NOVELSUncategorized

KWARATA 66

???? —— 66

      Jin nayi shiru yasa yace ki sake cewa wani abu mana marar kunya da kika raina mutane , ke “yar mitsitsiya dake nan har kin iya masifa da ƙure rai wanda idan nayi zuciya ina iya haɗiye ki ba tare da nasan naci komai a bakina ba wawiya “Yar matan Yazeed dake,


      Tunda na taho daga inda naje wallahi bana tunanin kowa sai ke , na taho cikin farin ciki ina kyarma inzo in ganki amma kika lalata min lissafi , maimakon ki tareni da farin ciki sai kika tareni da hawaye.

    Cikin kuka nace ba kawai dai kanajin zalinci kazo ka kamani kana ta dukana babu abinda nayi maka tsabar ƙwarewa da zalinci ai dama ba so na kake ba kullum baka da burin daya wuce kaga kana zalinci na.

     Haba An mata ke harni zaki faɗa ma bana sanki ? Idan har bana sanki ke har kin isa ki kalli tsabar idona ki zageni ? Na baki tayin soyayya na maimakon kalami mai daɗi sai mummunan sakamako , kicemin mahaukaci kuma ƙarshen ki wulaƙanta ni ki faɗa a gaban yara dake ganin girma na , duk a bana sanki ne kika ɗaga hannu ki zabgagamin mari na gyaleki ? Na rantse da girman Allah da bake ce kika mareni ba idan basai nabi ta kan ko waye da mota na wuce ba Allah ya tsinemin albarka , tou wai taya ma mutum zai kalleni bare kuma har yayi tunanin faɗar mummuna akaina ? Ko bakya so na ko albarkacin darajar wannan bazanci ba ? Yayi maganar yana taɓo gemunshi yaci gaba da cewa ba’a zagin mutumin daya ajiye shi amma ke sam baki da lissafi.

      Shashshekar kuka nayi ina cewa kana so na kake dukana ? Har so biyu ka dokeni , kaji min ciwo a gefen fuskata ka farfasa min jikina wannan duk soyayya ne ? Ai na faɗa miki kema so kike ki zama kamar doki ko an hauki sai an dokeki har so nawa na faɗa cewa bana san kina fita ai ke sai kin fita ki nunamin kunne ƙashi gareki ai dai yau jikinki zai baki labari…

      Wayyo Allah dama nasan wallahi ba so na kake ba yauma dukan nawa zakiyi ? Duk duniya zuciyata da kwakwalwata ko Dikko basu sani ba sai An mata , haka wayata ma bata san wani Dikko ba itama kanta An mata ta sani amma Dikko ke amfani da ita , ki ɗauki wayata password ina ki rubuta Dikko wallahi zata ce miki a , a amma kina rubuta An mata saita buɗe miki ,

    Banda hoton komai a wayata sai doki amma zuwanki yasa na zama zararre ki duba ki gani babu hotunan kowa a wayata na mace sai naki , duk inda kika shiga a wayata An mata zaki gani amma wallahi yau mai ƙwaceki a hannuna sai Allah addu’a ɗaya zaki dage kiyi shine Allah yasa har in gama dukanki ina cikin hayyaci na…

       A dai² lokacin daya shigo kwanar da zata sadashi da gidanshi tunda ya shigo santar ya kwace da gudu na tashin hankali kamar zai tashi sama motar har wani lilo take ya danne horn , gabana sai faɗuwa yakeyi cikina sai juyawa yakeyi hawaye kuma basu daina zubowa ba , koda muka iso har an buɗe get in hancin motarshi ya saka ya raba get in biyu ya sauke gilashin motar cewa kai Amadu zo nan…

       Da gudu yazo Dikko yace kai buɗe nan baya ka ɗauki wata foodflarks na nan kaje ka samun murfinta , matsawa yayi ya buɗe ya ɗauka yace mai gida ai ba’a siyar da ware² a idan za’a siyar da murfin tou dole da uwar ake siyarwa ba’a rabasu , ta cikin madubi Dikko ya kalleshi yace ni ba abinda ya dameni murfi kawai nake so ka samomin irinshi.

