A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shehu yace …”Dad Sa’adah tawace kabar fadin haka mana …ka lallasheta kar tace bata sona dan Allah …!!

“Ashe kun san Allah ….? ..Yaushe kuka sanshi ..ku fada man …!! …ta karashe maganar cikik tsawa …

" A gaida jakin malamin da ya tsaya fadarwa Shehu da ubansa fadin suna  Allah a baki don basu sanshi a zuciya ba ....!!

 " Sa'adah "....shehu ya fada tare da yin kneel down a gabanta ..."Dan Allah karki man Haka wallahi ina mutuwar kaunarki ...na tabbata idan ban sameki mutawa zanyi ...!!

"Aiko ya kamata uwarka ta tafi neman likafani tun yanzu ....!!

Lubna tace …”haba Hudah karki yi haka ba …karki zama mara imani …komae suka maki bai kamata kiyi haka ba …..!!

Cikin tsawa tace …”Kinsan Wacece Yaya Sa’a ? ….

Ba Shehu kadae ba Hatta Lubna sae da ta tsorata ….

 "Yaya Sa'a ...tana iya kwana biyu bata ci abinci ba amma bata taba barin Hudarta da yunwa ko da seconds 2 ....takan kwana tana wahala duk saboda Farincikin Hudah ....Wadannan munafukan Lubna su sukayi sanadin barata da duniya ke har da ummana .... _*A DALILIN YAYATA*_ Nayi komae lubna ba wae don kowa ba sannan nayi soyayya daku !!...


 "Shehu na tabbata baka manta wacece Ya ya Sa'adatu ba ...mumina saliha daka tarwatsa mata rayuwarta ....to Hudah ce kanwarta ...!! 

 "Wallahi nasan ban kyauta ba amma dan Allah ki gafarceni ...ki tsaya muyi magana wallahi na tuba na gyara duka halina  Hudah ...duk saboda ke ...dan Allah karki barni ...na tabbata dad zai bar manke ...,!!!

” Mtsee ….gobe kamar yanzu na zama matar barister Mahmoud mutumin da kukayi forcing yazo gidanmu ashe ma haske kuka kawo mana …!!

bata rufe baki ba ya fadi kasa yana tari …dad da hajiyar sukayi kanshi …dad ke fadin …

"Karkiyi haka Hudah ...na bar masa ke wallahi na hakura ...!!

Harara ta watsa mashi …

Tana fadin… …”Sweetheart ayi maza aje gwajin kanjamau don na tabbata akwaeta a jikinka …don ina tunanin har da jakar matarka ma ta kwasa …a lisaafina Yau 6month kenan da cutar ta shiga jikinka
na tabbata tayi kwarin da barata fita ba …..bye!!! ..ta juya ta tafi ..

Juyowa tayi da sauri tana fadin ..

“Oh na manta …Shehu ya sayar da wannan gidan akan Naira million 19..idan ya tashi ku tambayeshi ..wawan bai sani ba nina sayi gidan sannan ya maido man da kudin a matsayin kyauta …so nan da wata daya a tattara komatsae a fita!! ……

Ta fizgi hannun Lubna suka fita ….ita kam lubna binta take da kallon kamar tv …gani take kamar ba Hudah da ta sani bace ..

 Da daddare Uncle Mahmoud ya kaisu ita da Lubna da Farida kawarsu da tazo.. gidan liman ....

Bayan su Lubna sun fita daga motar ne ya riketa ….yana shafa kunshin da aka mata na zallah bakin lalle …

FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????

              ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…

 _GWS.....SWEERY ...ALLAH YASA ZAKKAR JIKINE .....PLEASE IDAN AN TARA KANKANA CIKIN KAYAN DUBIYA KI AKE MAN KIN JI KO .....????????_

76 to 78

    Kallonsa tayi a shagwabe tana fadin ...Uncle suna jirana please ...!!

Glass din gurinshi ya rage tare da kwalawa su lubna kira da suke gefe suna jiranta …

Suka matso Lubna na fadin “Uncle gani ” …

Lumshe ido yayi yana murza hannjnta …”Ku shiga ciki Lubna zamu shigo yanzu …”

“Uncle “….ta fada kamar zatayi kuka …

Kallon da ya bita dashi ya sata yin shiru tare da maida kanta kasa ….a hankali take mashi guguni tare da turo baki tana hararanshi ta kasa …

Idonshi na lumshe duk yana jin abunda take fada …bata tare da ta shirya ba ya rungumota kirjinsa tare da hade bakinsu guri guda yana tsotsa …

kokarin kwace kanta take tana yarfe hannu ...kin sakinta yayi ya cigaba da bata dpkiss ....sae ya ji ta fara kuka ne sannan ya saketa a wahale ...

“Maimaita abunda kikace !!…ya fada kasan makoshi..

kwallan daya fito ne ta saka bayan hannu tana gogewa tare da turo baki ta masa banza ….

A hankali ya bude ido yana kallonta sannan ya saka hannu da niyar rikota …tayi saurin ja da baya tana fadin ….

“Yi hakuri zan fada maka uncle” …ta fada tare da goge kwalla …

Maida kanshi yayi saman sitiyari yana jiranta …jin taki cewa komae yasashi dagowa .yana kallonta …..tayi saurin ja da baya ..

“Cewa nayi kamar baka taba aure ba !!!….ta fada a hankali …

“Umhuh …ina jinki ..sae kika ce mae…kuma bayan wannan?

” Shikenan fa abunda nace .”…ta fada tare da janye hannuta cikin nashi..

