A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

馃挧馃挧 A DALILIN YAYATA….馃崄馃崄

               馃崄

HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕

Na Feedohm馃挒

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS

1 to 2

Assalamu Alaikum …na canza wannan littafin daga A DALILINSU …to …A DALILIN YAYATA….Saboda naga sister jannah tayi littafin mai irin Sunan…….馃崄

Duk da bana da wayau amma nasan duk lokacin da wannan mai bakaken kayan yazo dole sae mamana tayi kuka ranar ....baya da maganar da ta wuce ta babanmu duk da yayi shekara daya da rasuwa...Mugun haushinsa ya turnukeni ...ji nake da ina da karfi babu abunda zai hana ban mashi jajjagen kasa ba abaki...

..Kai maman tamu bata nan kuma ba yanzu zata dawo ba.....na saka hannu na tare bakin kofar ina mazurai ...

 Yaushe zata dawo ...ya fada fuskar a murtake kamar yarda yake kullun ...

Ohon maka ….kullun kai kazo sae ka saka mamanmu kuka kai kana so kaga maman taka tana kuka ….na fada tare da rike kugu…

Yayata dake cikin gida tana wanke waken da zatayi awara ta kwala man kira ….

Na kalleshi duk na bata rai ina fadin …matsa zan rufe gidan saboda barayi.. ….ban jira komae ba na turo gidan da karfi …ina jin lokacin da ya sake tsaki mai karfi ….nayi saurin dawowa na bude kofar …lokacin har ya bude motarshi zaya shiga ….

Da karfi na kwala mashi kira kamar yarda naji mamana na kiranshi …..Lauya …

Ya juyo yana kallona ….Maman tawa ta dawo Ashe ban sani ba….na sake dariyar shakiyyanci …

Karamin tsaki ya dan ja sannan ya dawo cike da bacin rai ….na bashi hanya ya shiga ni kuma na koma kusa da motarshi na tsaya ….

Ina ganin ya fito na tattare siket dina na kwasa a guje …don nasan mamar tawa batta nan …tsakin da ya man ne ya bani haushi …

Ban dawo lungun ba sae da na tabbatar ya bar unguwar sannan naje kiran da yayata keman …

markade ta bani na kai mata sannan ta tace awarar ta daura saman wuta …

Mamana ta dawo rike da ledar gari yayi zafi ….nayi saurin karba ina dariya ….sae da ta dauko tabarma ta shinfida sannan ta fito da kayan dake ciki …..

Irin kayan kwancen nan ne da ake bata inda take aiki ….ta miko man dae dae nawa sannan ta mikawa yayata wanda zasu mata …nan na dinga murna tare da godiya …..

鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�

Tunda na fito daga gida yaron dake zagaye da kaskon tuyar awarar yayata suka fara watsewa …..bana dagawa kowa cikinsu ….don duk yawancinsu masu cima yayata zalun ne …basa bata kudinta idan sun dauka ita kuma ba mai yawan magana bace …sae dae ta kyalesu ….amma idan ina gurin ko karkashin gadon uwarka ka boye sae na bika na karbo kudina …..bana jin komae idan ka daukar wa yayata awarar naira goma na je har gidanku na kwanto akuyarku idan ma baku da ita zan iya dauko tukunyar ku na taho da ita ..kuma idan duk duniya zata hadu baran ce ga inda na kaita ba har sae anbiyani kudin sannan zan bayar …don bana ajeta gidanmu gudun kar mamana tace na bayar …

Shafi’u dan makwabtan mu na gani sae dauka yake yana ci ba tare da ya kirga ba ….na kafe shi da ido har na zauna bai san da zuwana ba ….sae da ya koshi sannan ya mike yana kakkabe riga ya fito da naira goma ya aje bisa kwandon yana fadin …Saa ga kudinki nan kin biyoni sha biyar …

Kam ubancan …Ashirin da biyar fa …na fada tare da rike kugu..

Yayi saurin kalloni yana washe baki kafin yace …Haba Hudata ina nufin saura naira Sha biyar aljihuna yanzu zan fito mata da ita sae ta biyoni Hamsin …

Nace …owo ai na dauka ta ashirin da biyar kaci …

Ya washe baki …aa ina ni ….ai ina lissafi …ya lalubi aljihu ya fito dasu ya mika mata …ya tafi yana kakkabe hannu tareda kalloni ….

Gurin na koma na zauna ….Yayata ta Bini da kallo tana so tace na tashi amma tana shakkata …tasan in har na zauna ba ciniki zatayi ba sossae ….Mutane na son zuwa amma Ni suke tsoro …

Feedohm馃挒
馃挧馃挧 A DALILIN YAYATA…馃崄馃崄

               馃崄

HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕

Na Feedohm馃挒

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..

3 to 4

      Barister Shehu abunda kake niyar aikatawa sam bai dace ba ...wannan zaluncine tare da yaudara  ...matar data amince da kai ta baka amanar dukiyar mijinta yanzu kuma ta fito kana so ka zalumcesu ...idan har kai baka taimakesu ba to bai kamata ka zaluncesu ba ....