      A tsorace na kalli Dikko murmushi yayi min tare da ɗaga min gira yana min kallon rainin wayau ya taka motar muka shiga cikin gidan da gudu , gidan an ƙara mishi wani irin girma na tashin hankali an maidashi gidan “yan gayu anyi mishi bene hadaɗɗe gidan ya ginu sosai gwanin burgewa amma ba’a gama aikin ba , ko me yasa yake sha’awar sissiye maƙota yayi gini……?

        Malam Amadu yace mai gida wallahi ba’a siyar da murfi , da sauri Dikko ya fita daga cikin motar bayan yayi parking ya koma wurin get , Amadu na ganin Dikko ya fito a hayaƙe ya wuce da sauri yabar gidan yana kallon rigima irinta Dikko ya za’ayi wai ya samo murfin wannan abun ne ? Ko a kasuwa ba’asiyar da ware² to kodai mai gida yana so yaɗan sha iska ne da macen daya zo da ita shi yasa ya korashi ? Saida ya kalli kular ya kallo gidan da Dikko ya rufe get in da kanshi !

       Cikin tsananin ɓacin rai ya dawo da sauri na fito daga cikin motar faɗuwar gabana ya ƙara tsananta yayin da Dikko ya ɗage but ya ɗauko wata irin zureriyar dorina irin wacce ake bugun dokuna da ita yace wuce muje , cikin fargaba nayi gaba Dikko ya biyo bayana ina tafiya ina waiwayenshi , cikin hayani yace ki kalli gabanki ki daina kallo na ya ƙarasa maganar yana zazzaro min duk iya girman idanuwan shi.

     Wata irin kyarma na farayi ta tsoro na shiga cikin palon na samu wuri na rakuɓe kamar asirin mayya ya tonu , shima wuri ya samu ya zauna a gajiye tare da cewa zo nan , ƙin tafiya nayi kamar banji shi ba , bakiji ina miki magana ne ? Basarwa nayi na nuna mishi ƙangara da yarinta , cikin hayani yace idan na sake cewa kizo baki zo ba saina tuɓe miki kayan jikinki zan zaneki ,

     Kamar ina iyayin wani abu nace ai sai kazo ka tuɓemin dama tuɓeni kake so kayi shi yasa kazo dani ko ni zaka nuna ma hauka ? Kai kaɗai ne mahaukaci kowa mahaukaci ne ? Naci gaba da zagin Dikko yace dama nan nake so kizo , ajiye dorinar yayi ya cire belt yazo yaci gaba da zabgamin shi kamar yana dukan “yar shi yana dukana yana cewa zaki sake zagina ne ? Cikin kuka naci gaba da zaginshi ina Allah ya isa mugu munafiki azzalimi ,

     Yanayin fushi ya fara zuwa ki daina zagina….? Ya ƙarasa maganar yana rufe idonshi daya rufe ido komai zai iya faruwa , cikin kuka na matsa daga wurin da sauri nace yi haƙuri don Allah kayi haƙuri ???????? kafin in rufe bakina ya fara zabura cewa saina kashe ki…….

        Cikin ruɗewa na fara gudu zan fita waje amma kafin in fita har Dikko ya ɗauko wata wayar wuta da aka sauke ƙasa ya wurgota ta naɗoni ya fizgo da ƙarfi na faɗi ƙasa ya jawoni na dawo cikin palon , saina kashe ki tunda kin rainani , dorunar ya ɗauka yaci gaba da dukana zaki sake zagina ko bana nan ? Yaya dan Allah kayi haƙuri zaki sake fita idan nace bana san abu zaki sakeyi ko bana nan ? Wallahi na bari ƙarya kikeyi sai kin sake kawai kasheki zanyi inje in wurgaki a ruwa ,

      Malam Amadu kuma ganin Dikko ya rufe gida ya lura kamar baya hayyacinshi sai yanzu ma ya gane Sultana ce bayan yayi dogon nazari , da sauri ya fiddo wayarshi ya fara kiran Ashiru , da farko Ashiru kamar bazai ɗauka ba dan yasan dama Amadu zai ce masa mai gida yana dukan Sultana ne shi kuma yana so Sultana taji yadda Dikko yake yarinyar bata da mutunci kwata² ga raini ga rashin kunya yauko zataci ubanta tunda ta raina mai gida , har wayar ta tsinke bai ɗauka ba Amadu ya sake kira saida ta kusa tsinkewa Ashiru ya ɗauka yace ya akayi ne ?

