A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

” Uncle “…ta fada a firgice ..
Tsawa ya daka mata “Da uban wa kike waya ” ..
Dukar da kanta tayi kasa ..bara ta iya jin zata fada mashi gaskia ba yanzu koda zaya daketa ne kuwa …
Wani uban mari ya bata yana fadi “For how long kika mallaka mishi komae naki …Uban wa yace ke ta shi ke ..?
“Uncle …!!
“Shut up !!! …ashe abunda yasa kike nacin ki ci gaba da karatu kenan …soyayya Hudah as your age 18 years fa .!!….girgiza kanshi yayi idanunshi suka ciko da kwallah …first time kenan da ya taba kai hannunshi jikin hmHudah ba da niyar ya lallasheta ba sae don duka …juyawa yayi da sauri zaya shige dakinshi…
Hannunsa ta riko tare da dukawa saman guiwarta
Cikin kuka tace ..”Na tuba uncle ..baran sake ba wallahi …i promise baran yi soyayyar gaskia da kowa ba wallahi ..please Uncle for morethan 6 years kana tare dani ba …baka taba sakani kuka ba …sae ni uncle ?sae nice Hudah zan saka fitar hawaye a idon mutumin da yafi kaunata a duniya …please uncle ka yafe man dan Allah ..!!!
…
Juyowa yayi a hankali yana kallonta kafin ya saka hannu ya dagota tare da share mata hawayen da suka bata mata fuska ...sannan ya hade ta da jikinshi ....
“Bana so Hudah it really hurts ….”…ya fada a hankali
Daga mashi kai tayi…tare da lafewa jikinshi …
••°°••
Barister Shehu na zaune maryam ta fito rike da keys din mota .. ta matse cikin riga da wando …binta yayi da kallo …ta gabanshi ta wuce zata fita …
“ina zaki haka ? …bakya da hankaline baki ga yarda kike ba ? …ya tambayeta tare da mikewa tsaye …
Wani kallon ta watsa mashi …”In da nafi wayau zan koma ..don na lura angulu ma ta koma gidanta na gaskia !!!
” Me kike nufi?…kina nufin a haka zaki fita wae ? .
“Kana mamakine? …Shehu kenan …to zan fita sana ‘ane …oh na manta baka san me nake ba kafin ka aureni ko …?
Kallon mamaki ya jefa mata !!
"Haba meye na wannan kallon ...karfa ka manta akan karuwarka ka mareni da safe ....nima kuma naga nawa karuwan suka can suna jirana ..shine naga ya kamata na kai masu ziyara ....!!!
Ficewa tayi ta barsa tsaye sake da baki …ga uwar sha’awarta da ta taso mashi ….safina ta fito daga daki da gudu tana kiran …
"Mah!! ..Mah ....zan bi ki "....itama fita tayi waje ta barshi ..... ganin ta saba fitane ta shiga part din hajiya ya sashi kyaleta tare da komawa daki ya hade kai da guiwa ..
Feedohm????
???????? A DALILIN YAYATA????????
????
HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )
Na Feedohm????
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..
55 to 56
Maganganun Maryam suka fara mashi yawo ....wae karuwanta ...tabbas ba tun yau ya kamata ya gane maryam yar iska bace ...tunawa yayi da first night dinsu ....ba cikakkiyar mace ya sameta ba ...amma salon da ta dinga mashi shi ya hanashi mata magana ....sae yanzu yake tuno wasu abubuwa wanda bariki irinta maryam ta hanashi gane komae ...
Wayar Hudah ya fara nema ….Switch off …yayi kira yafi dari a take amma bata shiga …kanshi ya fara mashi ciwo ya rasa inda zai saka kanshi yaji dadi …bama maryam tafi damunshi ba yanxu …aa Damsel dinshi …gashi bata turo mashi address din ta ba bare ya je gidansu
Zazzabi yake neman rufeshi …amma sae kokarin kiran Hudah yake ya kasa samunta …jin ihun hajiya ne ya sashi tashi ya fita yana dafa bango …..ko iya bude idonshi baya yi …
A bakin gate ya ga Safina a hannun dad ..hajiya kuwa sae ihu take kamar tababba …a hankali ya matsa gurin
“Lafiya hajiya me ke….”Chak ya tsaya ganin jini a jikin Safinar …
Saurin karbarta yayi a hannun dad din a firgice “Dad me ya faru …me ya sami safinar ..ku fada man meke faruwa ya naga jini a jikinta ..?…take idonshi ya ciko da kwallah jikinshi sae k’yarma yake ..
