A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ganin kamar kara haukacewa yake yana sabbatu ya sata kokarin kwatar kanka ….fa kyar ta mike daga inda take ….da gudu ta ruga zata shige daki …kafa ya saka ya tadiyeta ta fadi kasa da karfi …bakinta ya fara fitar da jini …still fizgarta yayi da karfi ta mike tsaye ya hadeta da karfi …Hanne kuwa Kuka take iya ranta …gani take kamar yazauce ….

“Wane irin so kake mata Yaya …wanda yasa zaka iya kasheta don ta tsaya da wani namiji ? …Hanne ta fada tare da rike mashi hannu tana kuka …

ita da Hudah ya hade guri Guda ….Kamar garwashi haka Hudah ke ji a ranta …barata iya daukar wannan dukan ba anymore ….bata san tana da karfi ba sae yau ….Hannun Uncle Mahmoud din ta rike tana kallonshi tare da angazashi baya da karfi …

“ka daina Uncle !!! ….ta fada cikin tsawa …tuni idonta ya bar zubar da kwalla ya bushe tare da sauya kala …

Yarda tayi tsawar ya sakashi kallonta shima …

“Ka dauka ban san Waye Barister Shehu ba ? …to na sanshi …sanin da shi kanshi wawan bai wa kanshi ba …ko ka dauka soyayya nake dashi …!!! …ta kareshe maganar cikin tsawa …

 Daga Uncle Mahmoud din har Hanne tsayawa sukayi suna kallonta ...

“Mutumin da yayi sanadiyar rabani da Mahaifiyata ya rabani da yaya sa’ata …a tunaninka shi zan so uncle ? …Juyar da kanta tayi ga barin kallonshi . …”ya ma yayata Fyad’e ..mukaje gidan Ubanshi yace ya sake mata idan yaso….a gaba suka wulakanta ta …Anan Mamarmu ta rasu tsakar titi Uncle …yaya Sa’a ta samu cutar HIV..shin kasan wacece yaya sa’atah? ..sannan kake tunanin ya ci bulus Kenan ? .. A DALILIN YAYATA na ke tare dashi …hakan yasa na rasa Mamata …Uncle shine ya kawo mana dukiyarmu ta gado sannan ya biyo dare da yan fashi suka sace Harda kai ciki Uncle!! …..ta fada tare da nunoshi da karfi….

FEEDOHM????

???????? A DALILIN YAYATA????????

                ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..

65 to 66

     Baya yayi tare da fadawa saman kujera yana kallonta  ...

"Hudah ...!!... ya fada a firgice ..

“Quite Uncle !!! …..ko zan manta idon kowa baran mata idon mutumin da na fada jikinshi ba lokacin da Shehu ke kokarin dauki jikkar kudin … .Da zoben dake hannunka na kara tabbatarwa lokacin da kazo gidanmu da safe Uncle ..idan har zaka lura har zoben na taba lokacin da ka daura hannunka saman jikina..!!! …

Har inda yake ta tako tare da dukawa kasan kujeran hannunta saka ta dago hannunshi ta zare zoben dake jikinshi tare da sakawa cikin dusbin ….sannan ta dago fuskarshi …

“Uncle aka pictures kadae ? …ka shiga gidan marayu? …haba Uncle …na sani kana son Abbanka amma Uncle bai kamata kaso naka ka tarwatsa wasu ba …kowa Uncle idan shi aka ma haka na tabbata hakan zai aikata ..Uncle na goge pictures din duka….!! ..Nagode sossae Uncle har yanzu baka canza ba a raina !!!

“Hudallah” ….ya fada ahankali …

Hannunta ta daura saman lips dinshi tare da mikewa taja Hannun Hanne da tayi mutuwar tsaye tana kallonsu ….

••°°••

Soyayya kuma da mutanen bata fasa ba …sae dae bata kara yarda wani yazo gurinta ba cikinsu ….

Kusan kwana uku bata ganshi ba .. .. tana so taje taga ko lafiya amma tana kunyarshi. . yarda ta dinga mashi tsawa ranar da abun ya faru sae take ganin kamar bata mashi halacci ba …

A hankali ta dan kalli Hanne dake cin abincinta hankali kwance…..

“Aunty Hanne wae Uncle baya garin ne ko baya lafiya ? …ta fada tare da dan goge hawayen da suka zubo mata da bayan hannu…

Ta dade tana kallonta kafin ta girgiza kai tace ..

"amma dae Hudah baki da zuciya mutumin da ya dakeki kamar jaka shine kike tambayarshi ...cab wallahi ni ko magana bana mashi ..."

Aunty baki san waye Uncle ba ko?.. …ta tambayeta tana kallonta …”Dan Allah ki yafe mashi kinji!!!

“Ke ai kin sanshi.. sakara mara zuciya anan falon ya gama cin ubanmu amma dan kina banza shine zakice na yafe mashi…” …ta mike tare da shigewa daki abunta …

Ita kam bara ta iya fushi da Uncle dinta ba..kwana biyun nan ma da bata ganshi ba Allah kadae yasan yarda take ji …Uncle dinta ya riga ya zama wani sirri azuciyarta wanda ba kowa ne zai fahimta ba .. …

mikewa tayi ta nufi dakinshi tare da turawa a hankali dauke da sallama.....