       Amadu yace mai gida ya rufe gida kuma ya aikeni wai na nemo mishi murfin kula kuma kamar yana yanayin fushi yazo da Sultana , Ashiru yasan komai dan haka yace to ka sani ko soyayya sukeyi ne ? Amadu yace duk dai yanayin fushi da farin ciki irinsu ɗaya a wurinshi bana tunanin soyayya da Allah kuzo , Ashiru yace ai kaima namiji ne ka shiga ka bashi haƙuri dan yacemin yau sai saɓa mata kamannu ai ta raina mutane barta taci ƙaniyarta yana faɗin haka ya tsinke kiran…

     Bayan Ashiru ya ajiye wayar yace kai gaskiya fa za’a iya samun matsala kunsan mai gida matsalarshi da yake duka yana buga mutum da wani abu , itafa ba namiji bace ba duk da bana tunanin zai bata wahala sosai kai ku tashi mu tafi kada rayuwar yarinyar nan ta samu matsala dai , gaba ɗayansu suka fito suka taho goruba cikin motocinsu ,

       Zuwa wannan lokacin ni kuma Dikko tunda ya ɗaga ƙafa zai takamin wuya ya kare in mutu kamar yadda yace na riƙe kafarshi na kalli idonshi cikin kuka nace karka kasheni ina sanka don Allah , murmushi yayi tare da takani da ƙafarshi a hankali yace ƙarya kike , da gaske nake ina sanka wallahi , duƙawa yayi ya ɗagoni daga ƙasa ya rungumeni yace da gaske kina so na An mata ? Cikin kuka na ƙara rungume Dikko kaina kamar zai ɓare saboda ya buga min a bango yayi wasan kura dani ya bani wahala sosai duk jikina ciwo yakeyi kamar jirgin ƙasa yabi takaina ya wuce , kwantawa nayi jikinshi sosai ina kukan wahala.

    A dai² wannan lokacin da aka fara dukan gida ni kuma daga nan ban sake sanin abinda ake ciki ba , cire Sultana ya farayi daga jikinshi amma ya kasa , An mata tsaya inje inga waye , ina Sultana ta tafi batajin Dikko dakel ya ciro wayarshi daga cikin aljihu saboda cakumar da Sultana tayi mishi Ashiru ya gani yana kiranshi , bai ɗauki wayar ba yace An mata sakarni in buɗo gida , tuni Sultana ta daina motsi dakel Dikko ya ɓanɓareta daga jikinshi ya kwantar da ita ƙasa har yanzu hawaye bai daina fita daga idonta ba amma gaba ɗaya ta tsaya ,

       Fita yayi daga cikin palon yazo ya buɗe gidan , Ashiru ya gani tsaye yace ya akayi ne ? Ashiru yace naji shiru ne nace bara inzo inga lafiya ? Lafiya lau Dikko ya bashi ansa , Ashiru yace mai gida to ina Sultana take ne ? Tayi bacci , Ashiru yace bacci ? Umm ya bashi ansa da kanshi , ɗan gyarawa Ashiru yayi yace tou amma ai kayi haƙuri ko ? Na daketa amma kaɗan yayi maganar yana yatsina fuskarshi ,

      Ashiru yace mai gida kuma duk da ka daketa sai tayi bacci ? Murmushi Dikko yayi tare da cewa ko ina cikin yanayin fushi nasan abinda nakeyi naso na bata gwalagwala amma sai tayi sauri tace tana so na , wannan kalmar ya ceceta daga azabata kuje kawai zanzo idan na maida ita gida , Ashiru yace bara dai mu jiraka daga ciki , ba tare da Dikko yayi magana ba ya dawo ciki ya bar musu gidan buɗe ,

      Ɗaukar Sultana yayi ya fito rungume da ita a jikinshi ya kaita mota , idan mutum ya suma a wurin faɗa ko duka ba’a fesa mishi ruwa , idan mutum ya suma a ruwa ba’a zuba mishi ruwa saidai a buɗe bakinshi a busa mishi lumfashi idan kuma yasha ruwa sosai sai ake danna ƙirjinshi a hankali , idan kuma mutum ya suma a faɗa ko ana dukanshi firfita ake mishi , idan mutum ya suma haka nan babu gaira babu dalili shine ake yayyafa mishi ruwa.

