NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 37

*_NO 37_*


………Shiru yaki magana, itama kuma ta kasa koda motsi, wayar dai na ba kunnenta, kusan mintuna biyu sai ya yanke.

    Rumtse idanu Ummu tayi tana mai zubewa a kan gadon daga ita har wayar, ba tare da ta shirya ba siraran hawaye masu ɗumi suka silalo bisa fuskarta.
      Kusan mintu uku da yanke wayar taji shigowar saƙo, biris tayi da wayar ta ci gaba da hawayenta, ahaka barci ya kwasheta saboda matukar gajiyar da damuwa dake tattare da ita.
    Koda Bily tazo ta kwanta ma tayi barci, bargo kawai ta gyara mata itama ta kwanta, dan garin akwai sanyi, ballema su da ruwa da doka.
     
         Da asubahi bayan sun idar da salla wayar ta ɗauka saboda zuciyarta da keta ingiza ta, saƙonsa ta buɗe.
        *_“Ba zaki kaɗai ke amsa suna sarki ba a dokar daji, mata sune manyan sarakan duniya, baku da ƙarfi, amma kuke ƙarama mai ƙarfi ƙarfinsa._*
          _Naki UMA_

   Siririn tsaki Ummukulsoom taja, wanda har bily ta juyo ta kalleta.
     “Kekuma lafiya?”.
“Ba komai”. Ummu ta faɗa tana tashi ta fita zuwa kicin ɗora breakfast kamar yanda ta safa kowacce safiya kafin tai shirin makaranta, sai dai idan taga zata makarane.
    Wayarta Bily ta ɗauka, tana cire security ɗin taci karo da saƙon A-waheed, karantawa tayi tana taɓe baki, ta fito tana fadin, “Ni yau zan kawo ƙarshen wannan wasan yaran naku, banzan mutum kazo sai wasa kake mata da zuciya”.
   Kira ta danna masa, har tai ring ta gama ba’a ɗagaba, ta sake kira, nanma ba’a ɗagaba, kira uku ba’a ɗagaba, cike da haushi ta goge kiran ta maida wayar yanda ta ganta itama ta tashi ta fice tana tunanin ta hanyar da zata haɗu dashi babu Ummukulsoom.
    Kicin taje tana tayata aikin da take na kokarin fere doya.
     “Bestie ƙarfe nawa zaki fita makaranta ne?”.
       Kallonta Ummu tayi sai kuma ta ɗauke kanta, “Yau bani da lecture ko ɗaya”.
        Daɗine ya kama bily, amma sai bata nuna a fili ba suka cigaba da aikin.

