A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsohuwar ta kwantar da murya …Haba Hudalliya ….na rantse maki da Allah da fatse ta dawo daga talla zan bashi ya kawo maki kudinki ..dan Allah karki sayar man da tunkiya ..

Ta juya baya tare da dage kitsonta tana fito keya …Nifa Innarsu Fatse dan karki ga na maki rashin kirki amma gaskia sae kin biyani kudina tukun na bada …

a ranta tace …rashin mutunci kuma har nawa Hudalliya…..amma a fili cewa tayi …iyakar mutunci kin man shi Hudalliya yanzu dae alfarma nake nema yar albarka …

Barister Mahmud dake kallonsu yana dariya har da rike ciki ya matso ya kama hannun Huda yana fadin …nawa ne kudin naki ..

Sarkin neman suna zaka biya mata ne …ta bashi amsa tare da mashi kuri da ido …..sannan tace …hala ba nan unguwar kake ba don ban taba ganinka waccen majalisar ba ta sa ido ….

Naira Ashirin ya fito ya mika mata yana fadin …karba ki sakar mata tunkiya …

Tsohuwar ta kalla tace …Allah ya soki da na maki rashin mutunci ..

Da dae taga an biya kudin sae cewa tayi
…..rashin mutunci har na wana shegiyarnan ……

Oho dae …huda ta fada tare da shigewa lungun ta janyo mata tunkiyarta ta koma ….

Barister Shehu ya kira ya fito daga cikin gidan suka shiga tare ….gabanshi ya mikawa Mamansu Huda duka dukiyarsu a cikin jikka sannan ya mika mata makullen suka tafi akan gobe zai dawo da masu gidan da zaa saya ..

da Suka fitone Mahmud ya mika mashi hannu cikin jin dadi da bai ci amanarsu ba sannan suka rabu …..

Wajen karfe goma na dare Wayar Barister mahmud ta fara kara …lokacin suna zaune da family dinsu suna dinner …ganin number barister Shehu ce ya saka ya dauka tare da sallama ….

Barister Shehu yace …Please ka sameni gurin gidansu wannan yarinyar akwae matsalane yanzu please ….

okey …ya fada tare da daukar keys ya fita da sauri ….yana isa lungun gidan yaga ba motar Shehu ya kira wayarshi ringing daya ya dauka sannan yace gashi nan ….da yake lokacin sanyine mutane duk sun shige gidajensu ….kofar gidan su Huda ya matsa ya zauna saman dakalin dake wajen ….

Kaya yaga an watso mashi a jiki ….yayi saurin mikewa tare da daga tsumman da aka jeho mashi ….bindiga ya gani a ciki nannade …da saurin ya daga cikin rashin fahimta ….ba dae wani abu akawa wadannan mutanen ba ..
ya fada da karfi tare da kara daga bingidar …..

Flashlight din da ta dinga haskashi tare da karar daukar hoto ya sakashi sakin bindigar kasa …..

Feedohm馃挒
馃挧馃挧 A DALILIN YAYATA..馃崄馃崄

            馃崄

HASKEN WRITERS ASSOCIATION馃挕

Na Feedohm馃挒

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…

7 to 8

    Weldon Barister ...ba dae kace zaka hanani aikata abunda nake so ba ....good gashi yanzu zaayi komae da kai ...

Barister Shehu ya fada lokacin da yake takowa kusa dashi …

Bai san lokacin da ya sauke mashi mari ba tare da shakarar wuyan rigashi …
wadanda suke tare sukayi saurin banbareshi tare da maida hannunshi baya suka rike …

Shehu ya sake dariyar mugunta yace ..

Kayi abunda kake so Barister ….zaka bimu gidan mu karbi abunda nake bukata sannan ka tafi ….ko kuma na watsa wadannan pictures din a duniya na rubuta bayan na kaiwa Marayu Hakkinsu …baristern duniya yaje da yan fashi sun karbe asirinsu ya tonu …kayi tunanin makomar baristoci sannan kayi tunanin mutuncin mahaifinka sannan da son da yake maka ….na tabbata daga rannar da ubanka ya sami wannan labarin bara ya kara motsi ba …kana sane da yana da hawan jini ….amma rufe wannan zancan shi zaya saka na goge wannan pictures din bayan wasu shekaru ….na lura kana so ka tuna man asiri …
don haka zabi ya rage naka …

Idanuwanshi suka ciko da kwallah ….tabbas indae har mahaifinshi yaga wannan labarin ya tabbata bakinciki zai zama ajalinsa …..ba tare da yace komae ba ya nuna kofar gidan da hannu …alamun su tafi …

Mask suka saka sannan Barister Shehu ya sakawa Mahmud suka shiga …..kauren an turoshi da alamun haka suke rufeshi dan an kangeshi da dutse ta ciki ……

Baka jin motsin komae sae kukan kaji dake tashi cikin ….suka kutsa kai suka shiga ciki …kamar rakumi da akala haka Barister Mahmud ke binsu …..

