A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hudah …lafiya ….tsaye yayi yana kallon Hanne dake shafa kan Huda tana murmushi tare da fadin “Kai baby don na maki ci uku shine zaki man wannan ihu “..

Kallonshi Huda tayi kafin ta sake murmushi ta ruga da gudu ta fada jikinshi …dagota yayi yana fadin..

“Hudah Game kuke ? ..

Hanne ta kalla sannan tace “Eh Uncle Game muke irin na aunty muguwa …Dan Allah Uncle’ banda mugunta irin ta Aunty Hanne sae ta murde man kunne da karfi ?

Hanne ya kalla duk tayi fiki fiki …kafin ya maida idonshi kan Huda …

“Me kika mata? ..

Feedohm????
???????? A DALILIN YAYATA????????

             ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…

39 to 40

       Hanne tayi karaf tace .."Amma Hudah ke munafuka ce ...daga wasa ? ...

Murmushi yayi kasa kasa ….sannan ya mikawa Huda ledar da ya shigo da ita …”Jeki dauko littafin da na kawo maki jiya …”

Babu musu ta karba ta shige dakinshi da gudu …

Bai cema Hannen Komae ba ya koma ya zauna tare da lumshe ido ...ita da kanta tazo tana bashi hakuri ...sae dae yayi murmushi ba tare da ya bude idonshi ba ...

Fad’uwar Hudah jikinshi ya sakashi bude idonshi yana murmushi …Sossae ta zauna jikinshi ..ya karbi novel din yana karantawa ….

••°°••

Barister Shehu na zaune gida kusa da Hajiyarshi ..phone din shi ta dauki kara ….

Kamar bara ya dauka ba …ganin babban yaronshi dake kular mashi da kasuwar zinaranshi ce ya sashi dauka wayar ..

“Hello …Bello ya akai “,..ya fada tare da saka wayar handsfree ya daura saman hannun kujeran …

daga dayan bangaren akace “Oga wallahi wata mata ce tazo ta sayar mana da gold dinta na 2.6m …bayan ta tafine muka gane gold din jabu ne …kuma mun rasa inda ta shiga a kasuwar…!!

What ? ….Uban wa cikinku ya auna zinarin lokacin da zaku saya ? …ya fada a firgice …

“Wallahi oga mu duka muna tsaye Bala ya auna ….Amma…

“Shuttt up …banzaye taya mace zata sayar maku da jabun zinari ku kirani kuna fada man bayan baku kamota ba ….wallahi bazanyi asara ba …kune zaku dauketa wawaye.!!!

Kashe wayar yayi yana kallon hajiya sae gumi ke keto mashi ….

“Zancen banza ne shehu …ba yarda za’ae mu dauki asara su zasu dauketa wallahi ..
barsu karka kara kiransu …!!

Amma Hajiya…

“Karka ce komae …gobe zan tura Auwalu gurin …zasu fito da su ne “

Tashi yayi zai shiga daki …tayi saurin tsaidashi tana fadin …

“Wae Shehu ya maganar yarinyar nan ta gidan Alhaji Tukur …Kun dai daita ?

Sosa kanshi yayi yana fadin ..”Adama wae Hajiya” ..

“Ita mana “…

“Nifa dama ba aurenta zanyi ba hajiya ..kawae mum hutane …Yarinyar duk da tana diyar mai kudi sae shegen roko ..!!..So nake Allah ya bani ta kirki sae na aura ..!..Yauwa Hajiya naga wata yarinya gidan liman ko ita za’a neman man …tana da bala’in kamun kai ga addini …kuma suma ba talakawa bane !!

Hajiya ta saki dariya tana fadin …Wae Maryam …nima kaina yarinyar ta kwanya man ..akwae natsuwa gata yar mutunci..bara idan dad dinka ya dawo sae in masa magana !!!…

MARYAM… Diyar liman ce wanda yace bara ya dauki Huda ba amma asali bashine ya haifeta ba agolace a gidan ….saboda Mugun Halin Matarshi ya hanashi daukar Huda !!….Hajiya zubaida itace uwar maryam …su biyune ya’yanta …daga Maryam sae Abdallah kaninta ….Shi liman Allah bai taba bashi haihuwa ba har yanzu …kuma bai taba damuwa ba !!,..Kullun tana sanye cikin zunbuleliyar hijab …a fuskarta kamar sahila amma azuciya sam babu tsoron Allah …idan ta saka hijab a unguwarsu tana fita daga unguwar zata kira saurayinta yaxo ya dauketa ….duk wani club dake garin babu wanda Maryam bata zuwa ….yar’ bariki ce ta k’in k’ari ….

Feedohm????
???????? A DALILIN YAYATA????????

                   ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…

41 to 42

     Duk unguwar kowa zai shedeta mutuniyar kirki ce ....mamanta kadae ta san irin rayuwar da take ...shima don tana kawo mata tsabar kudine ....ko da rana Daya liman bai taba fahimtar abunda ke faruwa ba a gidan ...!!

Bayan da ubanshi ya dawo hajiya ta mashi magana aka fara nemawa Barister shehu auren Maryam …

Wata Biyar aka saka bikin …ko da yaje gidansu Maryama bai samu matsala da Ita ba …ta amsheshi hannu bibiyu …

Lokaci na zuwa aka daura auren ...an kashe kudi sossae ...don ko lefenta set biyar ne ..Gidansu Huda Barister Shehu ya saka a rushe suka hade da nasu ...aka dibarwa Amarya nata part din !!! ...

•• •°°•• •

"Huda kira man Auntynki "...ya fada tare fa sauketa daga jikinshi ...

