A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hannunta da dungule tare da dagashi sama cikin jin dadi …

Number da tayi saving da Kwad’o tayi dialing thrgh video call…

Feedohm????
???????? A DALILIN YAYATA????????

           ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITER’S…

59 to 60

   Cikin Saa yana online ya dauka ...Rufe idonta tayi tana fadin 

“Uncle nayi fushi kuma baran bude idona ba sae kace man sorry …na canza phone da kyar na yi recalling numberka amma kai ko ka tuna dani haba uncle na …..oya kace man sorry sannan na kalleka .”..

Ta fada cikin wata irin murya tare da murmushi a fuskarta ...wanda ya dada fitowa da ainahin kyawunta ...

” double sorry pretty”..

Ya fada cikin sanyin murya ..duk da yana tunanin mistaken number tayi ba shi bane ...amma da yake ido ga mata sae yaga bara ya iya barin wannan pretty din ba ta wuceshi ...

Ta bude idon da sauri tare da waro ido wanda ta tabbata ko uncle tayi wa irinshi sae yafi minti talatin kafin yabude idonshi ya kura mata ido ..barewa wannan karen …wanda take tunanin ko jakka aka daurawa zani sae ya bita !!!!

Haka kuwa ya faru ..don baisan lokacin da ya rungume wayar ba ..sae alamun zanen shaddah da ta gani …

Dariya tayi mara sauti sannan ta datse kiran tare da aje wayar gefe guda …

Kasa hakura yayi ya kirata ..Tana jin alamun ana kiranta amma ta share wayar …sae da yayi mata missed call kusa 5 bata dauka ba …

Imo din ta koma ta tura mashi text   

“am sorry mistake din number nayi..a digit din karshe instead nasa 6 sae nasa 9 “

kafin ta fira har ya fara typing …

Nasan prety …amma babu ta inda Allah baya hada mutane !!!

“Ashe kunsa Allah ? …ta fada a fili sannan ta maida mashi da “

Ok”…

Kiranta yayi a video call …har sae da ta kusa tsinkewa sannan ta dauka

ba kunya ya tasa karamar yarinyar cikinshi gaba yana mata sabbatu . ….

Kallonshi kawae take tana murmushi kafin tace ..

“kayi hakuri na fada mata mistaken number nayi please…!!

At long last ma cewa yayi ta bashi adress din garin da take da gidansu …

” ba bukata “…ta fada a hankali ..”domin gaskia kai saan ubana ne kaga bara ya yiyu nayi soyayya da kai ba !!!

“So baya tsufa pretty” ….ya fada cikin sauri …
.
Datse wayarta tayi gaba daya sannan ta kashe …..

Dad din shehu kuwa cigaba yayi da kiranta amma yaji ta rufe …daran ranar kasa bacci yayi …bai taba haduwa da yarinyar da ta tafi da imanin shi ba irin yau ….

tana bude wayarta kamar rige kiran dad din Shehu na shigowa ..yana katsewa na shehun na shigowa …bata dauki ko daya ba ta shige tayo wanka …dama tun da daddare mama ta ce da safe Mahmoud ya kawota zata tayata zama saboda Abba zaiyi tafiya ….

Bayan ta shirya suka shiga mota ita da Uncle Mahmoud ..

Sun dauki hanya sossae ba wanda ya tankawa wani tsakani …sae dae lokaci lokaci suna kallon juna …shiru ya mata yawa gani take kamar baya lafiyane …tana so ta tambayeshi meke damunshi amma ta kasa …da ky’ar ta bude baki tace ..

“Uncle baka lafiyane ? …tana kallonshi …

juyowa yayi a wahale yana kallonta ..wani murmushi ta sake mashi da ya sashi ta taka birki da sauri ya kauce hanya …

tsoranta da tayi yasa ta fada jikinshi tare da zagaye hannunta jikinshi …sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya zagaya da hannunshi bayanshi ya riko hannuwanta tare da zameta jikinshi yana kallon idonta …

Bata fuska yayi ..”Kin san me kikayi kuwa? ..

Feedohm????
???????? A DALILIN YAYATA????????

              ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..

61 to 62

    "Uncle me nayi "...ta fada hade da fito ido waje ....yarda tayi tunani haka ta faru ..domin lumshe ido yayi na tsawon mintina ...

“Da kin kashemu da kin huta”,….ya fada still idonshi a rufe …

Rufe bakinta tayi tana fadin .”Uncle daga murmushi …

Harara ya sake mata …ta kwashe da dariya …ita kanta yarda take dariyan so yake ya zame mashi matsala …

Tada motar yayi yana fadin "please Hudallah".. ...sauran maganar ya makale a makoshi ....

Dariyan ta cigaba dayi cikin salo tana kallonshi tare da fadin …”Uncle …!!! Tare da Jan sunan

Motar ya kashe ba tare da ya kalleta ba ya fita …napep ya tsayar ya zagayo ya bude mata kofar …

1k ya daura mata saman cinyarta yana fadin …”zo ki wuce Hudah mun hadu acan please ” …

“Uncle ..”..ta fada a shagwabe …

"Please Hudah .!!..ya hade hannayenshi guri guda yana Nuna mata napep

Ba haushi ya bata ba …sae dariyar da ta masa ta hau napep din tana waigeshi …sae da sukayi nisa sannan ya tada motar ya tafi gidan shima

Sae da ya rigasu zuwa gidansu…yana zaune falo ta shigo tana kwalawa Maman kira …

Harara ta sake mashi sannan ta zauna still tana kwalawa mamanshi kira …

mama ta fito tana fadin. “”Wannan kira haka Huda sae ko fasawa mutun kunne “

“Mama na gajine mai napep din da ya kawoni zagaye yayi Dani” ..ta fada tana kallon Uncle din Wanda shima tunda ta zauna ita yake kallo ..