     A mota Dikko ya riƙe ruwa a bakinshi ya fesawa Sultana tunda ita dai ba lokacin daya doketa ta suma ba tana kwance a jikinshi ta ɗauke , ajiyar zuciya ta sauke ta sauke a wahalce , rufe motar yayi ya zagaya ya shigo ya rufe , ba tare da yayi magana ba ya tada motar muka fita a gidan.

      A waje yaga Amadu tsaye da kular daya bashi ya samo mishi murfinta , yana ganin fitowar Dikko yayo wurin cewa mai gida ba’a samo ba , ba tare da Dikko ya kalleshi ba yace maidata inda ka ɗaukota , buɗe bayan motar yayi ya ajiye ya rufe mukayi gaba su Ashiru suka rufo mana baya ,

        Har muka isa gida babu wanda yayi ma wani magana , fita nayi daga cikin motar dakel banyi magana ba , har zan wuce yace An mata zo , dawowa nayi banyi magana ba na tsaya , baki gode ba ? Nayi shiru , shigo , komawa nayi cikin motar a wahalce na zauna , rashin godiya ba ɗabi’a mai kyau bane dana kawo ki gida ai sai kicemin kin gode waike baki iya irin ɗan makircin nan na mata ba ? Gaskiya aikin yawa zaimin in koya miki hankali kuma in koya miki zaman takewa na rayuwa ya zama dole ki koyi kissar zama dani danni bazanyi haƙuri dake ba ke ya zamar miki dole kiyi haƙuri tunda nine samanki fita ki ban wuri ,

      Ƙoƙarin fita na farayi yace kuma tafiyar zakiyi da gaske ? Komawa nayi na zauna , kwantar da murya yayi sosai yace kin yafemin ? Da kaina na bashi ansa Eh , zaki aureni aiko ? Shiru nayi ina nazari , yaci gaba da cewa insha Allah ƙarshe watan nan zamuyi aure kuma idan munyi aure bazan miki ko kallon banza saidai ki anshi hukuncin ki a gado , wannan dukan insha Allah shine na ƙarshe bazan sake ba abinda yasa ma na dakeki nayi rantsuwa so adadin da bazan iya gane ko so nawa na rantse ba, ina sanki har abadan duniya bazan taɓa goge ki a zuciyata ba , kuma ai kema kina so na ko ? Yanzu ma da kaina na bashi ansa Eh , ngode zanzo da safe insha Allah kije , fita nayi ina masa godiya kamar yadda yace na wuce ,

Cike da tausayi Dikko yabi Sultana da kallo a bayyane yace duk wannan ɗa’ar wallahi ta banza ce bazata bar abinda take ba , motarshi yaja ya fita daga cikin gidan yana mai ƙarajin soyayyar An mata a zuciyarshi.

      Tsaye nayi a gaban madubi bayan na fito daga wanka ina kallon yadda Dikko ya farfasamin jiki sahun bulala babu inda bai fito ba , a fuskata kuma har yanzu akwai sahun marin da yayi min , murmushin ƙarfin hali nayi tare da cewa saidai ka kasheni wallahi bazan daina fita ba idan har baza ka gaji ba nima bazan gaji ba.

     Washe gari da wani irin masifar zazzaɓi na tashi ko sallah asuba kasawa nayi ina kwance a gado na rasa abinda yakemin daɗi har 11:15am , ga gidan namu yau cike yake baƙi “ya “ya da jikoki sai hayani sukeyi ɗan uwan Inna zai dawo daga tafiya shi yasa suka taho tararshi , dan abinda na fahimta shine gaba ɗayan ragamar su bana tunanin akwai wani mai kuɗi idan bashi ba ,

     Murmushin ƙarfin hali nayi yayin da naji murya wata mata akan ita babu yadda za’ayi a cuci rayuwata a gauraya mata zuri’a da jinin Aliyu , sunan Inna ta faɗa tana ci gaba da cewa har sukayi aurensu suka gama ni ban taɓa zuwa ko anguwar daya zauna ba bare nayi tunanin taka ƙofar gidanshi , ɗan iska mashayin banza mashayin wofi duk ma wanda yasan kanshi taya za’ayi ya bari a gauraya mishi zuri’a da gurɓataccen ahali.