Uncle …

Hannunshi ya saka saman lebenta tare da nuna mata kofa …

Ta lumshe ido kamar yarda yayi sannan ta tafi da gudu …Hanne na kwance tana waya tana fadin …

“Wallahi kawata na gaji da wannan shegiyar yarinya …Ni kawae zance ya sawake man na tafi gidan iyayenshi idan ta tafi ya maidoni”

tayi shiru tana saurarenta ..
kafin tayi dariya tana fadin …”Haba kawata ya za’ai yanzu na iya zama kauye …ai sae dae gidan iyayenshi ” …don ni da kauye hai hata hai hata ….Ke nifa tunda nazo ba abunda ya shiga tsakanin mu …..abun har ya fara damuna kawata “

“Aunty idan kin gama wayar Uncle na kiranki …amma dan Allah kicewa shegiyar kawarki ina da baba …itane shegiya bani ba ..!! ..idan kuma ke kika ce man shegiya to …Allah ya isana !!!

Bata jira amsarta ba ta kwasa da gudu ….

Tarota yayi yana fadin “Bara ki bar gudu ba ko Huda ? …baran sake goyaki ba !!…

“Sorry Uncle na rantse maka da Allah na daina ..kaji …!!!tayi rau rau da ido ..

Hannunsa ta kamo …Uncle wae idan Aunty Hanne ta tafi kauye tana da tsayayyene? …

 Dariya yayi kasa kasa ..." Ban gane ba Huda !!!

“Yauwa …Ina nufin tana da wanda zai aureta …?..

zaunar da ita yayi saman hannun kujeran ..”Me ya faru Hudah ?..

 "Kawae Uncle ka saketa mu zauna mu kadae ,,!! ..Kaji ? ...ta fada tare da langwabe kai ..

Murmushi yayi kasa kasa ...kafin ya dago fuskarta yace .."Idan na saketa ke zaki aureni "..?

“Eh mana …ko yanzu ma ai ina aurenka Uncle …tunda ni da aunty muke tsare maka gida …kai kuma idan ka dawo ka dafa man abinci ko ..?

Hanne ta shigo tana fadin

“Wallahi munafuncin wannan Huda kullun k’ara yawa yake …banda muguwar fata ni kike fadar a saka ?…Idan an sakeni Uwarki zaa aura?,..

Look Hanne !! ...ya daka mata tsawa ...wallahi kar na kuma jin kin zagi wannan yarinyar ..."

Bata ce komae ba ta zauna tana hararan Huda ….

“Ki shirya gobe ..ko kinki ko kinso ..da safe zamuje kauye a gano kawu ..!!

” To dan Allah yaya ka sawo man wanan safar ta leda mai kama da takalmi … “

Cikin Mamaki yace "me zakiyi da ita ?

Dan dukar da kai tayi tana fadin..”Wallahi yaya baran iya taka dattin gidan mu ba yanzu …bana son kazanta …!!!

Dariya sossae yayi …ba tare da yace mata komae ba yaja hannun Huda …Kin tafiya tayi ta tsaya gurin ..

Muje mana !!

” Uncle ba kace zaka goyani ba ?…ta fada a hankali …

Murmushi yayi …ai ba yanzu nace ba ko? …ya dage gira ….

Kafada ta make ..”Yanzu mana ” ..

“To naji …zoki hau muje …” ..duk abunki iyakarki toilet zan direki !!!

Shegiya ...hanne ta fada a hankali ...

Gwalo ta mata tana hura hanci ..tare da zaro ido …

a harzuke Hanne tace ..”Zanci Ubanki Hudah “…

Mahmoud ya juyo tare zabga mata harara …

Feedohm????

???????? A DALILIN YAYATA????????

               ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…

Yaseen mutane ma sun maidani yarinya …to wallahi am not a kid ..kyas nake kallonki …wae na bata un edited copy taza duba man ..yo Fathern ki ya man typing????????????????????

43 to 44

   Karfe biyun rana suka isa kauyen ..lokacin anata haramar shiga masallaci ....Mahmoud alwala yayi ya shige masallaci ya barsu Hanne zasu shiga cikin gidan ..

Hanne ta tattare Zaninta sama tana yatsina fuska …ta shiga gidan …da gudu kaninta ya taho yana fadin …

“Ga Hanne Ga Hanne …..”

Da sauri taja baya tana fadin ..."tsaya tsaya boy ...dontu touchi mai wallahi _dont touch me_ "

Sakin baki yayi yana kallonta tare da tsayawa jiki a sanye ….Hudah ta kura mata ido tana dariya kasa kasa ….Hanne na lura da Hudah ta zabga mata harara tare da jan karamin tsoki ….

Inno ta fito tana washe baki tare da lale marhabun …a dakile hanne ta amsa sannan ta isa tabarmar da inno ta shinfida …dank’walin kanta ta cire ta shinfida saman tabarmar sannan ta zauna….ko da inno ta kawo masu ruwa a kwano …cewa tayi Hudah ta tashi ta dauko mata swan water a mota don bara ta iya shan ruwan randa ba!!….

Hudah bata amsa mata ba haka kuma bata tashi daga inda take ba ..!!

Basu dade ba Hanne ta azalzalesu suka fito …a mota banda Dariya ba abunda Hudah ke yi …Hanne kuwa ta gama k’uluwa don sae Hudah ta kalleta ta madubi sannan ta tuntsire da dariya ….Shi kanshi Mahmoud ya fara gajiya da dariyar Huda …ta madubi ya kalleta yace ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button