa, “Nima na goyi bayan ki bashi dama, dan nasan da Zaid bai aikata daƙilesa ba da tuni yafara zuwa gidannan, amma nabaki dama kiyi tunanin acikin kwanaki Uku kacal, dan Abba sati biyu nikuma ya bani akanku”.
    Kanta ta jinjina masa alamar amsawa. 

      Yana fita maman Ahmad ta kalli Ummukulsoom da kulawa.
      “Ummukulsoom yanzu ke kinason Abdul-Waheed ɗin?”.
     Kallonta Ummukulsoom tayi tana guntun murmushi, “Aunty idan nace miki bana sonshi nayi ƙarya, sai dai rashin mu’amulantata azahiri da yake shike sakani jin rauni akansa, tayaya zan bashi dama bayan bansan halinsa ba, sau ɗaya kacal muka taɓa maganar fatar baki dashi, daga nan ko’a makaranta muka haɗu bama magana, sam ban fahimci nasa tsarinba nikam”.
        “indai dan wannan ne inaga ba abin damuwa baneba, dan lokaci bai ƙureba a gareku, ayanzu haka zaki iya buƙatar ganinsa, shikuma zaid Abban Ahmad nasan zaimasa magana yaje ya janye gargaɗin da yay masa na hanashi zuwa gareki ko kuwa Bily?”.
       Baki Bily ta turo gaba cike da jin haushi, “Nifa wlhy danma tawani dage ne, amma mizai hana ta koma gidan yaya Amaan, itama hankalinta sai yafi kwanciya wlhy”.
      Harara Ummukulsoom ta makama Bily, rai a ɓace tace, “Bilkisu idan har bason mu sami matsala kikeba kidaina sakomin mutumin nan a lamarina, ni nace mikine sonsa nake ko buƙatar sake zama dashi? Wancanma umarnin iyayene, kamar yanda yace shi da mahaifiyarsa da ƴan uwansa wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa a tsakaninmu to nima hakance yanzu a gareni, ko ɗauramin shi akayi saina since shi, Abdul-Waheed ɗin dai da baƙyaso dashi zan rayu insha ALLAH ”.
      Baki Bily ta taɓe tama fice daga ɗakin ta barsu tana jan tsaki.
     Itama Ummukulsoom tsakin tayi, ita maman Ahmad ma sai suka bata dariya.

★★★★

        Gaba ɗaya lamarin yazoma Ummukulsoom da ruɗani, dan ita dai da farko sai taga kamar ba Zaid baneba, amma bayanin da yay mata yasata gazgata maganarsa, musamman data turama Abdul-Waheed massege akan tana son ganinsa. saiya bata amsa da,
         *_“Ummuna yayanki yamin shamaki dake, dukda zuciyata na tsananin ƙaunarki, tunda kika turomin maganar aurenki ina cikin tashin hankali mai tsanani, dan ALLAH ki bani damar fuskantar iyayenki._*
     
       Bayan taga wannan saƙon saita sharesa batareda ta masa reply ba, kusan kwanaki biyu da faruwar hakan sai gashi ya kirata, abin ya bata mamaki, dan tunda suke bai taɓa kiranta a waya ba sai yau.
         Ɗagawa tayi jiki a sanyaye, su duka sukai shiru na wasu sakwanni, kafin daga can ya ɗan sauke numfashi murya ƙasa-ƙasa yace, “Assalamu alaiki”.
     Amsawa Ummukulsoom tai zuciyarta na wani irin harbawa, amma saita danne tana saita numfashinta tana gaidashi.
        Yanzunma a taƙaice ya amsa mata, hakan saiya kuma bata mamaki, amma sai ta share itama tai shiru. 
    A haka suka kuma cinye wasu seconds ɗin, harma ta fara tunanin yanke wayar taji yace, “Insha ALLAHU inason zuwa gareki inhar yayanki ya amince”.
     Ɓoyayyar ajiyar zuciya Ummukulsoom ta sauke, maimakon ta amsashi sai kawai tace, “Humm”.
     Sosai yaji Humm ɗinnan har cikin ransa, dan itamafa ya kula ba kanwar lasa bace, sai dai jan ajinta ke ƙara wutar sonta a ranshi sosai…
     Kuma katse shirun nasu yayi da faɗin, “Ban gane Humm ba?”.
     “To mikakeso nace maka nikam? Ni a ganina ya rage naka kazo a lokacin daya dace ko kazo a makare, ni dai a gareni babu fashi wajen bin umarnin iyayena”.
    Daga haka ta yanke wayar tama kasheta gaba ɗaya tanajin takaicin halayyar maza, kowa da kai tamkar giginya da tasa matsalar, taja tsoki tana miƙewa daga gaban mirror ɗin domin sanya kaya, dama wanka tayo tanason zuwa wankin kai ne.
       A gaba ɗaya kwanakin nan maganar auren nan ta dagula mata lissafi, sam batai niyyar yin aure a nan kusaba, amma bazata iya bijirema iyayenta ba, dan baba yamayi ƙoƙari daya amince mata taci gaba da karatunnan, abinda ba’a taɓayi ba a garinsu, yanzu haka da ansan matsayinta a garin da ko ruwa ba’a barta tashaba saboda surutai da za ai ta mata itada baba.

