BAKAR INUWA 48

Chapter 48
48
………Duk yanda taso zamewa basa abincin fir yaƙi. Dolenta ta bashi kamar yanda ya buƙata, kunya kamar ta tsaga ƙasa ta nutse a ciki. Shiko ko’a kwalar
rigarsa. Sai ma idan tayo ƙatuwar lauma ya harareta wai tafi ƙarfin bakinsa. Amma in namane dataso ragewa zai riƙe hanun da faɗin ‘Ban san mugunta Ustazah’.
A haka dai yaci ya ƙoshi itama ya tsareta sai taci. Fuska ta marairaice tamkar zatai kuka amma yace saifa taci babu ɗaga ƙafa. Dole ta ɗan tsakura dan a
takure take sosai. Bayan ta kammala ta tattare kwanikan ta fita da su. Numfashi ya sauke a hankali da barin aikin da yake a lap-top ya kwantar da kansa
jikin kukerar yana lumshe ido da furzar da numfashi. Sai kuma ya kai hannu a wuyansa dan har yanzu akwai zazzaɓi jikinsa dauriyace kawai. ‘Oh Ramadhan Taura
ka zama ɗan cali-cali kuma?’. Sai kuma ya sake sakin murmushi da girgiza kansa kaɗan. Shi kansa baya sanin sanda yake biyema Raudha. Abinda ya sani kawai
bai son ganinta cikin damuwa kamar baya. Sannan addu’arta a koda yaushe na bashi nutsuwa. Yayinda idan tana a yanayin tsoro da kunya take hana fitinarsa
zama lafiya ya dingajin kamar kawai ya…… “Ya ALLAH” ya ambata da kai hannu cikin sumar kansa. Sai kuma ya tashi zaune sosai ya cigaba da sarrafa system
ɗin cike da ƙoƙarin son ture abubuwan dake neman fin ƙarfin jarumtarsa……
___★★_
Alhmdllhi zamuce abubuwa sun fara daidaito tsakanin Ramadhan da Raudha, ta saki jiki dashi ba laifi suyi ɗan wasa da dariya. Idan kuma taga ya haɗe
fuska ta kama kanta ta nutsu. kwana ɗakinsa dai bata sake yarda tayiba tun randa yay zazzaɓi. Amma yanzu tana ƙoƙarin tashi a kowace bayan sallar asuba ta
haɗa masa breakfast da kanta. hakama abincin dare kafin ya shigo takai komai bedroom ɗinsa ta ajiye. Wataran ya leƙata da matsa mata tazo ta bashi abinci.
wataran ya shareta yaci abinsa sai da safe idan tazo gyaran ɗaki ta tattare.
A washe gari Ramadhan da Bappi suka gana, ganawar data zama ta farko a zahiri da har ƴan jarida suka fitar. Sai dai babu wanda yasan mi suka tattauna a
zaman nasu sai ni (Bilyn Abdull cctv footage ɗin ku????????). Sosai kansu ya tushe da mamakin ganin rubutun Raudha dai-dai da takardar da aka turama Bappi ana
jibi ɗaurin aurensa da Raudhan. An musu nuni ne da karsu yarda Ramadhan ɗin ya tare a gidan gwamnati har sai an cire ac ɗin dake a bedrooms nashi da
falukansa saboda akwai poison a ciki. Ranar sun shiga tashin hankali musamman Anne datace Ramadhan bazai tare government house a kashe mata shi ba. Shi da
Bappi sukaita lallashinta da mata nasiha harta nutsu, inda basuyi ƙasa a gwiwa ba randa Ramadhan ya shiga gidan gwamnati kwana biyu da aurensa da Raudha
suka canja duk ac ɗin dake sashen harma dana office ɗinsa. Hakama sai da suka bincike lungu da saƙo na ɗakin barci da falukansa na sirri gudun ko an saka
camaras a ɓoye. amma Alhmdllhi babu alamar hakan sai iya ta inda ya dace kawai da dole a samu a kowane gidan gwamnati saboda tsaro. Dan wani yaron Aunty
Zuhrah ne yay aikin. Sun sake tsintar kansu a tashin hankali lokacin da suka samu poisons a cikin ac’s ɗin. Ranar har hawaye Bappi yayi. Daga haka kuma ya
ɗarsama kansa zargin akwai boyayyen al’amari. Sai dai kai tsaye bai fito ya ambaci sunan kowa ba. Babban fatansu kawai susan wanene wannan mai turo saƙo.
Hakan yasa ganin wannan hand writing da yay dai-dai dana Raudha yay matuƙar ɗaure kansu.