★★★
            Wajen 12 na rana Bily tai karyar zataje wankin kai, dan tasan Ummu anan cikin Barrack tafi son zuwa wankin kai, koda ta tambayeta ma sai tace itafa wajen Jenny zataje.
     “ALLAH ya raka taki gona, idan nagama lecture zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu naje wajen Zuhrah na wanke nikam”.
     “Ok” kawai Bily ta fada ta fice.
    Hakan bai damu Ummu ba, dan damuwar da ta dameta daban.
     Kai tsaye makarantar su Ummukulsoom ta nufa, da taimakon wata ƙawar Ummu ɗin Devine Bily taje Office ɗin Abdul-Waheed.
      Bayan tayi knocking ya bata izinin shiga, kansa a duƙe yanata rubuce-ribuce, hakanne yasa Bily bataga fuskarsa ba sosai, ta zauna tana gaisheshi cikin danne haushinta, bai ɗagoba ya amsa mata.
     “Kina da matsalane?”. Yay tambayar yana cigaba da rubutunsa.
     Sai da Bily taja numfashi tare da dankara masa harara sannan tace, “Sister ɗin Ummukulsoom ce ni”.
    Yanzun ma bai ɗagoba, yace, “Wacece haka?”.
     Kallonsa tayi sosai da sosai tana gyara zamanta, “Abdul-Waheed kana nufin bakasan Ummukulsoom da kake turama massege ba”.
     Tsayawa yay da rubutun da yakeyi ya ɗago yana kallonta, “Ba sunana Abdul-Waheed ba, sannan bansan wadda kike magana akaiba”.
      Sosai Bily ta tsaresa da idanu, “Sir dan ALLAH magana mai muhimmanci ce ta kawoni nan”.
       Wani ɗan card ya miƙa mata batare da yace komaiba. Ta amsa ta karanta, *Uswan Mubarak Adam* taga sunansa, kuma hotonsa ne a jiki, ta ɗago ta kuma kallonsa cikin matukar damuwa, “Amma dan ALLAH to kasan ita Ummukulsoom ɗin ne? Dan itama ɗalibace annan”.
       “Gaskiya ban santa ba, danni watannina uku kenan da fara koyarwa anan, amma ita miya faru da itane?”.
      “Babu komai, na gode sosai”.
Kansa ya jinjina mata yana binta da kallo, danshi sam baima fahimceta ba.
        Gaba ɗaya tunanin Bily ya rikice, ko wajen wankin kan batajeba ta wuce gida, a harabar gidan ta iske Ummu zaune tana shan iska.
    Sannu tai mata bily, bily ta amsa tana zama kusa da ita.
         “Bestie dan ALLAH na tambayeki mana?”.
    Kallonta Ummukulsoom tayi alamar tana saurarenta.
      “Abdul-Waheed yana school ɗinku har yanzu?”.
     “Miyasa kikai min wannan tambayar?”.
    “Babu komai, kedai ki amsani”.
     Numfashi Ummukulsoom ta sauke tana girgiza mata kai, ta cigaba da danna wayar tana magana cike da damuwa, “Bilkisu Abdul-Waheed fa sau uku kacal ya taɓa mana lectures ma, sai dai nakan gansa lokaci-lokaci a school ɗin, watanni Uku kuma kenan ya sanarmin zaiyi tafiya”.
    Da sauri bily tace, “menen cikakken sunansa wai nikam?”.
      “Wai bily waɗannan tambayoyin fa?”.
      “Ummukulsoom ki amsani kawai”.
      “Abdul-Waheed Usman Mustafa”.
     Dafe kai Bily tayi, saboda kuma rikicewa da ƙwalwarta ke neman yi, “Ummu nashiga ruɗani”.
    “Ruɗanin mi?”.
“Wanda na tarar a makarantarku yau Uswan Mubarak Adam, shikuma Abdul-Waheed Usaman Mustafa, mai tura miki saƙo a kowanne massege naki yana saka UMA? Baƙya tunanin akwai ruɗani acikin wannan lamarin?”.
     Yanzu kam sosai Ummukulsoom ta maida hankalinta ga bily, ta ajiye wayarta tana kallonta, “Bilkisu warwaremun dan ALLAH, ni kaina ban taɓa damuwa da ma’ar UMA ɗinnan ba sai yau”.
       Murmushin takaici Bily tayi tana sake fuskantar Ummukulsoom, “Fahimtar hakan danai ce yasa aini nafara binciken, sai dai kema nasan karatune ya ɗauke hankalinki, ba wankin kai najeba Ummukulsoom, makarantar ku naje………..”
    Tsaf Bily ta zayyanema Ummu abinda ya faru, har kiran datai ma A-Waheed ɗin bai amsaba da safe.
      Tsaye Ummu ta miƙe ƙirjinta na wani irin kaikawo, tai taku ɗaya biyu sannan ta juyo tana fuskantar Bily, “Bilkisu a tsakaninnan ina ɓoye miki damuwata ne kawai, amma tabbas lamarin Abdul yana cin zuciyata, a yanda yake mu’amulantata zuciyata bataimin adalciba idan har tace zata cigaba da sonshi, sai dai sam nakasa yakicesa a raina duk yanda naso, bai taɓa min abinda ya taɓa zuciyataba irin jiya, Bily ayanzu Buƙatar ganinsa nake ido da ido, sonake ya sanarmin mike ransa? Amma na rasa wace hanya zanbi?”.
      Bily ta mike itama tana dafa kafaɗarta, “Hanya ɗaya ce Ummu.”
    “Wacece bily?”.
“idan har da gaske yake, kisa masa rana yazo gareki”.
     Idanu Ummukulsoom ta tsirama Bily, kalamanta nakai kawo a ranta, itama tun a daren jiya wannan shike mata kaikawo, to tunaninsu yazo ɗaya da Bily kenan, batace ma bily komai ba ta ɗauki wayarta suka koma cikin gida.
    Har dare abin ya kasa barin ranta, kamar yanda ya saba kuwa ɗan halak ɗin sai ga massege nashi.
     Yau ko karantawa Ummu bataiba ta tahau typing massege ta tura masa nata saƙon.
        _Next week insha ALLAHU zan bayyana mijin aurena ga mahaifina tamkar yanda ya buƙata, dan haka kabar wahalar da kanka wajen takura rayuwata da saƙƙonni._