Zaune yake ya hade kai da guiwa …kneeldown tayi kusa dashi tare da dafa kafarshi da hannunta …

Ko bai dago ba kamshinta ya sanar dashi wacece …

“Uncle “…ta kira sunanshi a hankali ..

Dagowa yayi yana kallonta ….da alama kuka yayi yarda idanuwanshi suka canza kala …itama kukan ke niyar kwace mata …

“Uncle me ke damunka ? ..ta fada a hankali ..

“Am sorry Hudah …dan Allah ki yafe m”…

saurin toshe mashi baki tayi da hannunta tana girgiza mashi kai ....

“Dan Allah ka bar fadin haka uncle..wallahi baka da wani bashin yafiya da kake bani ..ni ce nake dauke da bashin alkhairinka a tare dani …!!!

 "Tashi muje Uncle ..please kawae ka biyoni Uncle am assure baka ci komae ba Uncle..!! ...hannunshi taja ba tare da ta jira abunda zai ce ba ...

FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????

               ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…

67 to 68

Kitchen ta ja tana fadin "uncle zaune..!!

“Me zan dafa maka uncle ?

Shiru ya mata yana kallonta …”Zakaci indomie ko, Na dafa maka irish da sauce? …

Shiru ya mata …juya idanunta tayi tana turo baki ..”Uncle su kadae na iya fa !!

  Dan murmushi ya mata ba tare da yace komae ba ...

Attarugu da Albasa ta mika mashi tace yayi mata grinding dinsu ….irish ta dafa sannan ta hada mashi sauce da taji albasa da kifi busasshe sae kwai ….

Lallabashi take tana so ya saki jiki da ita kamar da …bayan ya gama ci ta hada mashi ruwan wanka sannan ta fita ta barshi …

••°°••

Tana ganin ya tafi office ta cewa Hanne zata je ta dawo ….general hospital ta nufa …direct dakin da masu karbar maganin HIV ta nufa …duk da baa barin marasa cutar su shiga da yake sirri ce …sae da ta ba masu tsoron gurin 20k suka barta ta shiga ta zauna tana kallon yan matan dake zuwa karbar maganin …

 Da sauri ta bi bayan wata yar kyakykyawa bayan ta fita daga gurin ..sallama ta mata ta amsa tare da juyowa sukayi musayar murmushi ...

“Mu dan samu guri mu zauna please muyi wata magana !!! …huda ta fada dauke da fara’a..

Cikin asibitin suka koma suka samu wani guri safe da babu koma suka zauna bisa fararen kujeru ...

“Wani aiki nake so kiyi man sister please” …huda ta fada tare da kamo hannunta …

“Wane irin aiki yar’uwa? …itama ta fada dauke da murmushi …

" Ina so kiyi sex da wani mutumi ...please !!...ta fada a hankali ..

Da sauri budurwa ta kalleta …zatayi magana hudah tace “please zan biyaki ko nawa ne ” ..

Idanuwan budurwa suka kawo ruwa …tace “me yasa Yar’uwa .. kema sun tabaki ne ? …

Hudah tace “Sun man babban tabone”….idanuwanta suka ciko da kwalllah ..

Sauke ajiyar zuciya tayi …”Zan maki ko ba kudi sister …kin ganni nan wallahi yanzu banki ace duka lalatattun maza suna dauke da cutar da nake tare da ita ba ..kadan cikinsu ne na kirki …Ina da saurayi har an sa mana rana dashi ..ana gab da bikinmu don har sadaki yakawo ..yace na rakashi unguwa …wani gida ya kaini yace ai yanzu na riga na zama matarshi tunda har an bada sadaki …ya yaudareni sossae har yayi amfani dani …wallahi tundaga lokacin bai kuma zuwa gidanmu ba …ashe yana dauke da cutar ..shine asalin lika man ita”..

Murmushi Huda tayi tare da fito da wayarta ta fara kiran number dad din shehu …rejecting yayi ya kirata …

"Please kana ina ..?

“Ina nan Guest House dina lafiya Prety? …

“Zamuyi discussing wani serious issue ne yanzu …”

"To bara bazo gida na sameki yanzu ..just ki bani 5mints ganinan zuwa Pretty" ....ya fada cikin sauri 

“No bani adress din nima na fito ina hanya man ..”..

“Ok pretty …Sardauna estate No 6 dandume road ….'”

katse wayar tayi tana kallon budurwar …

“Hudallah Ibrahim” ..ke fa ?

" Shafa'atu kabir" ....ta fada dauke da fara'a ...

“Please kinsan maganin da zaiyi raising fellings din mutun lokaci guda ?

Shafa’atun ta bude jikarta ta fito da wani abu ta mika mata ..”Kinga wani nan nima banishi akayi na kaiwa hajiyarmu ..gashi ” …ta mikawa Hudahn ..

Dae dae kofar gidan suka tsaya ta kirashi tare da fadin Sun iso …

Fitowa yayi da babbar riga da alamun ko dogon wando babu ciki …

Suna Shiga suka zazzauna ya bude fridge tare da fito masu da fresh milk ya zuba masu a cup ya mika masu ..

“Prety wannan special visit haka ? …bakuwa barka da zuwa . .!!.

FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button