Dad yace “Fyad’e aka mata Shehu ….an cucemu Allah ya Isa!!!…ya dafe kanshi tare da tokare hannunshi da bango …
Zaman dirshan shehu yayi tare da sakin kuka ...ji yake da zaiga wanda ya lalata mashi diya ba abunda zai hana ya kasheshi ....
••°°••
Hudah na zaune Uncle Mahmoud ya shigo rike da leda ….
"Uncle sannu da zuwa" ...ta fada a hankali ..
Dan kallonta yayi tare da sakin murmushi sannan ya mika mata ledar …sabuwar wayace Iphone6 …tare da mtn sim da recharge card din 5k …
Wanni uban tsalle ta saki tare da rungumeshi tana sake mashi kiss ba tare da ta sani ba ….tureta yayi da karfi ya shige daki yana mayar da numfashi …..Jingina yayi da kofar tare da lumshe ido …
Huda kuwa Dakin Aunty Hanne ta nufa da gudu ta nuna mata …..
“Aunty Uncle “…..ta fada tare da rungumeta ….
“Uncle na sonki Hudah!!!! …hanne ta fada da ma’ana biyu ….
Ba tare da ta fahimce ta ba tace ..."Na sani Aunty Hanne ....Ban san dame zan saka mashi ba ...?
“Da kanki Hudah ‘Zuciyarki ya dace ki bashi Hudah…!!Hanne ta fada tare da iko Hannun Hudah ..
Da sauri ta kalli Hannen ..."Aunty amma da wasa kike ko ? ...ta tambaya a hankali
“Ba wasa nake ba Hudah ….!!!..ta bata amsa kai tsaya
" Aunty ki daina wannan maganar please ...Uncle bara ya iya sona ba ..kawae yana tausayina "...ta mike tare da fita daga daki ...
Tana komawa dakinta ...ta hada wayar ...Number barister shehu tayi dialing ...har ta kusa yankewa sannan ya dauka ...yana jin maganarta duk ya rude yana tambayarta lafiya ....Ce mashi tayi bata garin ne taje maiguri grandynta bata lafiya .....
Bai yarda ta kashe wayar ba sae da ta bashi full adress dinta sannan .....ce mata yayi da marece zaya shigo yau ...
Tun wajen karfe 3 ta fara nacin uncle Mahmoud ya barta taje gidansu lubna ….hanata yayi daga farko ..sae da ta fara mashi kuka sannan ya barta ta fita da zunbuleliyar Hijab dinta …..
Karfe 4 ya kirata yace yazo kofar gidan …suna zaune da lubna alokacin …ta dan kalleta kafin tace ..”ya jira zata aiko yaro ya shigo dashi …”.
" Lubna yazo !! ...ta fada hade da sauke ajiyar zuciya..
Fahad Lubna ta kwalawa kira tace “yaje ya shigo da bako yana bakin gate …sannan ya kaishi falon baki “….yaron ya amsa da “to” ya fita da sauri
Mintina kadan yaron ya dawo yace ya kaishi …Huda tayi murmushi sannan ta ciro 1k tace yaje ya sawo chocolate …kin karba yayi ya koma ciki da gudu
Lubna ta sake mata harara …”Damsel karki fita da wadannan kayan daukar Alhakin zaiyi yawa …ko fa rana baa sa maku ba !!
“Da waye …? ..Hudah ta fada tana kallon cikin idonta
“Barister mana …sae ki rikitashi wallahi …”
Yar dariya ta sake mai sauti tace “Kina tunanin aurenshi zanyi ke !!!
