A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Huda dake tsaye jikin kofa tana jinsu ….ta fita da gudu ..

Feedohm????
???????? A DALILIN YAYATA????????

                    ????

HASKE WRITERS ASSOCIATION????

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…

23 to 24

        Ta fitaa da gudu daga gidan ... ..bata tsaya ko'ina ba sae kofar gidansu Barister Shehu ...Wai dadi taji ganin ba maigadi a kofar gate din.. ...ta kutsa kai ta shige cikin har tsakiyar  falon ...babu kowa a cikin ...katuwar Plasma dake falonsu ita ta nufa ta fito da duwatsun dake cikin jikkarta ta makaranta ...ta dinga bugawa da karfi ...kafin me plasmar duk ta farfashe ...sannan duk wani abunda tasan na glass ne sae da ta fasa shi..harta windows din dake cikin falon sae da ta fasa...!


 Jin karar Glass yasa Hajiyar fitowa da sauri daga sink din wanka. ..ta daura towel  ...don duk tunaninta daga waje karar ke fitowa sae da taji tabbas daga falon take fitowa Sannan ta fito daga toilet ....tana fadin  ..

"Waye anan ? ..."nace wane shegene ya shigo yake mana barna...? ...cak ta tsaya ganin karamar yarinya rike da duwatsu duk ta farfasha masu kayan dake falon ...!!

Nice nan Hudalliya ....ta fada tare da runtumawa da gudu ta fita daga falon ...hajiya ta bita da gudu tana fadin ..

   Bala rike man wannan shegiyar yarinyar karka bari ta fita ...!!!...ganin babu maigadi ya saka Huda sake juyowa tare da jifar Hajiya da wani dutsin sannan ta fice da gudu ...!!

Da sauri hajiyar ta dafe gefen idonta da dutsin ya sameta ..kafin zafin ya saketa Huda ta bace mata da tunani …!!

 "Wace Shegiyar yarinya ce wannan ? ..take tambayar Kanta ..yar gidan wane shege ce ? ...me muka mata dan ubanta ?..."Hurul ..aa Hudiya...mts ...aa ba haka tace sunan ba" ...ta fada tare da dafe kanta tana son tuno sunan ...Da yake bata san Huda ba ...don duk da suke zuwa Huda bata taba biyo Yaya Saa ko Mama ba ...

Barister Shehu ya shigo rike da friut din da Hajiyar ta aikeshi sawowa tun bayan fitar Maman Huda ….turus yayi yana kallon hajiyar da ta zabga uban tagumi zaune tsakiyar falon …

"Yan Fashine suka zo Hajiya? ...ya tambaya a rude  ...

"Yan fashi ko shegiyar yarinya Shehu ?...ta bashi amsa tare da mikewa tsaye..." wallahi wata shedaniyar yarinya ce ta shigo duk ta mana wannan barna ...ban san ko yar gidan uban wa cece ba ...amma tace ko Hurus ...wallahi sunan ya shige man ...amma zan saka a nemo man ita cikin unguwar nan ..."

da Sauri yace …”ko Hudallah? …

   "Ba Hudallah ba Shehu ...na manta sunan ...amma wallahi duk randa na kamo ta taja wa ubanta bala'i dan baran kyaleta ba ...har da ni fa tayiwa ruwan duwatsu Shehu ji binan Yar da idona ya kumbura"..to meye hadinmu da ita ..?..

"Hajiya kinga yi man kwatancen yarda yarinyar  take ...na tabbata Huda ce wallahi "...

"To wacece ita Huda? ..."na fada maka ba haka sunan yake ba" ..."itama da Hu din sunanta ya fara amma nata sunan ban taba jinshi ba ."..

“Huda diyar mamansu Saadatu ce wadda aka kora yau …kuma nasan yarinyar sarai bata da mutunci …bara yanzu zanje idan ma itace ta sake jawa uwarta bala’i ….!!!

Ya fita da sauri …ko mota bai dauka ba ya taka kasa ….baiyi Sallama ba ya fada gidan a fusace …Mama na tsugunne ta rafka uban tagumi …Yaya Saa tana wanke kwanukan da suka ci abincin safe dasu …

Su duka suka mike tsaye ganinshi …

 ya Nuna Mama da hannu yana fadin ..."Ina shedaniyar diyarki ? ....

Ran mama idan yayi dubu ya baci ta kalleshi a fusace zata yi magana yaya saa ta rigata …

  "Bamu da Shedaniya a gidannan ....amma akwaita a gidanku mai dattin da kwali sabon shigan arziki ...banza maciya amana jahilai ...!!! ...ta fada tare da rushewa da kuka ...

“Rufe man baki Shedaniya …akwae shedan irinki mai bin maza ….shegiya karuwa..!!!