     Maganar Kaka naji cikin rawar murya tana cewa ai hannunka dai baya ruɓewa ka cireshi ka yar ko kina tunanin asalin ɗanki yafi ita Maryam ne ? Cikin bala’e tace nidai babu wanda zai haɗamin ɗa aure da wannan yarinyar wallahi , yarinya “yar iska jahilar banza jahilar wofi , sai cin mutunci takeyi wa Babana , abun yamin ciwo amma banda yadda zanyi , 

     Ci gaba sukayi da caccar Babana suna gulmarshi suka tado da tarihin auren Inna ai saboda baƙar kafiyarta taje ta aureshi ta zaɓi namiji tabar iyayenta gashi yanzu taje ta haifo ɗiya ɗaya kwantilkwal ta rasa ubanda zai aure ta , ai tasan a zuri’armu auren zuminci kowa keyi jakkar banza taje ta rasa namijin da zata aura sai ɗan caca , shima ɗayan marar zuciyar dake sakarai ne aka sakota har ya dawo ya aureta , wato mijin da Inna take aure yanzu ko ? 

      Kaka tace to ina za’a kai rabon Maryam ? Cikin ɗaga murya tace rabon wahala ? Hajiya ku hausawa wani abune daku wai sai kuzo kuyi abu idan ya samu damuwa wai sai ku riƙa dangana shi da rabo ne sai kaji mutum na cewa wai rabo ko na abincine sai kaje kaci ka dawo babu wani maganar rabo tsabar kafiyace saboda haka ai itama ɗiyarta ta  tana da ahalin Babanta taje can suyi auren zumincisu su haifo masu bakin hali “yan caca karuwan banza.

     Ikon Allah wai waye ma yace musu auren “ya “yan nasu zanyi ? Aikin banza anba makaho kyautar ido yace banso wari yake dan yasan baya samu ne nima bana san “ya “yanku kuje can kuji dasu nayi maganar a dai² lokacin dana sauko daga saman gado ina tunanin wato ita Inna auren Babana tayi “yan uwanta basa so ? Toilet na shiga dakel ina cewa mune karuwan banza karuwan wofi…..? 

      Ku fiddomin shi Dady ne yake magana a fito mishi da Bello , bayan an fiddoshi Dady yace ina Sultana…..? Bello yace ban san inda take ba , Dady yace wai kunji har yanzu bai tuna inda take ba , tou ku sake markaɗashi muji , saida Bello yasha juyin alalar gero akace ka gano ko tana ina ? A wahalce yace tana tare Dikko , 

      Dady yace wane Dikko ? Cikin nishi yace Dikko U DK , Dady yace kai kana da hankali kuwa ? Idan har ka bari DK yaji ma kana danganta shi da wannan yarinya tou ka sani saiya yanke maka harshe wallahi , ko kana tunani DK zai saurare ta ne ? Bello yace wallahi yana tare da ita , kuma tana zaune a gidanshi na goruba road ,

      Duƙawa Dady yayi kusa da Bello yace ya akayi kasan yana tare da ita bayan shi kowa yasan baya harkar mata , murmushi Bello yayi ya fara cewa.

       Bincike na ya nunamin cewa tana zaune a gidanshi bayan dogon lokaci dana ɗauka ina nemanta , duk inda naje bata nan nasa an kirata da wayoyi da dama daga mutane daban² amma duk wanda ya kirata saita banbanta inda take ,

      Da naga rainin wayan nata yayi yawa saina duƙufa wurin ganin na samota ko ta halin ya ya ! Nayi binke a wurin ƙanin mahaifinta bayan nayi masa ƙarya cewa zan haɗa kan “ya “yan Binna ne a wuri ɗaya shine yacemin baisan inda suke gaba ɗayansu ba , Sultana dai da tana nan amma wasu ke memanta saita bar wurinshi ,

     Bayan an kwana biyu na sake komawa na tambaye shi ko masu neman nata sun sake dawowa ? Sai yacemin kullum sai sunzo yauma zasu zo ? Ban daɗe da zama ba muna fira da ƙarami sai gasu sun sake dawowa , drivern DK ne a da amma a halin yanzu sun rabu kuma bansan abinda ya rabasu ba ,

Bayan sun gama bincike² n su naje muka gaisa dashi Al ‘ Ameen nace masa lafiya kake neman Sultana ? Kai tsaye yace matar Dikko tasa a ɗauko ta kuma a halin yanzu sun gano tana zuwa erudite idan ta tashi tana zuwa islamiyya daga nan sai a nemeta a rasa ,

      Tunda naji tana zuwa Erudite na ɗanawa wurin tarkon , tun safe nake zuwa ina zama a wurin bana ganinta washe gari dana koma sai naga DK ya kawota da kanshi a mota , daya sauketa ya tafi sainabi bayanshi naga ya koma goruba road mai gadin gidanshi shi ya tabbatar min da Sultana tana zama a gidan.

