A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Mahmoud baka da kunya ni wallahi ban ma san haka kake ba dae yau ..”..kanwar Mamanshi ta fada tare da jehoshi da pillow ….Hudah kuwa yarda kasan ta nutse gurin haka take ji ..
..
Murmushi yayi kasa kasa sannan kama hannun Hudah ..tare da rarrafawa kusa da kafar Mamanshi …
“Hudallah ki gaishe da Mama “…ya fada dae dae saitin fuskarta …
Dukawa tayi kusa da kafar maman ba tare da ta iya cewa komae ba …bayanta maman ta dafa ..tana fadin ..
“Allah ya maki Albarka Hudah ….!
Kowa na falon sae da suka rarrafa ya na rike da hannunta yana fada mata sunanshi tare da matsayinshi ….ita kuma tana dukar da kanta a hankali …suna sa mata albarka sannan suka dawo inda suke zaune …duk abunda ake idon hudah na kasa bata dago ta kalli kowa ba …..
Bayan sun zauna ne babbar yayar mamanshi _Aunty Husy_ ta kama hannunta tare da kaita part din hajiya ta zaunar da ita saman gado ta fita ....
kamar jira Mahmoud yake ta fita ya fado dakin tare da saka key kamar munafuki nidae feedohm nace munafuncinne man…ya zauna kusa da ita ya janyo ta jikinshi yana fadin …
“Hudah sun man bakinciki wae anan zaki kwana ….dan kada ace nayi rashi kunya wallahi dana saceki mun koma gida ko ? …
Banza ta mashi tare da sakin kuka ….kanta ya dago yana lallashinta tayi shiru amma sam taki yin shiru ….sae da ya fara kokarin cire mata Saree da aka lillibuta dashi sannan tayi shiru …
FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????
????
HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of Expert & Perfect Writers )
Na Feedohm????
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..
81 to 82
"Uncle ka fita dan Allah !!....ta fada tana kokarin tsayar da kuka ...
Cikin sauri yace ..”Idan na fita zaki bar kukan Hudah …?
Daga mashi kai tayi tare da sadda kanta kasa ….dan kiss ya mata a lips tare da jan hancinta sannan ya fita yana waigenta …..duk da yayan mamarshi tace anan zata kwana hakan bai hana Mahmoud ja mata Allah ya isa ba …
Allah ya soshi ba wanda ya ganshi lokacin sa yake fitowa don suna can suns kokarin hada mata abincin da zata ci wanda zai kara mata lafiya …
Su biyu suka shigo da abinci tare da zame malullubinta …Aunty Husy ce ta bata abincin a baki …tare da daura fuska …don farko cewa tayi bara taci ba …sae da ta daure mata fuska sannan ta amsa …
Bayan ta gama cin abunci yayar mamanshi ta hada mata ruwan wanka masu uban kamshi tace ta shiga tayi …tana fitowa ta bata less red tare da head baki tace ta sanya …da katuwar sakar gold …sannan ta saka mata takalma hills bakake …ta rufa mata bakin mayafi a kai ..tare da kama hannunta ..suka shiga part din Abbah …yana zaune sanye fa farin glass suna shigowa ya mike dauke da fara’a yana fadin …
"Marhaban Hudallah" ....hannunta Abbah ya karba daga hannun Aunty Husy ya zaunar da ita bisa tuntu ....
Aunty Husy ta miko mashi plate dauke da saubatussamina …….kadan ya diba a hannunshi sannan ya saka mata a baki…ta daukesu photo ….Fita tayi ta ta barsu su biyu ….
Wa’azi ya mata mai ratsa jiki wanda ta tattaba ko mahaifinta na nan iya abunda zai mata kenan …bata da abun ce masu shi da liman sae dae fatan Allah ya saka masu da alkhairi ..
12:30 ..
Masu decoration suka iso ….kujeru suka fara fitowa suna jerawa a harabar gidan …
.sannan suka fara decorating din da yadi blue da fari ….gurin yayi masifar kyau kamar baa cikin gida ba ….
Tana zaune Aunty hanne suka shigo ita da Aunty Husy suka bata Saree blue colour ….kaf jikinta sae da aka nannade idanuwanta kawai ake iya hanguwa …..
Fita da ita akayi falo …acan taji muryar Uncle Mahmoud yana mayarwa da abokan wasanshi magana …”wae duk family dinsu babu mai kyaun amaryarshi ……!!
Gabanta ya fadi lokacin da taji tattausan hannunshi cikin nata ….babu kunya ya daga Sareen yana kallon fuskarta tare da fadin ….
” Gaskia na iya zabe …Tubarakallah …Aunty Husy da an gama walimar zan tafi da matata.. ..ku dan rufe idonku for some minutes ….!!.
Aunty Husy ta kai masa duka ..”.Gidanku Mahmoud ….ka rike hannunta ku fita bawae ka ma rashi kunya ..!!..
