Uncategorized

HEEDAYAH 15

 Abba ne xaune main parlor bayan isha, lkci lkci yake kallon agogon dake manne bangon parlon, Mami ta fito daga part dinta sanye da hijab har kasa 

ta karaso cikin parlon tace “Good evening Barrister” yana kallonta yace “Good evening Rahinah” xaunawa tayi one sitter dake parlon tace “Gani” Abba 

yace “Me ya sa kika dau lkci baki fito” tace “Putting things in other” Bai ce komai ba, ya kalli hanyar kitchen don Mumy na ciki, tun daxu take kai 

wa take komowa ko gaisuwa bai hadata da shi ba tun shigowarsa, shi kuma hakan bai hanasa ce mata yana da magana a parlor da ita da Mami ba, xata 

sake komawa kitchen daga bangarenta yace “Maryam” juyowa tayi fuska daure tana kallonsa bata ce komai ba, yace “Ke muke jira” Tana masa wani kallo 

ta karaso cikin parlon tace “Ni ku ke jira? in maku me? A kan me ma xa ku jira ni? Nace maku ina da wnn lokacin ne? Plss I have more important 

things to do then sitting and staring at you both, bani da wannan lokacin barrister….” Ta juya xata bar wajen, rai bace yace “Ina magana xa ki 

wuce?” Juyowa ta sake yi tace “Bbu tasirin da maganganun ka xa su min barrister, in xauna kace xaka mana nasiha ko me? Did I tell you I need that, 

ita dai xaka xaunar ka ja ma kunne ta tsaya iya matsayinta a gidan nan kar ta ce xata yi karambanin xuwa kusa da nawa matsayin, matsayina daban 

nata daban, ni uwar gidanka ce kuma uwar ‘ya yanka, ita kuma uwar rainon yar tsintuwar ka ce, wa enda xaka dinga ciyarwa, kaga banbancin kuwa ba 

karami bane, idan tace xata yi gigin matsowa lane dina ita xata kwana a ciki, so bbu wani xaunawa da xan yi ka hada mu kayi magana, bata kai 

matsayin ba, ga most important maganganun nan duk nayi, sai dai kawai tayi taking caution, ka kara mata da wanda xaka kara mata” Tunda ta fara Abba 

ke kallonta, Mami tayi yar dariya tace “To ai da sauki tunda kamar yanda xa a kira ki matarsa haka nima xa a kirani ynxu, kuma tunda baki isa korar 

yar tsintuwa ba balle ni Alhmdllh, muna nan sai mun xame maki kadangaren bakin tulu, xa ki gane matsayina da naki bai kai banbancin da xa ki dinga 

bragging ba….” A fusace Mumy ta karaso kusa da ita tana huci tace “Karya kike wllh, nace karya kike…” Tsawa Abba yyi mata yace “Kina da hankali 

Maryam??” Mami ta mike tace “Ina fa, sai dai in koya mata cikin yan kwanakin nan….” Daga haka ta bar masu parlon ta wuce bangarenta, Mumy ta 

fashe da kuka tace “Ka cuceni barrister, ka ci amanata, ka rasa warce xaka auro ka kawo mana gida sai yar bariki….” Mikewa Abba yyi ya dakatar da 

ita in few seconds ta hanyar nuna ta da yatsa strictly yace “Don’t you ever try that again Maryam….” Bai jira cewarta ba ya bar parlon. Mami ce 

xaune that same night tana kallon Heedayah tace “Ina jin ki…” Heedayah ta marairaice tace “Tea kawai….” Mami tace “Kece kike cewa kina son tea 

din kenan” Heedayah ta girgixa kai tace “Ammi na ce take bani in sha da daddare” Mami tace “To da safe fa?” Tace “Tea and bread and egg” Mami tace 

“Da rana?” Heedayah tace “Indomie” Mami tace “Sai kuma da daddare ki sha tea” Kai Heedayah ta gyada mata, Mami tace “Toh after this night baxa ki 

sake shan shayi ba duk abinda aka dafa aka baki shi xa ki ci is that clear?” A hankali Heedayah ta gyada mata kai, Mami ta mike ta dauke fried rice 

da chicken dake cikin plate da Heedayah ta ki ci wai sai tea ta nufi kofa ta fita, hanyar kitchen ta nufa ta bude kofar kitchen din, tsaye ta ga 