         Tashin hankali shine abinda Dady ya faɗa tare sa cewa wallahi bata taɓuwa a bayyane dole wurin boka zamu koma shine kaɗai ya isa ya kashe mana ita , domin barin yarinyar nan a raye barazane ga dukiyata domun ita kaɗai tasan sirrin komai idan har yarinyar nan bata mutu ba tabbas miliyan 45 na kuɗin gado zasu fito kuma daga cikin dukiyata zasu fito , manyan gonakai dake funtuwa da wanda suke a cikin gari gidajen zama da duk sauran ƙaddarori kai haka bama zai yuwu ba , 

     Da kanshi ya ɗauko kayan Bello yace saka ka tashi mu tafi idan har ba haka ba dani dakai ƙaryarmu ya ƙare , zuciyar Bello cike da kudurirrika akan Dady domin dukan da yasa akayi mishi ya saka kayanshi suka fita daga cikin station suka nufi wurin boka…

      Bayan nayi wanka nayi sallah na kira Inna muka gaisa nace Inna yaushe zaki dawo ? Tacemin sai bayan wata biyu , tambayarta nayi cewa ina so nasan ya akayi kika auri Babana ? Basar da maganar tayi cewa Dikko ma ya kirani ɗazu da safe kashe wayar nayi na ƙyaleta ni bata bani ansar tambayata amma ita tana so tayi min nata maganar daya shafata !

    Ina tsinke kiran Inna na kira wayar Dikko , yana zaune a palon mahaifiyar shi tana ta zageshi ɗaiɗaya akan wai bayayi ma Jiddah adalci baya cin abincin ta yace zai riƙa ci , kuma tayi maganar Mardiyya , yace taje ta riƙa kwana , wato ana sasanci dai tana ta farfaɗo matsaloli kuma akan Dikko , Dikko dai sai haƙuri yake bawa Momy ya ƙagara ya tashi yaje wurin An mata gashi harta fara kiranshi , hankalin shi yana kan wayarshi yaji Jiddah na faɗawa Momy wai tayi ma Dikko magana baya barinta baccin dare ita yana shiga haƙƙinta da yawa maganganun dai babu daɗin ji , kunya ma ta hana Dikko ya iya ɗago kai gaba ɗaya wutarshi ta ɗauke zufa yaji tana tsiraro mishi cikin jikinshi lallai yau ya saki da lamarin Jiddah miƙewa yayi zai fita itama Momy kamar saukar aradu haka taji maganar cikin karyewar murya tace Dikko jirata ku tafi , Momy ba gida zanje ba yana faɗin haka ya fice daga palon ,

     A kunyance ya shiga mota kamar wani yana kallonshi a zuciyarshi yake cewa tashin kallabi amma kullu yaci amanar koko yanzu idan har Jiddah ta sameni da wannan matsalar ai zamuyi maslaha basai ta tonamin asiri ba , dakel ya ɗauki wayar Sultana cikin damuwa yace An mata da Allah yi haƙuri ganinan ina zuwa wurinki yanzu in Allah ya yadda,

      Karka zo gidanmu , me yasa ? Sunyi baƙi sosai kuma banajin daɗi ? Me ya sameki ne ? Inayin rashin lafiya , sannu bara dai inzo , a , a , nidai karka zo , wani abu ya faru ? Babu , gidan ne bana so kazo , ni kuma ina so in ganki bari inzo in ɗaukeki mu tafi goruba ? Nace tou , riƙe wayarshi yayi a hannu yana tuƙi a ranshi addu’a yakeyi Allah yasa An mata ita dai bata da wannan jakancin ,

     Dikko yana fita Jiddah tace ni gaskiya Momy kin barshi ya tafi baki mishi magana ba , basarwa Momy tayi kamar bataji ba tace yanzu dai tunda nayi mishi faɗa saiki tattara Al ‘ Ameen ya maidaki.