*BAYAN KWANA BIYU*

       Kamar yanda Abdul-Waheed ya alkawarta yay mata massege akan yau zai zo.
      Dan kawai ta baƙanta ran Yaya Zaid da har yanzu bai koma ba ta shirya tarbar Abdul-Waheed, harma fatan Amaan ma ya gansu tare take, dukda ma ita a tsakanin nan gaba ɗaya bata ganinsa, taji dai kamar ranar Attahir na faɗin yaje kaduna.
        Da taimakon maman Ahmad aka shirya masa abinci mai ma’ana mai kuma sauƙi, dan Bily catai batayi, ita gaba ɗaya batason wani Abdul-Waheed, tafiso Ummu ta zaɓi Zaid ko yaa Amaan, rashin dawowar Umar ma ba ƙaramin daɗi yake mataba.
        Shareta Ummukulsoom tayi, suka gama tsaf sannan ta wuce yin wanka, kamar kullum yauma bawata kwalliya ce tayiba, sai dai tayi ƙyau masha ALLAH, ga ƙamshinta mai daɗi tana fiddawa. 
        Huɗu da rabi dai-dai ya turo mata massege akan ya iso, da kanta ta fito ta sanarma Maman Ahmad.
     Maman Ahmad ta kalli bily dake zaune ta saurarensu sai kumbura take, dariyar dake cin ranta ta danne tace, “Yi haƙuri aunty B ɗinmu dan ALLAH ki kaisa falon baƙi kafin ta ƙaraso”.
    Kuma kumbura Bily tayi, “Nifa gaskiya Aunty ki…..”
     “Yi haƙuri Aunty B ɗinmu, ai har yanzu Bestie ɗinki allura ce cikin ruwa ko”.
     “Aunty kuna wani goya mata bayane keda Yaya Attahir za’ace allura cikin ruwa?”.
     “Ai komai sonmu data auri Abdul idan ba mijinta bane bata aurensa wlhy”.
      Dariyar ƙeta Bily ta sanya tana cewa, “Insha ALLAHU ma bazata ƙulluba wannan igiyar” tai maganar tana yima Ummukulsoom gwalo sannan ta fice.
     Hakan saiya soki zuciyar Ummukulsoom, taji a ranta kai tsaye zata bama Abdul-Waheed dama dan kawai ta cusama bily takaici.
  
