A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ba tare da ta bashi amsa ba tacigaba da kukanta ....shafa bayanta yake a hankali ..yana so ta mashi magana amma ta kasa ..sae uban kukan da take ...

Liman ya taso ya dafa bayanshi tare da yi mashi bayanin komae …

A tsorace ya kalleta da idanuwanshi da sukayi jawur …kafin ya sakw rungumeta sossae yana bubbuga bayanta ….

Suna nan tsugunne har aka gama addu’ar sannan aka fara shawarar wanda zai tafi da Huda gidanshi …don babu wanda yasan dangin babanta bare a kai masu ita…

Liman yace “Har ga Allah ina son daukar Hudallah amma ina tsoron uwar dakina ? …sam bata kaunar taga wani ya rabeni sae ta dinga azabtar dashi …kuma rikon Huda ba zai yiyo haka ba …domin ita marainiya ce ta sha banban da sauran yaran da ake rikewa kara zube ….dole wanda zai dauketa .. ya guji kukanta da bacin ranta …sannan kuma bazai saketa hakanan ba ….Saboda marainiya Mutun na iya shiga wuta !! …Na tabbata uwar dakina bazata taimaka man ba mu riketa tsakani da Allah ba tare da cuta ba …”..Amma dan Allah cikin ku idan akwae wanda ya tabbata zata iya zama gidanshi cikin farinciki …wallahi nayi alkwarin duk wata zan bashi buhun shinkafa da taliya da jarkar mai da kudun cefane …dan Allah wani ya taimaka !!!

Mahmoud dake tsugunne yana jin duk abunda suka fada ....ya dago Huda daga jikinshi tare da share mata hawayen da suka wanke mata fuska ..

“In je na dawo ko Huda ? …zauna kinji …!!! ..ya zaunar da ita sossae sannan ya tashi ya matsa gurin

Yace “Malan za’a iya bani Hudallah ….na maka alkwarin riketa kamar uwa da diyarta …sannan in Sha Allah barata taba kuka ba ta sanadiyata ….Dan Allah ku bani ita ..”

Liman ya dade yana kallonshi kafin yace “Wane unguwa kake Yaro ? …kuma dama kasan su ne ? ..

Cikin Sauri yace …”na sansu wallahi ba tun yau ba ….nan take ya fadawa liman din address din gidansu ..

Liman Yace “Alhamdulillah Mahmoud ai nasan mahaifinka …duk wata yana kawo mana taimako …na tabbata zata ji dadi gurinku !!!

 Godiya sossae yayi kafin ya koma gurin da Huda ke zaune ....

“Zaki bini ko Huda ..zan baki rayuwa mai cike da jin dadi ..zan maye maki gurbin Yaya Sa’anki …Muje ko? ..ya fada a hankali tare da tsugunnawa kusa da ita

dagowa tayi a hankali tana kallonshi …bakinta ya motsa ahankali sae dae bai ji abunda take fada ba ….gurin da su liman yake tsaye ta nuna mashi da hannu…..

Tare da fadin … ..”Lauya”

Feedohm????
???????? A DALILIN YAYATA????????

                  ????

HASKE WRITER’S ASSO????

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…..

35 to 36

  A hankali ya juya yana kallonsu ...Barister Shehu ya gani rike da wata takadda yana nunawa liman din rai a bace ...

Da sauri ya mike ta rike mashi hannu tare da binshi suka isa gurin …

Cikin fada barister Shehu yake fadin “Dakata malan me ka sani dangane da wannan gida …in jin nine lauyan ubansu tun kafin ya rasu ….to wannan gidan da kake wani hakilo akan basu sayar dashi ba ….to tun kafin uwarsu ta rasu ta sayar man dashi kuma ga shaidata nan”…ya mikawa Liman Takardar gida

Barister Mahmoud ya karbi takardar ba tare da ya kalleshi ba …ya budeta yana karantawa …tabbas takardar gidan ce amma ya tabbata karya yake ba sayar mashi da ita akai ba !!