Dariya yayi tare da kissing dinta a hannu sannan ya jata suka fita harabar gidan …
Sun nuna mata kauna sossae … kamar yarda exclusive suka kaunaci feedohm ….sabon lefe suka hada mata wae kayan karbar amarya ….
Agaban mutane ango ya ciyar da amaryarshi har ta koshi ….sannan aka ce itama ta ciyar dashi …kasawa tayi ..ta nuna alamun zata yi kuka …
Auntu Husy ce tace ta sayi hannun amarya naira million daya cash ta zubesu a table din da suke zaune …
Duk da hakan kasa bashi tayi …hannuta ya kamo ya kai bakinshi saitin fuskarta …
“Ba kya sona Hudah? …..ya fada a hankali …
Dagowa tayi da sauri tana kallonshi kafin ta girgiza mashi kai a hankali …hannuta ya kama ya debo abincin sannan ya saka a bakinshi yana lumshe ido ….gurin ya dauki tafi da ihu …abokan wasanshi kuwa cewa suke wae amaryar bata sonshi tunda har ta kasa bashi abinci …
A hankali ya dago da fuskarta yana kallon …”Prove it Hudah …ki nuna masu kina sona …ko bakya sona .?..
Ba tare da tace komae ba ta kai hannu ta debo Muhassimba ta kai bakinta ta b’alli kadan sannan ta sa mashi sauran a baki ….
Ba karamin burge mutane sukayi ba …Aunty hanne kam na can cikin gida bata san wainar da ke toyawa ba …Yayar Mamanshi ta bata yan shila tace ta gasa masu da ruwa ruwa idan zasu tafita a tafi da ita..dan haka bata gani ba.. bare ta kwashi takaici …..
••°°••
Bayan Magrib ne akace a fito da amarya ….sae da sukaje falon Abbah suka masa bankwna tare da Mama sannan Uncle Mahmoud din ya jata har harabar gidan inda aka ajiye motoci ….Daga ita sae Aunty Hanne da Aunty Husy kadae suka shiga motar …dan Aunty husy cewa tayi bara su shiga mota dashi da Amarya ba tunda baida kunya …..
Sae da aka fara tafiya sannan ya masu gyaran murya lokacin Aunty Husy tana karawa Hudah nasiha ..Hudah kuwa kuka take a hankali …
FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????
????
HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )
Na Feedohm????
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..
83 to 84
"Aunty Husy dan Allah ki barta hakanan ...kinga zaki ja ta bata kwalliyar tun kafin na gani ...kuma duk abunda kike fada mata Allah yau zan fada mata ba tare da tayi kuka ba " ....ya fada tare da kunna fitilar motar ...
Sake da baki aunty Husy ke kallonshi “∆mma Mahmoud baka da mutunci …ashe dan Ubanka sae da ka biyomu ….shine ka karbi driving din ko?….ya maka kyau!! ….
Dariya yayi kasa kasa tare da kallon Hudah da ta kwantar da kanta sanan cinyar Aunty Husy tayi lamo kamar maijin bacci…
Hanne ta saka hannu ta kashe filitan …ba tare da tace komae ba …har suka isa gidansu …sannan aka shigar da Amarya Part dinta …amma ba asalin wanda take ciki ba da …aa saman bene aka kaita …dama kuma gurin rufe yake …
Kamar yarda addini ya tsara bayan kowa ya watse ya tarasu falonshi tare da masu nasiha mai ratsa jiki …sannan yace kowa ta fadi bukatarta …
Aunty Hanne tace …Idan da hali ya taimaka masu da jari saboda ita tana so ta dinga fita kasashe tana dauko kaya … tasan ko ance ta koma karanta bara tayi abun kirki ba ….
Yacce ..”kamar nawa suke bukata ?
Hanne tace ” ko nawa yake da hali …”
Hudah kam jinsu take ..don bata da wani guri da ya wuce tayi karatu domin cika gurin Yaya Sa’arta !!
Leda da ya shigo dashi yace Hanne ta je ta dauko masu plate ..
Aa tace …yafi kyau suje can su ci abunsu kamar yarda akewa ko wace amarya …sannan ta mike ta daga Hudah tare da daukar basket din da ta shigo dasu suka nufi part din Hudah ….bawae bata jin kishi bane sae don ganin ko tayi kishin a banza tunda bata da abunda zata iya biya mashi bukatarshi ..
Part dinshi ya shiga …yayi sallah tare da wanka sannan ya shiga part din hanne ya mata bankwana tare da hugging dinta yana mata godiya …don ba karamin burgeshi tayi ba a hidimar bikin …bai tafi ba sae da ya dan bata farinciki ta hanyar romancing dinta sannan ya fita …. Ajiyar zuciya ta sake ta bishi da kallon ..wannan ne karo na farko da ya taba kai hannunshi a jikinta da niyar faranta mata..kwallah da suka taro idonta suka gangaro mata ….