BAKAR INUWA 53
Episode 53*
……….JIHAR ƊILLO (HUTAWA)
A Hutawa kam kowa yaga M. Ɗan-azumi yanzu sai yay matuƙar mamaki. Dan kamar yanda ya ƙudiri ƙara sabon aure ya auro dalleliyar budurwa sabuwa dal
a kwali. Kai daka ganta kasan ƴan kuɗin ta biyo. Baƙaramin tashin hankali Larai ta shiga ba, dan saika ɗauka ma wani sabon haukane ya hau kanta. Data nema
birkice masa sai ya aikata gida taje ta huta. Roƙo iya roƙo ita da danginta amma ya birkice musu ƙememe dama fitinarta ta isheshi, ga baƙin cikin rabasa da
masoyiyarsa Asabe da har yanzu ko ɗigon sonta baibar zuciyarsa ba. Ganin haka Baba Nafi ta ƙara kama kanta da mutuncinta a gidan, dan tun dawowar Inna da
ƙaninsa da matarsa dama gidan ya sake zama sai a hankali. Gadai jin daɗi yanzu a cikinsa amma kowa zaman haƙuri yake da ɗan uwansa saboda fitinar sirikarsu
dabance a rayuwa, shi kuma M. Dauda na biye mata dan duk haukarsa yana ƙaunar Innarsa.
Tun auren Raudha alaƙar zuminci mai ƙarfi ke tsakaninsa da hakimi, hakama jama’ar gari sosai suke respecting nashi kowa burinsa ya zama abokin
mu’amularsa (kaiko sirikin shugaban ƙasa fa ba wasa ba????). Da wannan damar M. Dauda kan samu na hura hanci sai ya zaɓi wanda yaso ayi zumincin, shi da M.
Gambo ne dai ana nan tif da taya, sai dai baisan M. Gambo nata masa zagon ƙasan ƙoƙarin kiran Asabe a wayaba kullum, wani lokacin harda mata ɗan text na
soyayya dan ƴar sakandire ɗin nan dai shi da M. Dauda sunyita. Ita Asabe har zuwa yanzu batasan wanene ba. Dan tun tana sharesa da masa masifa idan ya
kirata harta ɗan fara kulashi.
Hakimi daya fahimci rawar kan M. Dauda bata risinaba saima giyar kuɗi dake neman ɗorasa a wani layin bayan wanda yake kai yasa shi ƙara jansa a jiki
yana masa nasiha, ya kuma bashi sarautar data tilastashi kullum zuwa gidan Hakimi ayi fadanci dashi. Koda yake mugun ɗagawa da faɗi yake da sarautar, inma
ka kira sunansa baka haɗa da sauratarba to kuwa kaji barbaɗin jaraba daga sama har ƙar zai zugeka yana hura hanci da kiran shi ya wuce raini ai. Surikin
shugaban mai ƙasar yake baki ɗaya, Baba sama baba ƙasa yake kiransa kuma saiya risina yake gaisheshi koda a wayane balle wani ƙaton ƙawai da talauci yayma
katutu. (????????ALLAH ya bar mana Man Dauda).
Ya sayi ƴar kwariɓar motarsa ana yanga da ita kwana biyu ta birkice, cike da masifa ya maidawa bakaniken daya saida masa yace wlhy koya dire masa
kuɗinsa kokuma yasa azo daga Bingo a cukuykuyesa yasan dai uban matar shugaban ƙasa yake. Da farko makanike ya ɗau abin wasa, dan mahaukacima suka maida M.
Dauda shi da yaransa. Saiko gashi ko mintuna ashirin baiyi da barin wajenba motar ƴan sanda har uku sunzo sun yayesu gaba ɗaya har yaran nashi. Dan kuwa M.
Dauda yana zuwa police station d.p.o da ayanzu ya gama haddacesa shi da yaransa koda ɗunbin alkairin da suka samu a ranar auren ƴarsa da shugaban ƙasa sukai
masa tarbar mutunci. Harda matsar kwallan munahinci wajen faɗa musu abinda akai masa a gareji. Rai ɓace d.p.o ya bama yaransa umarnin zuwa a kwasosu yana
bama M. Dauda haƙuri.
“Baba ai kun wuce ko kallon banza yanzu a ƙasarnan, kunefa iyayen masu ƙasar. Gamu nan tunda ɗanku ya hau mulki albashinmu ma ninkashi akai tsabar
adalci na wannan shugaba. Ai mu babu abinda muke sai fatan alkairi a garesa, mun kuma tabbatar lallai matasa masu jini a farce ƙasar NAYA ke buƙata irinsa..