“Yo garin ya ? …ba tare dakuka taho dashi ba …!!

“Mama tambayarshi dae… har fa mun taho daga na mashi dariya shine ya saukeni ya tare man napep yace na taho …!!

Mikewa yayi ya shige ciki ba tare da yace komae ba …mama kuwa dariya ta masu ..sannan Hudah ta mike suka shige ciki …

  ••°°••

Kwanaki na kara ja….soyayya sossae ake tsakanin Hudah da Shehu da kuma dad dinshi …

duk sun dauki son duniya sun daura mata …Dad address din gidansu wata kawarta ta bashi …duk lokacin da yace zaya to sae ta shirya ta tafi ….

Lokaci guda ta gama rikitasu ….Barister Shehu yace mata yana so suyi aure a wannan shekaran …

Ce mashi tayi “bara ta iya auren mai mata ba Wallahi sae dae idan zai saki matanshi sannan zata yarda ta aureshi ..!!.

Kamar ta mashi asiri yace ya yarda zai saki maryam din yau ….Ita dae bata ce mashi komae ba sae murmushin da ta mashi …

Ranar da ya saki maryam din ranar yazo gidansu lubna gurinta ....

Da kyar dama uncle Mahmoud ya barta ….bayan sun gama firansu ne ta rakoshi ….ko a wajen janta yake da fira sam idan yana tare da Sa’adah baya so ya rabu da ita ….murmushi kawae take mai cike da ma’anoni daban daban ….Karar motar Uncle Mahmoud taji ta juya da sauri tana kallonshi …Ji tayi numfashinta na Neman barin jikinta ..da kyar ta tsaida natsuwarta guri guda…..

Kallon kallo suke su duka ukun ….wanda barister shehu yafi maida hankalinshi ga Barister Mahmoud …Hudah kuwa dukar da kai tayi kasa

FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????

                 ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…

63 to 64

Ba tare da yace komae ba ya figi motar ya koma cikin gida kamar zaya tashi sama

Barister shehu ya saki ajiyar zuciya yana fadin …

“Kin san wancan ne Sa’adah ? …

Girgiza mashi kai tayi tana murmushin yake .. “

“kai ka sanshi ne ? …ta tambaya tare da kura mashi ido

" Yeah ...da gurin aikin mu daya ..Don shine ma babban mu ..but yanzu ya bar gurin aikin for morethan 5years ban san inda ya koma ba ...amma naga yana maki wani kallo ...ko ya kyasa ne ...?

Murmushi tayi ba tare da tace komae ba …

” Kwalelenshi …Sa’adah sae Shehu,! …Ya fada yana murmushi …

“Jiya munyi magana da dad …yace zaa turo gidanku …!!

Ba tare da tace mashi komae ba sae juyawa da tayi tana daga mashi hannu ….

Dakin Lubna ta fada tare da fashewa da kuka …

“Damsel menene ? …wani abu ya maki …ko cewa yayi baya sonki ….please kiyi magana mana !!! ..ta fada a rude tare da rike kafadarta …

“Uncle Lubna …Uncle ya ganni da mutumin da ya fi tsana a duniya ….!!! ..ta fada cikin kuka …

" Ina ya sanshi Damsel ? ...ya akai kika san baya kaunarshi ...? ..shin uncle din ya maki magana ne ? ...


"I know everything a tsakaninsu lubna ...wanda shi kanshi uncle din bai san na sani ba ...!!!

"Kinga damsel kije kiyi magana da Uncle din mana ...may be ma shi bai dauka da wata manufa ba ....!!

Ba tare da tace komae ba ta dauki zunbulelen Hijab dinta ta saka sannan ta fita cikin sanyin jiki …yarda taga yayi parking din motar sae da gabanta ya fadi ….

Tana shiga falon ta iskeni tsaye hanne na tsugunne sae uban bala’i yake mata …..fuskarnan tashi jawur kamar an saka mashi ruwan zafi . …

bai bari ta shigo sossae ba ya shakareta tare da wurga ta saman kujera …kafarshi yasa ya take mata ciki …Uban ihu ta sake tana hawaye …

“Kinsan Uban waye kike tare dashi !!! …ya fada cikin tsawa …

 ihu ta sake ta kasa magana saboda wuyanta da ya shake ...hanne ta taho tana rikeshi tare da kuka  ..

“Dan Allah ka barta ” …kar ka kashe masu yarinya ” …haba ya….Wani uban mari ya sake mata tare da hankadata gefe guda …!!

“Bansan baki da hankali ba sae Yau Hudah …kin san da uban wakike tare …fada man tun yaushe kike soyayya da wannan banzan ….!!

Batace komae ba sae uban kukan ta take mashi …..dukanta ya fara yi yana tambayarta …amma bata masa magana ba …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button