 Dan Murmushi ya saki kafin ya kamo hannun Barister Shehu ya damka mashi takardar yana fadin  ..

“Malan ku bar mashi ya tafi ….Barister har kayan dake cikin gidan ya kamata ka yi takarda don babu abunda zatayi da su ….A juri zuwa rafi “…..

Ya juya tare da jan hannun Huda suka tafi ba tare da ya juyo ba …Huda kuma tafiya take amma Barister Shehu take kallo ta kasa dauke idonta akanshi har suka isa bakin kofar ….

Gaba ya bude mata ya sakata sannan ya koma ya shiga suka tafi !!!

Falo suka iske hakima Hanne kwance saman kujera tana kallo ... Suna shiga ta mike da sauri tana dariya ..ganin Huda ya sakata matsawa da sauri tana fadin ...

"Tsaya  tsaya ...karki shigo ....yaya ina ka samo wannan yarinyar duk datti ...!!!...karki shigo bara na miko maki towel kiyi wanka a wancan tap din sannan ki shigo ...yaya yar aiki ce? ..

Bai saurareta ba ya janyo Huda Har tsakiyar falon …tare da dagata sama yana dariya ya zaunar da ita saman hannun kujera ….

Juyowa yayi gurin Hanne yana fadin “Hudallah .. Daugter ta …Best friend dita …. Little sister ta ….Heart cherry … My Queen ……Kin fahimta ? ..

Ta gurin Mamanka kuka hadu ? …ta tambaya a dakile

Huda ya kalla yana fadin … Hudah ta ina muka hadu ? …ta nan ko ? …ya taba kirjinshi yana mata murmushi ..

Bakinta ta gumtse kafin ta fara kyafta idanu tana kallonshi …..

Oh Sorry …Taso muje kiyi wanka kici abinci…mu dawo na baki labarin Abunda Yaya Sa’armu tace na gaya maki …

Da gaske ? …ta fada tare da fito da idanu ..

Kai ya daga mata yana fadin …”Yes …muje “…… Ya mika mata hannu ta sauko ..

Hanne dake tsaye tana kallon ikon Allah tace ..”Wae Wacece wannan ? …

Kallonta yayi a fizge yana fadin .
“.Hanne bara nayi wanka zamuyi magana kinji ko …”

Binshi tayi da kallon har suka shige part dinshi ….

  " Kutmar Uba...ban taba shiga  part dinshi ba amma ya shiga da wancan ... " ..ta dafe kai tare da fadin ..."to ko dae kanwar uwarshi ce "

Dae dae zai fito ya baro Huda tana wanka yaji tana fadin Kanwar uwarshi ….

Shigowa yayi Falon yana fadin ..”No Hanne ba kanwar Uwata bace …Marainiya ce ta wuce duk yarda kike tunanin”

Wani Uban tsalle tayi tare da mikewa ..”Kuma dan Iskanci anan gidan ?

A fizge ya kalleta yana murmushi yace ” Ki rushe in da kika gina man !!!

"Wallahi bata yiyuwa Yaya ...bamu gidan marayu " ...ta fada tare da zama kusa dashi 

Look Hanne !! ..kina son zama dani ? ..

Gyad’a kai tayi tana kallonshi …

“Good …to ki so wancan yarinyar ….”

“kwana nawa zatayi ?…ta tambaya a hankali …

"Abadan da'iman".....shima ya fada a hankali ..

“Amma ai nan da shekara 8 idan tayi aure shikenan ko yaya ? ..

Kallon da ya sake mata ne ya sata yin lakwas …tashi yayi ya shiga dakin …Hudana Zaune bisa kujera da alama lokacin ta fito daga wanka …

“Come on …kin yi alwala ? ….ya fada tare da fito da t shirt daga drawer shi …red mai dogon hannu ya mika mata …

“Tashi ki saka kafin anjima mu je Super market a sayo maki naki ko ?….

