A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ko baa fada mashi ba ya san abunda takewa ihun ….duk da ta bashi tausayi amma dariya yake mata ….bai ga wanda ya sakata ba kilbibi ne irin nata …..

Cikin kuluwa da dariyar da yake mata ta juyo tana hararanshi tare da watsa mashi ruwan sanyin da ke cikin bucket ….

“Ba komae kije da zafinki …..see ..naga wani abu irin wannan a gurin wata mata idan na fita zan sayo maki sae ki kara sakawa ..tunda naga kin girma da yawa ….!!! …ya fada yana dariya …

Da sauri ta juya ta hade kanta da bango cike da kunya …ga azabar take ji …Allah ya isa kuwa ta jawa Lubna yafi cikin kwando …..

Kamar yarda barister shehu ya fada …haka ta faru …gidan da suke ciki ya sayar a tunaninshi nan da shekara daya idan ya samu ya maida masu gidansu …da marece ya kawo mata kudin ….ba tare da sanin kowa ba ta rabasu uku …kashi daya ta kai gidan marayu akan Allah ya kai ladar kabarin Yaya Saa ….sannan gudan ne ta kaiwa Aunty hanne tace ta boye mata ….sauran gudan kuwa …babban masallacin garin ta kai tace a gyara shi sannan a sayi duk abunda zaa bukata ….ta sadaukarwa Yaya sa’a da mamanta sae babanta .
..

••°°••

Barister Shehu ne ke fada mata dad dinshi baya lafiya …45%t fever …ga diarrhea sossae ……”Allah ya sawake ta fada .”…!!

°°••°°

FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????

                ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS….

72 to 73

Tun daga ranar da uncle ya kamata tana matsi bata kuma bari suka hada ido ba …tana kwance tana chat dinta …ya shigo tare da tsaya bakin kofar ya zuba mata ido …rigar dake jikinta cottonsilk orange ta bi mata jiki sannan iyakarta guiwa ….cinyoyinta sun fito kamar irin na turawan nan ..sae gashinta data hade shi ta daure baya ….

Bude hanci take tana shakar kamshin uncle a tunanunta daga dakinshi kamshi ke fitowa …

Pictures dinshi ta nuno tare da rungume wayar tana fadin…” I miss you uncle …matsalanka ka fiye gano abunda yafi karfinka …

Wa yace yafi karfina ....? 

Da sauri ta juyo tana waro ido kafin ta boye kanta cikin pillow ….

dan murmushi yayi kasa kasa yace ..”ki tashi ki shirya zaki rakani unguwa “..

ba tare da ya jira amsarta ba ya wuce abunshi ….dakin hanne ya shiga yace ta shirya zasu tafi ….wata uwar harara ta watsa mashi don tun dukan da ya masu over 6month take rike dashi ….

“Bana zuwa ” …ta fada tare da gyara kwanciyarta ….

Ba tare da yace komae ba ya juya …amma a zahirin gaskia baya kaunar mutun mai riko ..
wacce yama dukan ma ita da kanta ta nemeshi tare da ba shi hakuri duk da shi ya dace ya bata din ….

Dan karamin tsoki ya sake dae dae lokacin da Hudah ta fito daga dakinta sanye da gown red ….

a tunaninta da ita yake tayi saurin kallonshi tana fadin …”Uncle sorry wallahi gyalen na rasa inda yake “…

Dan murmushi yayi yace “Baki man komae ba Hudah ….kinyi kyau sossae ….amma bara ki fita a haka ba ….”

 komawa yayi dakin ...cikin kayanta ya dauko mata bakar hijab  mai hannu tare da mika mata ta sanya tana murmushi ....

A mota ma duk sec sae sun kalli juna tare da sake murmushi …

“Zaki zauna da Auntyn kine koko kinfi so na ajeki GRA ke kadae” …ya fada tare da dan kallonta …

Shiru ta masa ba tare da tace komae ba …juyowa yayi yana kallonta yaga gaba daya hankalinta ba ga motocin dake kokarin wucesu ….hannunta ya janyo tare da kura mata ido ….

“Bakya jine “…..ya fada dae dae kunnenta …

“Me kace Uncle ? ….ta fada tare da zame hannunta daga nashi …

Kafarda ya janyo yana kokarin rungumeta ..”may be idan kina jikina kya fi fahimtar abunda nake fada ….”

“Wallahi uncle naji ..ka sakeni please !!..

Hararanta yayi sannan yace ..”bana jin kinji abunda na fada tunda baki bani amsa ba !! …ya fada tare da kokarin hade bakinta …

cikin sauri tace ..” Uncle please ka daena ….da Aunty hanne zan zauna “…ta fada tana kallonshi da idanuwanta ta suka koma kalar kuka …

Dariya yayi kasa kasa tare da sakinta yana kallonta …turo baki tayi tana fadin …
“Saukeni na tafi a napep ni dae !!