      Sai da bily ta dawo da kusan minti huɗu sannan Ummukulsoom ta miƙe ta fice ɗauke da tire.
      Haka kawai taji zuciyarta na ayyano mata abinda ya faru ranar tsakaninta da Zaid, saurin kauda abun tayi a ranta tareda karanto addu’a sannan tai sallama.
     Sassanyar muryarsa dake saka Ummukulsoom shiga ruɗani ta ce ta amsa, ta ɗan rumtse idanunta sannan ta shiga.
      Zaune yake ƙafa a harɗe, kansa a sunkuye yana danna waya, ƙamshin turarensa dukta cika falon.
     Sai da ta ajiye tiren sannan ta kuma satar kallonsa, yana sanye da farin yadi mai ƙyau harda hula, sosai yayi ƙyau a asalin bahaushensa, Abdul-Waheed ɗintane tabbas, hakan saiya saka zuciyarta samun nutsuwa, sai dai tana mamakin bugun da zuciyarta ke ɗanyi da sauri-sauri.
         Kallonta yake ta cikin eyeglasess ɗin fuskarsa mai cike da kwarjinin cikar kamala, sam fuskarsa babu walwala.
    Sai dai hakan bai damu Ummukulsoom ba, dan ayanda ta lura dashi haka shima yanayinsa yake kamar Ama…, kasa ƙarasa sunan tayi dukda a zuciyartane kuma.
         Ganin kallon da yake matane yasata cewa, “Ina yini”.
      Ya janye idanunsa daga kanta yay luu har zai lumshe sai kuma yay azamar buɗewa.
   Kaɗan ya rage numfashin Ummu ya ɗauke, dan ba ƙaramin rikita zuciyarta taso shigaba ganin yanda yay da idanu, sai dai buɗewar da yay batare da ya lumshe ba ne ya sa ta saume ɓoyayyar ajiyar zuciya.
       Shi kansa ya kula da halin data kusa shiga, yay saurin kauda yanayin da faɗin, “Ko ba’ai murna da ganina bane gimbiya?”.
     Murmushi Ummukulsoom tayi kawai, amma batace komaiba.
    Ya ɗauke idanunsa daga kallonta yana ɗan furzo iska a bakinsa, “Nasan akwai tarin tambayoyi a bakinki akaina, sai dai nima bazanso kimin suba kulsoom, dama kawai nake buƙata”.
       Batare da ta kallesa ba tace, “Miyasa bakason na tambayeka? Bayan kuma waɗan nan tambayoyin sune abu mafi cin zuciyata a tarayyata da kai”.
     “Nasan da hakan Kulsoom, sai dai sam bansan taya zan baki kowacce amsaba idan kinmin”. ‘ya ƙare maganar yana ɗan dafe kai’.
     Kallon mamaki Ummukulsoom tai masa, dan sosai taga alamun ƙosawa da magana a tattare dashi.
    Ta ɗauke kanta kawai zuciyarta na kuma tsunduma a wasiwasi.
       Shiru duk sukayi babu wanda ya sake tankawa, zuwa can ya kuma kallonta ya janye idanunsa, “Baki ce komai ba”.
       “Humm” ta faɗa kawai tana basarwa, kamar bazata tankaba sai kuma tace, “Bansan mizan ce ba nima, kamar yanda na lura kaima bakinka babu abin faɗa”.
      Lallausan Murmushi taga ya saki a karo na farko, sai dai badan kallonsa takeba ma bazata taɓa fahimtar yayiba, yakai hannunsa a saman ido sai kuma yay azamar waskewa ya dafe kansa…
     Tsira masa idanu Ummukulsoom tayi tsoro na kuma bayyana karara a fuskarta.
       “Ba abin faɗa bane babu, yanda za’a faɗa ɗinne matsalar”. ‘Yay maganar cikin basar da ita’.
       Janye idanunta tayi tana sauke ajiyar zuciya a hankali, “Abdul-Waheed kenan, to ni dai yanzu mike tafe da kai?”.
      Sai da ya gumtsi iska ya fesar yana mata wani kallon ƙasan ido, kafin yace, “Maganar aure”.
      Ta ɗan taɓe baki, “Ai banga alamar hakanba”.
       Idanu ya tsira mata yana kuma ƙoƙarin control ɗin face ɗinsa wajen sakinta, “Ban cika son nuna lamarina a zance ba, ki bani dama ta halattacciyar hanya kawai”.
        “Miyasa da sauri haka?”.
    “Saboda nafi kowa buƙatarki”.
      Murmushi Ummukulsoom tai taɗan basar, “Baka tunanin bakai kaɗai bane a filin dagar?”.
      “Sanin hakan ne yasani tahowa da ƙarfina”.
     “Banda cika baki dai”.
Shiru yay bai amsaba, alamar yakai maƙura.
      “Yakai shiru? Ko dai bazaka iya takararba?”.
      Bakinsa yaɗan motsa, amma yarasa abinda zaice mata, sai kafeta da idanu da yayi.
           “Yawan magana akwai wahalarwa ko?”.
    Da mamaki ya kalleta, karfa yazam kallon ƙitse akema juna? Ya faɗa a ransa. A fili kuma saiya jinjina mata kai alamar A’a.
      Tai murmushi dan ita haka kawaima saiya bata tausayi, wannan kam da a kd suka haɗu babu abinda zai hanata yarda basuda alaƙa da Dad, dan halayyar tazo ɗaya…….
        Katse mata tunani yay da faɗin, “Ba maganar wasa ya kawoniba kulsoom, inason tura iyayena gidanku a satin nan”.
        Kasa amsashi tai, sai zuciyarta ke mata kaikawo akan ta amsashi koko ta ƙara jansa?….
      “Dan ALLAH karkice A’a”. Ya faɗa a hankali can ƙasan maƙoshi.
        “Ai baka ci jarabawa ko ɗayaba”.
    “A jinkirta min ita mana har sai na gama nutsuwa waje ɗaya”.
    “Minene matsalar?”.
“Mahaifiyata nason na auri watanki, bayan kin mamaye ko ina”.
       Kallonsa tai na wasu seconds tare da janye idanunta.
   Yayinda shikuma ya dafe kansa saboda tsantsar ƙosawa yana tsoron kar akai maƙura komai ya buɗe…..
     “Zanyi tunani”. Ummukulsoom ta faɗa cikin katsesa.
     Kansa ya rausayar gefe batare da yace komaiba.
     Ganin hakan ne yasata miƙewa tana faɗin, “Bismillah kaci zwani abu ina zuwa”. Bata jira cewarsa ba ta fice.

     Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke bayan fitarta, ya maida kansa ya jingina da kujera yana lumshe idanu………..✍????


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

????????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863


*_ƴan Niger kuma_*

_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*

*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*

 _TA NUMBER;_
 *+22795166177*   


Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button