      A hankali na fito daga ɗaki na shigo palo kuma har yanzu basu daina zagin Babana ba , shi kuma wanda suka zo su tara har yanzu bai iso ba , cikin sakin fuska na gaishe su babu wanda ya ansa inda Kaka take zaune na kalla tare da cewa zanje in dawo , Allah ya tsare hanya tayimin na fita dan Dikko yamin waya yazo.

      A ƙofar gida na sameshi tunda na fito yake kallona cikin yanayin damuwa har na shiga motar , zuciyoyin kowa na ɗauke da damuwa ni ina tunanin yadda zanyi in faɗawa Dikko abinda akayi min akan zagin Babana da aibatashi da akayi , shi kuma yana jinjina yadda zai faɗamin tashi damuwar ,

        Saida muka tafi yace An mata babu gaisuwa ? Yayi maganar yana miƙomin hannunshi , kamar jira nake yayi magana na fashe da kuka , murmushin ƙarfin hali yayi cewa Allah ya baki haƙuri danshi a tunaninshi maganar da yayimin yasa nake kuka , ni kuma abun duniya ya dameni ,

      Har mukaje goruba kuka nakeyi kuma Dikko bai bani haƙuri ba saida nayi kuka na gaji nayi shiru dan dama da yayi parking bamu fita a mota ba , saida na gama kukan yace An mata meke damunki….? Dakel nace masa damuwa ji nake dama in mutu kawai in huta , ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa kiyi haƙuri dukkan tsanani yana tare da sauƙi , ina tare dake kuma in Allah ya yadda damuwa ya ƙare , kuma kiyi haƙuri dan idan ina damuwa ko kinayin taki zan faɗa miki nawa ki koyi riƙe damuwa biyu a cikin zuciya ɗaya , kuma ki koyi farantamin koda kina cikin damuwarki kiyi ƙoƙari ni ki bani farin ciki.

     Yau idan zan faɗa miki abinda yake damuna ke kanki sai kin tayani jin babu daɗi , juyowa yayi sosai yana kallona yace An mata dan girman Allah ki daina tsokana na muna ɓatawa , ina da lalura ƙatuwa ki tausayimin ki riƙa kwantarmin da hankalina , ki kiyaye ɓatamin rai dan Allah , ki koyi riƙe damuwata kuma ki zama mai  yayemin duk wani baƙin ciki idan kika ganin a yanayi mara daɗi , ni a rayuwata gaskiya ina san mace “yar gayu wayayya mai aji , wadda ta iya tarairayar namiji mace mai sirrinta sirrin ta da ɓoyemin nawa sirrin , macen da zata anshi buƙata ta kuma yi haƙuri ta biyamin ita cikin soyayya da kulawa ba tare data gajiya dani ba , ina san mace ma’aboci ƙamshi da tsabta danni gaskiya ban haɗa mace da komai ba ki zama mai kula da tsaftar jikinki domin ko wane lokaci zan iya buƙatarki kuma ina so duk lokacin dana zo ya zama na sameki a shirye dan natsuwa bata samu babu tsafta ba ƙamshi.

        Har yanzu ke yarinya ce kuma kina magana irin ta yara maganarki tanamin daɗi a haka amma yanayin kallon da kikemin baya ɗaukar hankalina kallon da kikema kowa bada irin kallon nake so ki riƙa kallona ba , dole sai kin zama jajirtacciya ki zama gogaggiya wurin iya sarrafawa da kuma ɗaukemin hankalina ga tunanin kowa saike , 


     Kwantar da kujerar mota yayi ya kwanta saitin zuciyarshi ya taɓa yace kinga ni ba mahaukaci bane ba amma ke kina ganin inayin ɗabi’u irin na mahaukata , murmushi yayi yace ina da lalurar aljannu basu a jikina amma suna tare dani suna shafar jikina yayin da na shiga yanayin fushi , shi yasa idan raina ya ɓaci nakeyi abu kamar mahaukaci yadda kika faɗa , amma ana ta addu’a kuma nima inayi kema ki tayani kinji “Yar matana ? Nace to , ba tare daya kalleni ba yace bara inyi waya a kawo mana abinci muci kisha magani sai in madaiki gida…

CLICK DINKU AKAN  TALLAH SHIKE BAMU KWARIN GYUIWARYIN POSTING

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());



        Wata irin ashariya boka ya babbaka tare dayin wani irin mazurai yana

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button