Da sauri Lubna ta kalleta …
Amma kafin ta bata amsa ta fice daga dakin da sauri …
FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????
????
HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & Perfect writers )
Na Feedohm????
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…
57 to 58
Cikin takun jan hankali ta shiga falon dauke da murmushi a kyakykyawar fuskarta ….duka jikinta juyawa yake …da yake riga da siket ne na atampha holland kuma dinki ya amsheta sossae da yake atamphar ash ce da orange a jiki…
Zumbur Barister Shehu ya mike …ji yake kamar ya je ya rungumeta amma sam ba da shashanci yake son Sa’adah ba …so yake ya aureta ya adanata gidanshi …don yanzu sam shida maryam sae kallo gashi ya kasa tabuka abun kirki a kanta ….
Katse mashi tunani tayi ta hanyar hure mashi ido …kamshin mint din bakinta ya sashi lumshe ido ..ya koma ya zauna kamar wani sakarai…
“Damsel” …ya kira sunanta tare da zuba mata ido …
"Why ? ...me yasa kike wahalar dani ...2weeks bama waya wallahi kamar nayi hauka ....bak'ya tausayina Sa'adah....!!
.
Kallonshi tayi …a zahiri ya rame …amma wannan ba shine matsalarta ba
"Ayyah sorry baby ..na fada maka naje maiduguri gurin grandy ta da bata lafiya ..amma ai yanzu gani na dawo kuma ina gabanka ..meye na bata rai ...kaga bani phone dinka dear na tura maka pic dina kaima na tura naka yarda ko bama kusa da ka gansu zaka ji dadi ko .....ta karashe maganar tare da langwabe kai ...
Cikin sauri ya bata wayar yana murmushi tare da fada mata pin din.. …
Janshi ta dinga yi da fira ba tare da ya lura da abunda take ba …har sae da ta dauki abunda take so sannan ta tura mashi pic dinta guda biyu ….
.
Suna firan tana duba agogo …..
••°°••
Ihun da ta saki ne yasa daga Hanne har Uncle Mahmoud din shiga kitchen da sauri ….
Tana rike da hannu sae hawaye ke zuba a idonta ….da sauri ya rike hannun yana kallonta ….yar yankar da tayi karamace amma duk ta cika gidan da ihu..
Dan karamin tsoki Hanne tayi ta juya tana fadin “Kin daiji kunya wallahi ..kamar ba mace ba “…. Su hanne mata!!!
Uncle Mahmoud din ta kalla da idonta da har yanzu ke fitar da hawaye …shima ita yake kallo …sun fi minti 10 suna kallon juna wanda ke cike da sako kala kala ….ganin baya da niyar daina kalllonta ga jinin da ke kara tada mata hankali ya sata fara bugun kirjin shi a hankali alamun ya mata wani abu …
.
“Uncle please do som…!!!.bata karasa ba ya saka hannun a bakinshi yana tsotse hannun ido a lumshe ….
Bude ido tayi tana kallon kyakykyawar fuskarshi …zata iya rantsuwar tun da take bata taba ganin mutun mai kyau kamar Uncle dinta ba ….
A hankali ta janye hannunta a bakinshi ba tare da ta daina kallonshi ba …….
Idonshi na lumshe ya janyota jikinshi tare da zagayeta da hannu …!!
Idan har hakan zai saka uncle dinta jin dadi zata iya tsayuwa a hakan har Allah ya karbi Rayuwarta…..ta fada aranta bata san ya fito fili ba…
Ji ta yi ya sake da sauri tare da girgiza kai ….” Bana fatan Allah ya karbi rayuwarki a haka ba Hudah In Sha Allahu …..!!
Binshi tayi da kallo har ya bar kitchen din..sannan ta jingina da drawers din tare da lumshe ido …
••°°••
Sae da ta kwanta sannan ta bude wayarta …text din Barister Shehu ta gani kusa 6 …ko daya bata bude ba sae ma tabe baki da tayi sannan ta bude Imo dinta ….