AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 39-40

Cike dajin tsoro tafara typing

Ameelah ” Dan Allah da gaske kake kataba kisa akan yaudara, kodai wasa kakemun”

Hmm “?? beauty kenan ai babu wasa a cikin maganata, ni makashi matane masu yaudara, amma idan kina tattama jirani kigani”

Gaban ameelah yafadi sosai tace nashiga ukku, motsi tajiyo a bakin kofar dakin da hilal yke kwnce,
Cike da jin tsoro ta juya gurin, bakomai bane kofar dakin ne tayi kuka, domin ta manta dazata fito bata rufe kofarba, a hankali tayi ajiyar zuciya sannan tatashi taje ta rufe kofar tadawo tazauna, tadauki wayarta..
Images tagani guda ukku sunshigo, a hankali tasaka download dinsu, nafarko wata kyankyawar maccece, a kasan pic din an rubuta “wannan itace SAJIDA itace budurwata ta farko, ta yaudareni kuma na kasheta” kuma babu abinda kayi..

Ameelah ta zare ido a zuci take fadan innalillahi wa inna ilaihi raju un”,

Pic nabiyu yabude a hankali tasa hannu ta dannan cikin pic din yabude, shima photon maccece amma bata kai kyau ta farin ba, a kasan photon an rubuta “wannan sunanta FARIDA, munhadu da ita ne ta Facebook, munkusan share wata biyu muna soyayya hartakaimu gamun hadu a fili, data ganni shine tace bata sona, a take gurin zuciyata tahau na kasheta halla hira”

Cab jekaga zufa a jikin ameelah, idanuwanta sunfito bulla2, jikin ta har wani rawa yake,
( nace ” ameelah tahadu da jafa i, hmm farawace idan har bata daina cin AMANAR AURE ba, )

Hannunta narawa ta danna cikin photon na ukku, tashin hankali ?? Gawar maccece anyanka mata wuya gata akwace cikin jini, ameelah jitayi kamar ta burma ihu, (koni da nake gefe saida nakasa tsayuwa, saida bro Abdul yacemun “be a man plx” sannan na tsada hankalina naci gaba da rubutu)

Ameelah takasa tsayawa ta duba abin aka rubuta a kasan photon, domin tataba ganin photon a wani grp nata na whtsapp akace wani yakashe budurwarsa saboda ta yaudareshi,

Zuciyarta duka takeyi sama sama, a akan photo nan text ne kusan guda shida, a tsorace tafara karantasu,

1, wadan nan sune matan da suka yaudareni,

2, a yanzu haka babu ko daya a duniya

3, beauty karki yaudareni domin bazan iya hakurin rashin kiba

4, koda yake ai nasan kina sona bazaki yaudareniba

5, ina fatar kinfahimci maganata ko beauty, karfa kiji tsoron halina niba mugu bane, kuma bana cutawa kowa sai wadda ya cuceni,..

Kafin tagama karanta text 5 taji karar shigowar wani sakon a waje, bakuwar number data gani dazuce akayi mata text da ita,

A hankali ta duba agogon dayake saman screen na wayarta karfe 2:31 tagani, duk tsoro yakamata
Sannan takaranta text nashida

6, nasan yanzu kin tsorata dani. Dan haka zanbarki kije kiyi bacci kisamu natsuwa, Saida safe. Nyt swt drm my beauty???? “

Saman sunansa taduba taga last seen dinsa kusan minti biyu da saukarsa, bata masa reapply ba tafito, bakuwar number data gani wadda akayi mata text kuma number bata nageriya bace sakon takai hannu ta danna sakon ya bude, sakone kamar haka ” ke dan kutumar banki ya inai miki magana kin wani shareni, bana son iskanci fa” …..
(To wata sabuwa inji yan chacha)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button