    Iya abinda ta rubuta kenan ta tura masa tare da kashe wayar gaba ɗaya.
      Bily bata tambayeta mita turaba, ita kuma bata sanar mataba. 


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

             Kwanan baba uku a asibitin jikinsa yay sauƙi, dama Basiru jinsa yake tamkar akan ƙaya, bayan an sallamesu sun koma gidane Inna kebama Basiru labarin tutsen ciwon baba akan sane, dan kullum suna a cikin damuwa da rashin ganinsa, su summa zata koya ɓatane.
     Haƙuri yayta basu kamar gaske, tareda shaida musu wasu ayyukane suka riƙesa a can.
     Baba dake masa kallon tsaf yana daga kwance yace, “Basiru ka canja wannan rayuwar taka kafin lokaci ya ƙure maka, inaji a jikina akwai abinda kake ɓoye mana, ina tsoratar maka yau da gobe basiru, dukfa wanda ya hau motar ƙwaɗayi zata saukesa ne a tashar wulaƙanci, yanzu yadace ace mace ta jaka wata uwa duniya tsawon shekaru biyar? Sannan ita daya dace ta biyoka gidanka amma kaine ka bita, bata taɓa sanin hanyar tushenka ba a matsayinta na matarka ta aure” Baba yay shiru hana haɗiye wani nannauyan abu daya tsaya masa a ƙirji, idonsa ya kuma kaɗawa yay jazur, yaci gaba da faɗin, “Basiru babu rayuwar dakeda inganci ga bawa irin ka tsaya matsayinka, dukkan wanda zai hangi na sama dashi a rayuwa to katabbata yana tanadama kansane ranar kuka, idan har kana tafiya akan ƙafafunka karka kalli wanda yake a mota, kalli wanda yake tafiya a keken guragu bashida ƙafafun shi, kakuma saka a ranka badan ALLAH ya ƙasƙantar da gurgu bane ya hanashi ƙafa, badan ka fisa bane yabaka ƙafa, badan mai mota ya fiku bane ya bashi abin hawa, zata iya yuwuwa ma wannan gurgun duk ya fiku, ALLAH ya ganar damu gaskiya baki ɗaya”.
     Da amin suka amsa shida inna da talatuwa da itama tazo, kamar gaske Basiru ya ɗauka, dan saida ya ƙara kwanaki uku a ɗilau sannan ya koma katsina..    
       A yanda ya samu tarba daga Meenal kawai sai jikinsa yay sanyi, yasan fushi take dashi, maimakon ya nuna mata ɓacin ransa akan ƙin zuwa duba mahaifinsa da tayi, wanda ko a waya bata taɓa tambayar yaya jikinsa ba, dukda Ya sanar mata yazo ya iske baida lafiya ne, amma saishine yashiga bata haƙuri da lallashinta.
     Da ƙyar ta sakko suka daidaita.