Dan murmushi yayi tare da rungumota yana niyar kissing dinta …

“Zan fada wallahi ……!!

sakinta yayi tare da zuba mata ido …..

A ha kali tace ..”sae kuma nace..huh…kayi hakuri Dan Allah Uncle” …ta fada tare da kallonshi ..

“May be dama kina bukatar na cigaba da kissing dinki shi yasa baki so ki fadi abunda na tambayeki .!!..ya dago fuskarta da hannunshi na dama ..

Da sauri tace ” aa wallahi uncle ..cewa nayi ka cika jaraba ….!!..ta karashe maganar tare da sanya kanta cikin cinyoyinta …

Murmushi yayi kasa kasa tare da bude motar ya fita ya zagaya ya bude mata …ba tare da ta kalleshi ba ta fito tare da rugawa cikin gidan da gudu …

Binta yayi da kallo tare da lumshe ido ya jingima da motar tsawon wani lokaci ….

Karfe 11:30

Dae dae lokacin aka daura auren Barister Mahmoud da Hudallah Ibrahim …wanda liman ya daura …tare da halattar dunbin mutane daga garuruwa da dama ….

Duk yarda barister Mahmoud yaso ayi party …liman hanawa yayi …yace …

“Indae kuna son aurenku yayi albarka Mahmoud to dole ku kauracewa duk wata bidi’a …ban hanaku idan an kai maka matarka ba …ku shirya walima cikin gidanku domin mutane su tayaku da Addu’a …!!

Godiya sossae Mahmoud yayi sannan ya tashi suka tafi ….

Bayan magrib ne …motocin da zasu dauki amarya suka iso …kanwar maman Mahmoud ne ta amso amarya an nadeta cikin Saree yellow colour tun daga kanta har kafarta …..

Rungumota tayi tare da sakata cikin Clinto yellow colour ..sannan ta rufeta ta koma cikin wata motar.. aka barta ita kadae ….

Duk da baa gaban iyayenta take ba …amma ranar mutuwarsu ta dawo mata sabowa…ta tabbata da yaya saa na raye babu abunda zai hanata zama gefenta a yanzu …tayi kwadayin taga farincikin da zata gani a idon yayar tata … ….

FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????

                    ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home pf expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..

79 to 80

  Wani sabon kuka ya zo mata  ..yayin da ta sa hannu tana kokarin rufe bakinta gudun kada drivern yaji ta ....

Ji tayi an janyota tare da kwantar da ita …kamshin da tajine ya hanata firgita don har ga Allah bata dauka akwae wani a cikin motar ba bayan driver …

A kan kirjinsa ya kwantar da ita tare da bubbuga bayanta a hankali alamun lallashi …ba tare da yace komae ba ….

Lafewa tayi tana kuka kasa kasa ….Hannunshi ya kai tare da lalubar bakinta ya tura yatsunshi a ciki yana wasa dasu a bakinta ….

Kukan ya tsaya cak sae dae ajiyar zuciya da take saki tare da kananan kwallah ……

Jin zaa bude motar ne ya sata tashi daga jikinshi tana gyara Saree dita ….

Bude motar akayi tare da fito ta …sannan Aunty hanne ta matso ta kama hannunta …Uncle Mahmoud dinne ya zagayo tare da rike gudan hannun nata ….

Pictures aka dinga dauka kala kala ….ga dandazon mutanen da sukazo taran amarya …Ba gidan barister Mahmoud din bane aka kaita …gidan iyayenshine ….zuwa gobe idan anyi walima su wuce gida ….

Tare suka jera su duka ukun har tsakiyar babban falon Gidan …sannan aka zaunar da Hudah din a kasan tuntu …Shima barister Mahmoud din zama yayi gefenta …har lokacin fuskarta na nannade da Saree ….

Falon ya dauki haske ta ko ‘ina ….yana zagaye da dangin Abba da kuma na mamanshi sae su biyu a tsakiya …

Yayar Mamanshi ce Aunty Husy ta taso tare da aje yan kunne da sakar gold wanda ya kai naira million 15 …kusa da Mahmoud …na sayan fuskar amarya …

Gurin ya dauki tafi ganin Mahmoud din ya tura mata sarkar yana girgiza kai …alamun bai sayar da fuskar Hudah haka ba …

Wata kanwar mamanshi Aunty Zuby ta taso tare da cire tata sarkar da yan kunne ta hada mashi ta tura …still tura masu yayi yana girgiza kai …alamun bai yarda ba …

Gurin ya kara daukar tafi lokacin da mamanshi ta taso ta cire tata sakar da yan kunne ta daura mashi a saman tasu …

Sannan ya saka hannu ya dafa sarkokin tare da fara bude Fuskar Hudah Ahankali ..har sae ya kusa budewa sannan ya kalli kanwar mamanshi yana fadin “Gaskia Aunty Zuby ku karo wani abu tukun …”

Aunty Husy ta mashi dakuwa tare da watsa mashi harara ..
Sannan ya bude fuskar duka yana murmushi …..

Kanta na a kasa tana kallon carpet din gurin ….

“Masha Allah …tubarakallah ..Alhamdulillah amarya ta hadu ta ko’ina ….fatan mu Allah ya bada Zaman lafiya!! ….Babbar yayar mamanshi ta fada tare da daukar su photo ….kamar an bude gidan photo haka flash light ke tashi gurin ….

Sae da aka gama photo sannan gurin ya sake yin shiru …Mahmoud dinne ya saka hannunshi na dama tare da dago fuskarta …sannan ya goga hancinsa a lips dinsa yana lumshe ido ….duk uwayen mutanen dake zagaye da falon..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button