Mama ta daukeshi da mari …”Karya kake Shehu har yanzu ban haifi Karuwa ba Wallahi kuma baran taba haihuwarta ba ” ..!!

Ni kika mara ? ...ko da yake ba komae bane tunda har na kwanta da diyarki !!..zafin ba wani bane da zai dameni ....don ko kadan bai kai zafin da zakiji ba alokacin da kika fahimci diyarki karuwar Shehu ce ..!! ..don bana tunanin ban bar maku yaron da zaku raina ba na Shehu ..ko a tunaninku mutuncin da nake maku sonku nake ..? mtsee Jahilai ...to Sha'awar diyarki nake kuma fine ta kawon budurcinta har gadona ....!! ...ba wani shegen da iyasa ya tsaya maku ..matsiyatan banza!!

Wani wawan mari yaya saa ta dauke shi dashi ..tare da sakin kuka …bata sauke hannunta ba ..Mama ta dauketa da mari itama tana kallonta cike da tuhuma ….!!

Sulalewa Yaya Saar tayi bisa guiwarta tana fitar da wani irin gujin kuka ….!!

Dariya Barister shehu yayi tare da fita daga gidan ya barsu cirko cirko …yaya Saa na tsugunne Mama na tsaye tana hawaye …

A zaure yazo fita sukayi karo da Huda …wani mugun kallo ya aika mata ….itama ta sake mashi nata …sannan tayi cikin gidan da gudu jin kukan yaya Saa ….

Yaya Sa ‘a ….dukanki ki ya kuma ?….ta fada tare da dukawa kusa da ita …

Mama ta saka hannu a fusace ta janye Hudar Gefe guda tare da dauke yaya Saa da mari ta janyo kwalar rigarta ta dago kanta ….!

   "Fada man Sa'adatu' ...fadan man gaskia abunda Lauya ya fada hakane ?..ko karya ya maki Sa'adatu?..ta fada tana kuka ...

“Wallahi karya ya mata Mama!! …Huda ta fada ba tare da tasan abunda ake magana akai ba kawae ta tsinci maganar ne…

“Yi man shiru Huda dan Ubanki …!!!..mama ta kwasa mata tsawa ….firgitar da tayi ya sakata fadawa jikin yaya Saa tare da sakin kuka …”Fada man Saadatu “…shin na haifi karuwar Shehu kamar yarda ya fada?.. koko sharri ne .!!…

Cikin Kuka Yaya Saa tace ..”wallahi Mama baki Haifi karuwa ..ba laifina bane Fyad’e yayi man mama …!!

Wani uban duka ta kai mata tana kuka da karfi ….Huda ta rike mata hannu tana kuka …

"Wallahi Mama Hard'e yayi mata ".....ta leka fuskar yaya Saa tana tambayarta ...Yaya Saa Hard'e kika ce ko? ...

Fizge Huda tayi daga jikinta tana dukanta ba tare da tasan inda take duka ba …su duka ukun kuka suke kamar ransu zai fita…

“Dan Allah Mama ki kyaleta na rantse maki da Allah Hard’e yayi mata ..!! .mama wallahi agabana yayi mata …har cewa nayi karka yi mata Hard’e amma yaki saurarena !!! …kuma wallahi Yayata bata Amai kullun!!!. ….Mamarmu dan Allah ki bar dukanta ..bana so ..!!…..ta karashe maganar tare da rike hannun mamar tana kuka…

Wani Uban Mari Mamar ta bata ‘ ..kafin ta hankadata gefe guda ta cigaba da dukan yaya sa’a …amma Huda dawowa tayi jikin yaya Sa’ar mama ta ci gaba da dukansu a tare …

Jikin Mama har ky’arma yake …jin zata fadi kasa ya sakata jingina da bango tana kuka ….sannan taja jikinta ta shige daki ta barsu tsakar gida !!

Feedohm????

???????? A DALILIN YAYATA????????

                 ????

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITER’S…

25 to 26

Da marece Mahmoud yazo kofar gidansu Huda ya aje motarshi ...jingina yayi yana jiran ko Huda zata fito ...don so yake yau yayi magana da mamanta ....

Cikin saa ta fito idanunta jawur tayi kuka har ta gaji ….bisa dakalin gidan ta zauna tare da hade kanta da guiwa ….

A hankali ya tako ya iso gurin ya zauna gefenta ..yana kallonta..

” Hudallah”….

dagowa tayi tana kallonshi kafin ta kalli motarshi ta sake maida kanta gurinshi ba tare da ta amsa ba …

a hankali yace “Me aka maki Huda? ….wani abu kike so ? ..

Kai ta girgiza mashi a hankali tana goge idonta ….