Ya kife wayar tare da juyowa a firgice yana kallon Mahmud daya kafeshi da ido harde da hannayensa a kirji …

Cikin borin kunya yace …so what dan naci amanarta kanwar babata ce …kai Mahmud zan iya komae akan kudi …

Ni kuma Barister Mahmud nace indae har ina raye bara ka taba wannan cin amanar ba ….

Wae me ya shafeka ne da rayuwata ….kaga ka fita wannan maganar …meyasaka tunda mijin nata ya rasu baka je ka taimakesu ba sae yanzu zaka zo kana man wani waazi …

Sabida ta yarda da mutumin da bai kamata ta yarda dashi ba….yana gama fadar haka ya matso kusa da table din shi ya dauki takardun da zai dauka tare da briefcast dinshi ya fita …

Tsaki Barister shehu ya sake kafin shima ya tattara nashi nashi ya bar office din ….daga nan gidansu Huda ya nufa kai tsaye …

Cikin lungun ya hango ana dambe da huda …ta haye ruwan cikinshi sae jibgarshi take yara sae kara zugata suke ….yayi kwafa …yana tunanin da itace ake duka haka to babu abunda zai kaishi rabasu …yafi kaunar a kasheta kowa ya huta don da alamun yarinyar tana neman shigar mashi hanci ….da wannan tunanin ne ya isa gurin …tare da fincikota ya dagata daga yaron da karfi sannan ya dauketa mari …….

Marin ya shigeta sossae ta dago tare da zuba mashi ido kafin ta dauki katon dutse ta jefawa glass din motarshi ta gama ……nan take glass din ya fashe …ya juyo da azama amma kamar walkiya ta bace …..yayi kwafa tare da sake murmushin mugunta yayi sallama gidan …da yake baida katanga da gidan ya fada ciki ba tare da shamaki ba ….

Bayan sun gaisa yake fadawa mamanta cewa ….kudin sallamar aikin babansu Huda malan Ibrahim sun fito …yanzu haka gobe yake shirye shiryen fito dasu banki sae ya kawo masu zuwa jibi …

Tace …ka barsu hannunka lauya …idan ka kawo mana ina zamu ajesu …na tabbata bara ka cucemu ba …don haka ka barsu hannunka ..sae dae ka dan bamu abunda zamu kara jari dashi dan Allah ..

Murmushi yayi yace …aa hajiya zan kawo maki su ki gani bayan kwana biyu sae nazo na karba …don yanzu haka ina shirye shiryen saya maku da gida wanda zaa zuba yan haya a ciki duk shekara sae su dunga baku kudin …idan na kawo kudin jibi to wanshekare zanzo da mutanen da zaku sayi gidan gurinsu sae a karbi kudin a basu ….

To Amma ina tunanin inda zamu aje su Lauya …

Murmushi yayi yana fadin …Allah zai karesu Umma ….ya mike yana fadin zan tafi idan huda ta dawo a ja mata kunne bata jin,magana yanzu daga rabasu fada ta fasa man glass din mota …

Ta hau sallallami tana bashi hakuri tare da fadin idan kudin sun fito dan Allah ya sayi glass din dasu …

Yace mata to …tunda dama haka yakeso …..

鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�

Barister Mahmud indae kana bukatar wani abu cikin kudin ka fada man bawae ka dinga man wani waazi ba na daban ….

Wani kalan murmushi ya sake yana fadin …nawa ne kudin nasu …

Yauwa dan gari …10m …ne …zan baka 1m …..shikenan ko …

Dariya ya sake mai cike da maanuni daban sannan yace …zan baka 10m ka bar masu nasu please

Barister Shehu ya sake dariya yana fadin ….Am not a kid Barister baran taba cin kudinka na zauna lafiya ba ….nasanka sossae …don haka kabar wannan uwar watsin …

Suma wannan sae ka basu kayansu …

Dariya yayi yana fadin gobe karfe biyar na marece zan kiraka na basu agabanka barister ….ya juya ya shige motarshi …

鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�

Karfe biyar dae dae ya kira Mahmud ya mashi kwatancen gidansu Huda sossae yace yazo lungun gidan ya iskesu …ko minti talatin bai cika ba ya shigo lungun ….

Feedohm馃挒
馃挧馃挧 A DALILIN YAYATA馃崄馃崄

               馃崄

HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕

Na Feedohm馃挒

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..

5 to 6

 Motar Barister shehu da ya gani ya tabbatar mashi da yana gurin ...ya fito ya jingina da motarshi tare da harde hannaye ....kafin ya ciro wayarsa ...ya hango Huda janye da tunkiya da gudu ....yana gani ta shiga wani lungu sannan ta fito babu tunkiyar ta cire dan kwalinta ta daure a kugu .....

Wata tsohuwa ta shigo lungun da sauri janye da hannun wani karamin yaro ….

Ke diyarnan yanzu akan naira shabiyar zaki kwanto man tunkiyar dubu sha biyar dan rashin mutunci…..tsohuwar ta fada tare nuna huda da Hannu ..

Me ya saka da nace ki biyani kudina baki bayar ba ….idan kina son tunkiyarki wallahi sae kin bani kudina …idan ba haka naje na sayar da ita na baki canjinki ….ta fada cike da tsiwa …

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button