“Wannan ya sake tabbatar min yarinyar nan Alheri ce kuma akwai dalilin zuwanta garemu”. Bappi ya faɗa lokacin da suke ganawa da Ramadhan a office.
Cikin sauke numfashi Ramadhan yace, “Tabbas akwai abinda bamu saniba kuma ita take ɓoye mana. Abin ɗaure kan anan kawai shine a gaba ɗaya tarihin
yarinyar dana bibiya babu wani alamun alaƙarta da wani sai danginta ko anan cikin Bingo. Sai dai sister ɗin mom nata tanada alaƙa da matar forma president,
a yanzu kuma matace ga Alhaji Yaro glass Vice ɗina, dama kuma sun taɓa zaman aure ta fita. Bappi inhar hasashena yana kan dai-dai akwai boyayyar manufa
tsakaninka da abokan nan naka gaskiya”.
Murmushi Bappi yayi yana ɗan jinjina kai. “Komai zai iya faruwa musamman idan akai la’akari da abubuwa masu yawa. Sai dai bana so zargin sunan kowa anan
har sai muntabbar. Shawarata gareka anan lkawai ka cigaba da jan yarinyarnan Ameenatu a jiki, zaka iya jin fiye da abinda muke buƙata daga gareta. Amma
tabbas ka shaida naji ƙarin ƙaunarta a raina da kimarta fiye da zaton mai zato. Dan zuciyata bata gayamin an haɗa kai da itane dan a cutar damu”.
A hankali Ramadhan ya sauke numfashi wani abu mai sanyi na sauka masa a cikin zuciya. Jiyake kamarma ya buɗe ido ya ganta gabansa. Jin yau ɗin yake daban
da kullum a rayuwarsa. Sai dai me, yana zuwa gidan ya iske ɓacin ran su Lubnah da har takaisa ga marin Lubnah ɗin. A kuma daren yasa driver maidata gida.
Sai dai abun ƙarin takaici washe gari Maah tasa aka maidota.
Wannan haushin ya sakashi tunda ya fita gida da safe bai dawoba sai dare. Washe gari kuma tafiya ta taso masa zuwa ƙasar faransa babu wani walwala
tattare da shi sukai sallama da Raudha da ayanzu ta sake nutsuwa akan makaranta dan harta fara jin daɗin lectures din saboda taimakon da su Basma ke bata.
Ta ɗan shiga damuwa da canjawar tashi, sai dai daga baya ta watsar da komai dan indai dan abinda su Lubnah sukai matane ita ya wuce a gareta basa ma
gabanta. Fatanta dai ALLAH ya bata kariya daga cutar da waninsu.
A washe garin daya wuce ta tashi da ciwon mara. Tasha azaba sauƙintama yasa Bilkisu dawowa gidan saboda ya fahimci suna ɗasawa da Raudha ɗin. Sai dai
sunsha gargaɗi kamar babu gobe akan abubuwa da yawa. Hakama su Muneera sunsha nasu, dama tun marin da Lubnah tasha suka koma shiru-shiru a gidan dan sun san
hali. Yanzu ko daya tafi sun ɗau alwashi kala-kala akan Raudha sai akai rashin sa’a Bilkisu ta dawo kusa da ita.
Bilkisu ce ta sanar masa halin da Raudha ke ciki ta hanyar massege. Hankalinsa ya tashi lokacin daya lura ta text ɗin. Sai kuma a lokacin ya tuna da
zancen Dr Hauwa’u a wancan lokacin. Bai samu magana da Bilkisu ba sai dare bayan ya samu nutsuwa. Ta kwantar masa da hankali akan da sauƙi, dan Anne ta kira
shine ta turo musu Maman Jabeer (Dr Hauwa) tazo ta dubata. Ta tabbatar masa tayi faɗa sosai akan ƙin zuwan Raudha ɗin bayan tun wancan karon tace taje bayan
ta warke.
Yaji babu daɗi sosai, dan kuwa akwai sakacinsa tunda shine bai nuna maida hankali akai ba matsayinsa na wadda take a ƙarƙashinsa. Bai ce a haɗashi da
Raudha ɗin ba, sai dai ya tabbatar ma Bilkisu tayi ƙoƙari idan Raudha ta samu lafiya suje asibitin Maman Jabeer ɗin.
Haka kuwa akai, bayan kwana biyu ta koma ragas kamar ba’ita ba. Dan haka sukaje asibitin da dare gudun idon mutane. Sai dai tana tare da dogaranta duk
da hakan.
Sosai Dr Hauwa tai mata gwaje-gwaje na musamman yanda ya kamata. Cikin amincin ALLAH kuma ta gano matsalolin dake tare da Raudha ɗin harda imfection.