     Kwana biyu da dawowarsa aka shiga hidimar bikin yayanta, sam meenal ta hana basiru sakewa, idan har bata tare dashi to bai isa ya fitaba shi kaɗai, tun abin na bashi dariya da nishaɗi harya fara sosa ransa, amma ko a fuska ya gaza nuna mata, sai cin zuciyarsa yakeyi.
      Yau dai ALLAH ya bashi sa’a ta manta bata kulle ƙofar baya ba ta kicin, dan haka take masa dan kar ya fita, (mijin hajiya kenan????????), duk ya duba baiga keys ɗin motocin taba, ta kwashe ta ɓoye, yaji haushi sosai, harma zuciyarsa ta fara tunanin shima yakamata ya mallaki motar kansa tunda sun dawo 9ja, ƴan kuɗin dake Accaunt ɗinsa kuma bazasu ishesa komaiba, dama waɗanda ya tattarane na su Suhailat da Lubna, aurensa da Meenal kuma ya fahimci kuɗaɗen ba komai bane akan ita abindama take dashi, saiya tattaresu ya sa a banki, sai dai ita kuma Meenal sam tasha banban dasu Suhailat, dan bata masa ɓarnar kuɗi, komai nata kaffa-kaffa take da kayanta, shiyyasa har zuwa yanzu bazaice ga wani ƙwaƙwƙwaran abu daya cizga daga jikinta ba kona mahaifinta.
       Tunda ya fito ya zauna ƙofar gidan Zulfah dake cikin mota take kallonsa, dama tunda aka fara bikinnan take bibiyarsa shida Meenal ba tare da sun saniba, ba kai tsaye take son zuwa garesa ba.
        Kallon Abu da sukazo tare tayi, “broth inaga plan B zamuyi amfani dashi tunda plan A babu ƙofa, dan haka aikinka zai fara fa”
        “Karki samu damuwa muje zuwa kawai”.
    Basiru ta nuna masa, yay murmushi tareda ficewa, murfin ya maida ya rufe mata ya nufi Basiru.
     
       Kan Baseer sunkuye yana danna waya, kallo ɗaya zakai masa ka fahimci akwai abinda ke damunsa, Abu yay masa sallama.
     Ɗago ido yay ya kallesa cike da isa,  amma ganin Abu shiɗinma a haɗe dagani ɗan manyane sai Basiru ya ɗan saki fuska suka gaisa, duk da dai yasan anguwace ta manya da wahala asamu mai ƙaramin ƙarfi dama.
      Ba tare da Abu ya jashi da wata magana ba sukai sallama ya wuce.
    Da kallo Basiru ya bisa harya koma wajen Zulfa dake mota ya buɗe ya shiga suka bar wajen suna dariya.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

              Tsawon kwanaki Uku da tura saƙonnan Ummukulsoom taƙi buɗe  wayarta, gashi Abba yazo da kansa yakuma jaddada musu maganar aure, yauma ya wuce Chaina daga nan lagos.
      A gefe dai Yaya zaid ya dameta da kira ta wayar Bily, tasan bai wuce maganar So ba, ita kuma sam taƙi aminta suyi wannan maganar dashi, daya fara take yanke kiran.
     Shi sam baisan damuwa yake ƙara mata ba akan wadda take a ciki, Muhseen ɗin Bily harsun aje magana akan tura iyayensa……
          Sallamar maman Ahmad ta katse tunaninta, ta janye mata tagumin data rabga tana faɗin, “Ummukulsoom kinada baƙo”.
     “Baƙo kuma aunty Hafsat?”.
     “Eh”.
“To nikuwa banyi da kowa zaizo ba, dan Umar ma yana gombe”.
      Ƴar guntuwar takardar dake hannun maman Ahmad ta miƙa mata, jiki a sanyaye ta amsa, sai dai ganin abinda ke rubuce a jikine ya sata zabura da mamaki.
     *_“Abdul-Waheed!”_*
Haka ma ɗan aiken ya faɗa, gashi can Bily ta buɗe musu falon baƙi, saiki tashi ki shirya.
    Kasa koda motsi Ummukulsoom tayi, to ita daɗi za ta ce taji da zuwan nasa kokuwa haushi?.
   Bata da mai bata amsa, dan haka ta miƙe tamkar wata munafuka, dama bata daɗe dayin wanka ba, dan haka ta canja kayanta zuwa doguwar riga ta atanfa, batai kwalliya ba sam, sai turare da ta ɗan fesa, a ganinta bata buƙatar fentin komai a fuska dan zataje wajensa, dan tagama yanke shawarar zaɓar Umar matsayin mijin aurenta..    