Karba tayi ta sanya …tazo mata iya guiwa ta mata kyau sossae …ya kalleta yana murmushi ..

“Ayehhh Hudata ..kinga yarda kikayi kyau …come on …na maki photo ? …

Uhm Uhm …ka fada man abunda Yaya Sa’an tace ….tayi rau rau da idanu …

Hannunta ya kama ...tare da dukar da kanshi saitin fuskarta yana fadin ..."Sae kinci abinci sannan "...yaja hannunta suka fito falon ...

Feedohm????
???????? A DALILIN YAYATA????????

                ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS….

37 to 38

     Still Hanne na zaune inda ya barta ....

” Me kika hada mana lunch ?…ya fada tare da kallon Hanne …

“Lah Yaya bana fada maka ba tun shekaran jiya kaina ke ciwo .”.
..

“Good”…ya fada tare da fadawa kitchen …yana janye da hannun Huda ..

Zaunar da ita yayi bisa table din dake cikin din…..sannan ya kunna gas ….

“Me kike so ki ci “…ya fada dauke da murmushi tare da kura mata ido …

Lumshe idonta tayi ba tare da tace komae ba ….Tabbas yasan Har yanzu Yaya Sa’a na ranta ….hannunta ya kamo …

“Hudallah …zaki ci Indomie ? …

Girgiza mashi kai tayi alamar aa …..

“To me kike so ? … Cous cous ..?

nan ma girgiza kanta tayi …

Dago kanta yayi yana kallonta …”Su kadae na iya Huda …ya fada a hankali …ko na soya maki Dankali? …

Bude idonta tayi da ya ciko da kwalla tana kallonshi …Ganin zatayi kuka ne ya sakashi juya mata baya tare da kurawa Tagar kitchen din ido …wanda a zahiri hankalinshi na kan yarinyar …!!

Da sauri ya juyi yana fadin …Yaya Sa’a tace idan har Hudallah na kuka to barata taba samun sauki ba a ranta ….

Share hawayen tayi da sauri tana fadin ..” To idan na daina fa ? ..

Idonshi ya lumshe ….”Allah zai sakata aljanna taji dadi sossae “,..

 "To na daina kaji ...kace mata na daina kukan ...taji dadi sossae dan Allah ...kuma kaji kace har yanzu ina sonta ....!!! Idonta ya ciko da kwalla tayi saurin maidasu tana kakaro murmushin dole ...


Rungumeta yayi tare da mata peck a goshi ...sannan ya daura tukunya ya zuba ruwan zafi tare da kayan miyan leda ya bata albasa ta yanka mashi ....cikin mintin kadan ya dafa masu indo mie da kwae ...ya juye masu a plate...


 Hanne ya kalla yace ..."Come and enjoy your lunch ...ya aika mata wani mugun kallo ...

Tana son taci amma babu fuska duk da an mata tayin ….!!!

••°°••

Satin Huda Biyu gidan ta fara warwarewa …Sae dae matsalan idan ya fita hanne ta sakata a gaba …da zagi …

Tana zaune a falo ita kadae sae game take abunta tana dariya ….Hanne ta shigo tare da fizge game din ta wurga saman kujera …

Kunnenta ta murde ta zauna kusa da ita tana hararanta …

Da sauri Huda ta dafe kunnen tana ihu ….

Bakin hanne ta buge tana fadin “wae ke dan ubanki idan Yaya ya shiga dake daki me kike ce mashi da kuke dadewa a ciki kuna dariya”

Cikin jin zafi Huda tace …”Fada mashi nake ke muguwa ce kullun idan kina zaune kiyi ta man tusa ..sannan bakya wanka !!!

Wani uban rankwashi ta kai mata akae …ihu ta sake da karfi ..

Dae dae lokacin Mahmoud ya shigo falon …jin Ihun Huda ya hanashi karasa sallamar ya shigo da gudu yana fadin…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button