"A da kenan Hudah lokacin da nake tsoron na tabaki ba yanzu ba da kika zama tawa ...kina iya yin duk kalar abunda kika so ..am ready na bi da ke yarda kike so ...duk da dama kin shirya don har ...!!.

Hannunta ta sa abakinshi tayi rau rau da ido ..”

“.Uncle Dan Allah kabar fada …wallahi lubna ta bani ….!!

wani fitinannen kallo ya watsa mata tayi saurin maida kanta kasa tare da zame hannunta daga bakinshi …

Central market ya nufa da ita …wani katon shago suka shiga ….Wasu kayane gefe guda …gurin suka nufa …

“Ki duba abun da bai maki ba …gobe zai koma dubai din sae ya sako maki wasu …” ..ya fada yana kokarin daga mata kayan

Wani fitinannen kallo ta sake mashi tare da juyawa ta fita daga shagon ta koma mota ta zauna ….

Kallonshi tayi cikin natsuwa lokacin da yake kokarin kunna motar tace

“Uncle idan zaka hada man lefe har sae kazo dani na gani …? ..Uncle zan iya aurenka ko babu lefe kuma na rayu dakai kamar baiwa..Ka mani komai a rayuwata uncle bansan dame zan saka maka ba …!!

So yake ya kashe maganar yace “Lubna ta cigaba da baki abunda take baki ke kuma …!!

Kuka ta sake da karfi tana kokarin bude motar ta fita …hannunta ya rike yana dariya …ita kuma sae neman kwacewa take …

“Sorry Hudallah na daina kinji ko !! …ya fada dae dae kunnenta …

Kallonshi tayi tana turo baki …sannan tace “promise” …a hankali …

Lumshe idonshi yayi tare da daga mata kai ……kafin ya budesu tar ya zuba mata cikin salon soyayya …juyar da kai tayi tana kallon waje dauke da murmushi …

FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????

               ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..

74 to 75

3 month …

Shirye shiryen biki ake sossae ..hanne ta zage sae gyara Hudah dun bata mata kallon kishiya sae yar ‘uwa duk da akwae dan kishin kadan a ranta ..amma ta tabbata idan har ta fiyo dashi to batawa Mahmoud adalci ba …tun da har ya jure zama da ita tsawon shekaru ba tare da cin mutunci ba…

“Aunty Hanne Dan Allah bara naje na dawo …Lubna tashi muje !!!!

Hanne tace ..”.ina zaki Hudah ..so kike mutane su zargeni …duka gobe fa daurin aurenki kuma zaki fita …aa gaskia !!

Hudah ta riko da hannunta …”Please aunty hanne…wallahi daga yau baran sake irin wannan fitar ba …dan Allah ….kinji auntyna …!.

" To Hudah ...ki kula amma kinji ko !!!

“Yauwa” ….ta fizgi hannun Lubna suka fice ….Motar Mahmoud din suka shiga …

"Ina za mujene ? ...lubna ta tambayeta ...

Hararanta tayi ..Gidansu Shehu …!

“Amma Damsel baki da imani ..bayan kinki aureshi kuma har da zuwa gidansu ki masa me ….?

Bata ce mata komar ba tayi parking kofar gidan …tare da fito da wayarta ta kira Shehun …ta tambayeshi “yana gida ..”.ce mata yayi. ” eh yanzu ya dawo shi da dad asibiti suka karbo magani …”

Lubna ta kalli ..”fito muje” …ta fada tare da yin gaba abunta…

Ba tare da tayi sallama ba ta hankade labulen falon ….cikin saa su duka ukun na zaune sae safina dake gefe guda tana wasa …

Zumbur Dad da shehu suka mike ….Dad yace …”Pretty”…kafin ya rufe baki Shehu yace “Sa’adah “,….sannan suka kalli juna tare ….

Yar dariya ta sake ..kafin tace ..

“Sa’adah ..damsel Pretty.. ..amma asalin sunan Hudallah Ibrahim _!!! …

“Hudallah .”.su duka duka maimata har da hajiya data mike lokacin ..

“Kwarae amma ba farat daya karamar kwalwarku zata fahimta ba …Soyayya ……da uba da dansa ….!!

” Damsel ..”.barister shehu ya fada tare da matsowa kusa da ita …”Ban fahimceki ba …”

"Yanzu kam zan maka yarda zaka fahimta dakai da jakin ubanka har da ma tunkiyar uwarka ...!!

“Ke mara mutunci ….uban me kike nufi ? ..hajiya ta matso a fusace …

Dad da yayi mutuwar tsaye yace ..”.karki kuma zaginta hajiya …dan Allah Pretty ki zauna muyi magana …wallahi har yanzu ina mutuwar sonki .!!…ya fada cikin kyarma ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button