   A falo maman Ahmad ta bata madaidaicin tiren da aka ɗora ruwa da juice sai kofi da dambun nama.
     “Aunty ni dama kin barsa kawai”.
    “Bazai yuwuba ai Ummukulsoom, yau ya fara zuwa, ya cancanci karramawa daga garemu.
     Batace komaiba ta amsa, haka kawai takejin ƙirjinta ya mata nauyi, ga wani rawa da zuciyarta keyi, ta rasa dalili, sai kace yaune zata fara sanin wanene Abdul-Waheed ɗin.
      Bataga bily ba harta fito, dan haka tai tunanin ko tana wajensa, da ƙwarin gwiwar hakan ta ƙarasa ƙofar falon, tai sallama can ƙasan maƙoshi.
    Sam ba’a amsa mataba, inma an amsa bataji ba, dan haka ta harari labulen tana ɗan gyara gyalenta sannan ta shiga da wata sabuwar sallamar.
         Akan bayansa daya juya ta sauke idanunta, Suit ne jikinsa kalar jaa, baisa ta saman ba, ta cikice kawai baƙa sai ƴar karama ta saman, ta ajiye tiren hannunta a hankali, yayinda zuciyarta keta wantsale-wantsale.
    Yanda yanajinta bai juyoba bai kuma yi magana ba haka itama ta samu waje ta zauna ta sharesa, itafa bazata ɗauki wannan isar tashiba sam.
    Kusan mintuna biyu suna a haka, kafin ya juyo a hankali yana takowa tamkar mai gudun aji motsinsa, Ummukulsoom na jinsa amma ta dake taƙi koda motsi itama balle ta saci kallonsa.
      Gabanta yazo ya tsaya cikeda izza, ya harde hannayensa ya zuba mata manyan idanunsa kawai, ganin bazata kallesa bane yasashi saka hannu ya zare wayarta da take dannawa.
    Gabanta yaɗan fadi tabi hannunsa da kallo, sai kuma ta basar taƙi kallon nasa balle ta tanka. Minti biyu ne ya sake shuɗewa, haushi ya fara tasiri a zuciyar Ummukulsoom, dan haka ta miƙe da nufin tafiyarta dan wannan Ummu ɗin bata da bace da maza ke garawa, ta yanzu itace zata gara mazan, inhar bazaiyi maganaba to ita kuma bazatayiba a matsayinta na mace, ballema tamasa sallamar da addini ya wajabta mata amma bataji ya amsaba.
      Taku ɗaya biyu tayi taji an damƙo hannunta.
    Cak ta tsaya tare da juyowa a fusace, “Sakemin hannu!”.
     Shiru bai tanka ba, bai kuma saketa ba.
    A kausashe tace, “Abdul-Waheed sakemin hannu, sannan daga wannan ranar karka sake zuwa inda nake, dama ban taɓa sonka ba, a yanzun ma nazo na tabbatar maka na fidda mijin aurene, karka sake turamin shirmen saƙonka danni ba doll ɗin wasan, yara bace kaji, inada wanda nake S……”
    Fisgotan da yayne ya hanata ƙarasa kalmar SO din da tai niyyar fada, ya turata ta manne da bango, ya kuma dinkareta yanda bazata taɓa kufce masa ba.
     “Duk abinda naso nawane ni kaɗai yarinya, babu wani mahaluki daya isa nai raba daidai dashi koda wajen farautarsa ne..”
    Sosai Ummu ta rikice, ta kalla fuskarsa amma sam ba shi bane, Abdul-Waheed ne dai malamin makarantarsu, to miyasa muryar kuma?….
       Sake kallon hannunsa tayi dan shima zai iya zame mata shaida, sai dai kuma dogon hannun rigar ya rufe, cikin zafin nama tasa dukkan hannayenta ta turashi baya da dukkan ƙarfinta, dan kusancinsu yayi yawa, tsigar jikinta sai tashi yake, ko motsi baiyiba, saima hannayen nata daya riƙe duka ya maidasu baya a matse da hannunsa ɗaya.
    Baki ta buɗe zatai magana ya ɗora yatsansa a baki yace, “Shiiii????”. Alamar tayi shiru.
     Ɓam kuwa ta maida bakin ta rufe tana hararsa, shikuma yasa ɗayan hannunsa  akan fuskarsa ya fara zame fuskan saman daya ɗora akan tasa ta ainahi……….✍????


⛹????‍♀️⛹????‍♀️⛹????‍♀️⛹????‍♀️⛹????‍♀️


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

????????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863


*_ƴan Niger kuma_*

_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*

*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*

 _TA NUMBER;_
 *+22795166177*   


Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button