“To fada man mana ‘ …ko mamanki ta dukeki? …

nan ma kan ta girgiza mashi tare da kura mashi ido …

"To Yaya sa'arki aka batawa rai? ...yauwa Hudallah goge hawayen kinji ki fada man ...oya Yaya Sa'a ce? ..ya fada cikin sigar lallashi ..

Daga kai tayi tana fadin …” Ba lauya bane ya cuci Yaya Sa’a yayi mata hard’e …kuma sae da nace kar yayi mata …amma yaki jina!! ..gashi yanzu ya saka mamanmu sae dukanta take …tana kuka …”

Hard’e ? …mene haka Huda?….!

Harara ta balla mashi tana fadin ” karka maidani yarinya mana …kato da kai baka san Hard’e ba ….wanda idan akayiwa mutanen gidansu suyita kuka??? ..ko baa taba maka bane?..

Shiru yayi yana tunanin me take nufi …zuwa can yayi saurin kallonta yana fadin ko dae Raping kike nufi ?

Ba tare da tace mashi komae ba ta mike zata shige gida …yayi saurin riko hannunta yana fadin …” Tsaya man Huda kinji ….please idan kin shiga gidan kice ina son magana da mama …!!

” amma kai mugune …!! ..baka ga irin marin da ta man ba yau” kake aikeni na mata magana …so kake ta sake marina kenan. ?

kamar yana tsoronta yace ” Please Huda ki taimaka kinji ko “…

“Idan ta dakeni ‘ kanka zan rama wallahi “

Da sauri yace ” Na yarda Hudallah “

Shiga tayi ciki zuwa can ta fito tace mashi Idon mamar a rufe yake ….ta mata …magana taki budewa …..ce mata yayi taje tacewa Yaya Sa’a dan Allah yana son magana da ita ..

Kafin ta bashi amsa yaya sa’a ta fito daga gidan da gudu tana kuka …tare suka shiga gidan har da Mahmoud din…

Mama na kwance bata motsi daukarta yayi da sauri ya sakata mota sannan yaya saa da huda suka shiga ciki suna kuka sannan yaja da gudu suka fita daga lungun …

Direct asibiti ya nufa da ita …cikin gaggawa aka amsheta ….bayan an dubata ne aka tabbatar masu da tana raye ..hawan jini yayi attacking dinta sossae … Bp dinta 210 …

Daga Hudar har Yaha Saa kuka suke …Barister Mahmoud kuwa tsaye yayi yana kallonsu ..shi ya biya kudin komae …aka hada mata magunguna ..

Har isha’i yana asibitin …sae da ta daeo normal sannan likita yace zaa sallameta su tafi gida …..

Barister Mahmoud ya dauko su ya kawo su gida …da zaya tafine ya fitk da 20k ya bawa mama yace su sayi abinci kafin ya dawo ..

Sam Mama taki karba …tace wanda ya mata bata sani ba ta gode amma wannan bara ta karba ba don yanzu bata bukatar taimakon duk wani mutun Taimakon Allah kawae take so …Babu irin rantsuwar da bai mata ba …amma taki karba …

Ganin yafi damuwa da Huda ne ya saka Yaya Sa’a saurin janyo huda jikinta tana hawaye …don bata kaunar wani namiji ya kula Huda yanzu …..a iya saninta zata iya kashe duk wanda yayi kokarin batawa Huda rayuwa …

ganin kamar basu bukatar shi ya sakashi tashi ya tafi …zuciyarshi cike da tunanin maganar huda …”wae Hard’e”…what does she means? …haka yayi ta sake sake har ya isa gida …

Yana Shiga Mama tace ya dauki matarshi ya tafi da ita …don wallahi ta gaji da Hanne ….!!!…

Ba dan yaso ba ya shiga dakin Hanne tana kwance sae barcinta take hankali kwance ….pillown da ta daura kanta ya dan buga kadan

ta mike ba salati tana fadin …”wane banzane mutun na bacci yake tadashi ?

Ba tare da yace mata komae ba ya juya zai fita …”sam hanne ba da’a” …abunda ya fada kenan a ranshi …

hannunshi ta riko “Ohhhh …Yaya ne ….Yi hakuri bansan kai bane yasin” ….ta fada tana dariya

ba tare da ya juyo ba yace ” ki iskeni falo zamu tafi gidan yau” …

  Ihun dadi ta sake tana fadin " Haba yanzu  naji magana amma an kunshe mutun cikin gidan sirikai ba damar ya sake sae shegen sa ido "...

Ko nuna alamun yaji me take fada baiyi ba …ya fice daga dakin …kafin ya zauna har ta fito janye da uwar jikkar …

Mamanshi yayi wa bankwana tare da Abba …sannan suka tafi ..da yake bai ci komae ba ..ya tsaya wani karamun restaurant zai sayi abinci …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button