Shuraim gaban kettle din ruwa alamar tea xai hada don ga kayan shayin a ajiye gefe, ta kasan tiles yake kallon wanda xai shigo kitchen din, yana 

ganin wacece kuma ya kauda kai ya ci gaba da abinda yake, Mami ta ajiye abincin hannunta ta nufi inda cups suke ta dau daya da cokali, ko kafin ta 

juyo har ya fice daga kitchen din, karasawa tayi gun kettle din ta juye ruwan ciki a cup din ta bude kayan shayin ta hada tea sannan ta fita 

kitchen din, Khadijah ta gani parlor ta shigo daukan takardunta, tana ganin Mami ta kwashi takardun ta wuce bangarensu da sauri, Mami dama tun da 

ta kalleta sau daya bata sake kallonta ba har ta wuce nata bangaren, sai da shayin ya huce sannan Heedayah ta sha Mami ta sa ta kwanta nan da nan 

bacci ya dauke ta. Washegari Saturday tun kafin yan gidan su tashi bacci Mami ta hada ma ita da Heedayah breakfast, da yake abinda Heedayah take so 

ne tsaf ta cinye komai, Mami dai sai kallonta take, sannan tace “Kin koshi ae?” Heedayah ta gyada kai, Mami ta mike tace “To mu je ki gaida Abba” 

har parlon Abba Mami ta kai ta, Abba dake aiki system ya daga kai yana kallonsu, Mami tace “Weldone” yace “Har ina tunanin kawo maki ki karasa” 

tace “Noo nima ga nawa can” yyi murmushi yace “Akwai maganan da nake son xa mu yi Rahinah” tace “Alright, but before then nima ina da magana da 

kai” yace “Yanxu?” Tace “Later…” Abba ya xaunar da Heedayah gefensa yace “How are you my dear” tana washe hakora tace “I’m fine” Mami tace “Baki 

yi gaisuwa ba” tace “Abba ina kwana” yace “Lafiya lau daughter” Mami tace “Let me freshen up” daga haka ta fita parlon, yana kallon Heedayah yace 

“Wa ke koya maki English” tace “My teacher” ya d’an bude ido yace “Really?” Tace “Ehh” Abba yace “Me da me yake koya maki kuma a ina yake koya 

maki?” Heedayah tace “Ammi tace min she’s a Female, tana koya min komai da komai a gidanmu” yace “Wani sura kike?” Da sauri tace “Jinnnn” Abba na 

gyada kai so impressed yace “Kullum take xuwa koya maki?” Heedayah ta gyada masa kai, Abba xai yi magana aka bude kofar, Shuraim ne ya shigo parlon 

da sallama yana sanye da jallabiya, Abba ya amsa, xaunawa yyi nan kasa gefen Abbansa yace “Ina kwana Abba” Abba yace “Lafiya lau” Heedayah tace 

“Abba har da boko take koya min ma….” Satan kallonta Shuraim yyi ya kara hade rai, Abba na kallonta yace “Toh xan kawo maki warce xata dinga koya 

maki a nan gida” Heedayah ta wara manyan idonta tace “Thank you Abba, but…” Yace “But what?” Tace “Yaushe xaka kai ni wajen Ammina? Kila tana ta 

nemana” a sanyaye tayi maganan, Abba ya shafa kanta yace “Ina sha Allah xan kai ki, har yanxu ana neman Ammin taki” Tace “Abba ai gidan Yakumbo 

take” Abba yace “Eh ban manta ba xa mu je can” Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa yace “Sai anjima Abba” Abba yace “Da yaushe kake yi ma su Khadijah 

karatun qur’ani” Juyowa yyi yana kallon Abban nasa, ganin kallonsa Abban ma yake yace “Da asuba” Abba yace “Ohk, Heedayah will join also, sai ka 

dinga masu gaba daya” dawowa yyi ba tare da ya shirya ba ya durkusa inda ya tashi yace “Abba ai na kwana biyu ban koya masu ba” Abba yace “Eh to 

sai ka dinga yi mata ita kadai tunda ba Islamiyya xata je ba, su kuma dama suna xuwa islamiyya” Kasa cewa komai yyi yana kallon Abban nasa, 

Heedayah tace “Abba a suratul jinn nake” Abba yace “Eh daga nan xa ku ci gaba” Shuraim yyi karfin halin satan kallonta, Abba yace “That’s all xaka 

iya tafiya, idan ya so sai in samar mata lesson teacher na boko kawai” Mikewa Shuraim yyi bai ce komai ba ya fice daga parlon ya kulle kofar, fuzar 

da iska yyi bayan ya fita ya juya yana kallon kofar da idanuwansa da suka sauya kala. Mumy ce xaune dakinta tayi tagumi, da ka ganta kasan tana 

cikin tashin hankali, kanwarta Salima ce xaune dakin, tace “Allah kuwa nake gaya maki Yaya, duk wannan tunane tunanen da saka kai a damuwa ba shi 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button