ALLAH ya ƙara masa zaman lafiya da matarsa nan da watanni asake zuwa taron suna NAYA muci musha muyi warkan. Dan muna alfahari first lady tamuce wlhy”.
Daɗi kamar zai kar m. Dauda, ya dinga washe haƙwara yana sake baje babbar rigarsa dan ɗinkunan alfarma da Alhaji Hameed Taura yay masa na biki har kala
goma sune suka zama na faɗi yanzu a gari. Lokacin da aka shigo dasu Gali a ɗage M. Dauda yake kallonsu da watsa hannaye gaba. “A rufeminsu har sai na manta
da wanzuwarsu sannan a tunamin”.
Cikin roƙo da magiya kanikawan nan ke roƙon Alhaji Dauda (dan tunifa dama gargaɗi yake abar kiransa M. Dauda????????). Amma ko kallonsu baiyiba. Cikin takun
ƙasaita ya buga babbar rigarsa aka fice dan d.p.o ya bada motarsa a maidashi gida.
Kwanakin kanikawan nan huɗu a ofishin ƴan sanda sannan ya bari aka sakesu da sharaɗin maido masa kuɗaɗensa nanda sati guda. Hakan kuwa akai sai gasu
da kuɗaɗensa cif sun kawo, ya dinga antaya musu harara yana sake baje riga da hura hanci. Bayan ya koma gida ne ya nema kuɗin ya rasa da kwana biyu shine ya
yanke jiki ya faɗi har saida aka kaisa asibiti. Wannan ne dalilin zuwa su Fatisa dubashi har suka sanarma Raudha, to ayanzu haka dai ya haɗa duk yaran gidan
nasa da matan ya tabbatar musu idan kuɗinsa basu dawoba nera dubu ɗari bakwai wlhy suma cell zaisa a zubasu har sai sun magantu.
(????????To bara muga ta inda kuɗin Alhaji Malam Dauda surikin shugaban ƙasar NAYA zasu fito).
BINGO CITY (TAURA HOUSE
Barci sukasha sosai kamar yanda Ramadhan yaso. Ga Anne daga falo na musu gadi dan koda su Basma suka taho wai anan zasuyi breakfast korasu tai
duk da tasan da wahala hayaniyarsu takai ga sashen Ramadhan ɗin. Dama tunda ya shiga ya gaisheta bayan sallar asuba yace kar ai musu breakfast da wuri. Dan
haka ba’a ɗora ɗinba kuwa sai kusan sha ɗaya na safe. Zuwa sha biyu an kammala komai an kawo falon part ɗinsa an shirya bayan an gyarashi yanata ƙamshi duk
da bawani datti yayi ba.
A yanzu ɗinma kusan tare suka farka sai dai motsintane ya tadashi. Tai ƙoƙarin janye jikinta ya hana hakan. Cikin yanayin kasalar barci ya mika
hannu ga side drawer ya ɗakko agogonsa yaɗan kalla time cikin lumshe idanu da buɗewa. Har sha biyu ta gota. Agogon ya ajiye da kai lips nashi a goshin
Raudha da taƙi buɗe ido ya sumbata. Kafin ya saketa ya sauka baki ɗaya batare da yayi magana ba.
Bata iya motsawaba sai da taji ya rufo toilet ɗin. Ta miƙe da ƙyar itama dan barcine da bata sabayi ba ace tun sallar asuba har kusan 1. Gadon ta shiga
gyarawa a ɗan gurguje, ta maida net ɗin yanda ta gansa, sosai yake birgeta dan ya sake kawata gadon da ɗakinma baki ɗaya. Har falo ta fito neman kayan
shara, cikin sa’a ta samu a cikin kitchen bayan ta karema falon da kitchen ɗin kallo. komai akwai na buƙatar ɗiya mace har tana mamakin sai kace mai mata.
Shara ta gama tana tsaka da mopping ya fito. Bata yarda ta kallesa ba, sai shine dake binta da kallo ya nufi mirror yana faɗin, “Waya saki wannan
aikin?”.
Amsa ta bashi batare data yarda ta kalla inda yakenba dai.
“Ba kowa”.
Komai bai sake cewaba harta kammala ta fita da kayan, taɗan jima kafin ta dawo da fatan ALLAH yasa ya saka kaya. Sai dai addu’ar tata bataci ba dan har
lokacin ɗaure yake da towel tsaye a gaban Wadrobe da alama kaya yake nema. Kaita kauda cikin sauri ta faɗa toilet.
Baki yaɗan taɓe dan duk yana kallonta ta gefen ido. Ta jima bata fitoba, har sai da ta leƙo taga baya ɗakin. Da sauri-saurin tai shirinta cikin atanfa