Barister shehu ne ya saka kafa ya naushi mamar dake bacci ….tayi firgigi ta mike tana tasbihi ….

Nan da nan ya canza murya yace ina kudin da aka kawo masu ….

Bamu da kudi Wallahi dan Allah kuyi hakuri ….ta fada tana hawaye .

Karyane shegiya ….wani ya fada da karfi ..

Kaine dae Shegen munafuki ….Huda dake bacci ta farka tare da bashi amsa ….ya kai mata uban duka da yake dama ba kaunarta yake ba ….

Ta sake uban kara tana fadin ….Allah ya isa shege mugu ….ka bugi Uwarka na kashi …….

Bata rufe baki ba ya kara daga hannu da niyar dukanta ….Saa ta rungumeta tana kuka tare da bashi hakuri ….

Mahmud dake tsaye kamar gunki ..yace …No………kayi abunda ya kawoka amma banda duka ….ya karashe maganar da karfi …

Gurin Uwar ya dawo yace….kina son ranki Hajiya ….ki fito man da kudin da aka kawo maki yau naira million goma da marece ko kuma na kasheki anan …

Wallahi hakkin marayune kuyi hakuri dan Allah ….ku barmu hakkinsu …ta fada cikin kuka …

Duka ya kai hannu zai mata saa ta rarrafo tare da rike mashi hannu tana kuka …Dan Allah karku dakar mana Umma wallahi inda kudine zan fito maku dashi …ku barmu dan San Allah …..

Karkashin gado ta leka ta janyo jikkar bakko….ta fitar da tsumman dake ciki sannan ta janyo masu jikkar ta aje gabansu tana kuka ….

Huda tayi tsalle tare da dira saman jikkar ta cire kallabinta ta daure a kugu tana kuka tana fadin ….Wallahi ko uwayenku zasu zo nan bara ku fita da jikkar nan ba ….

Barister Shehu ya hankadata gefe guda ta fada jikin mahmud ….rikeshi tayi gam tana fadin ….karku tafi da ita Dan Allah …da itane Mamana zata sakani Js One ….ku bar mana don Allah ….

Lumshe ido yayi ya banbareta daga jikinshi ya fita daga dakin da sauri ..

Motarsa ya fada ya cire Mask din dake fuskarshi ya jefar sannan ya data motar ya fita da ita daga lungun da gudu ….ko da ya koma gida Dad dinshi na zaune baki gate yana jiranshi …yana ganshi ya taso tare da rungumoshi yana fadin ….

Lafiya dae ko …..

Dauriya ya saka a ranshi ya sakar mashi murmushi yana fadin ….Alhmd dad ….me kake anan har yanzu ..

hannunshi ya kama yana fadin …taya hankali zai kwanta banga ka kwanta ba har 12 …..

Baice komae ba sae dae ya bishi da kallo suka shige ciki …sae da Dad din ya rakashi har part dinshi sannan ya dawo ya kwanta ….

Feedohm馃挒
馃挧馃挧 A DALILIN YAYATA…馃崄馃崄

                  馃崄

HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕

Na Feedohm馃挒

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…

9 to 10

  Tunda suka tafi mutanen gidan suka hade guri guda suna kuka ...mamarce ke karfin halin lallashinsu amma sam Huda taki shiru sae ma abunda yaci gaba .....bawae yawan kudin takewa kuka ba ...wae Mamarta ta mata alkwarin idan har aka samu kudi ta kaita Js one zata dinga bata naira Hamsin na break  to shi takewa kuka ....

Saa kadae ta fahimci abunda Huda kewa kuka …don sae da mama ta fita sallar asuba sannan ta rarrafa tare da kwanciya saman cinyar Saa tana fadin ….Yanzu Shikenan Yaya Saa tunda an dauke kudin mama bara ta dinga bani naira hamsin din da tace ba ta tara …..ta saka bayan hannu tare da share hawayen tana fadin …Allah ya isa ban yafe ba …kullun naira hamsin in kashe ashiri na saka talatin asusu ..don Allah nawa zan tara yaya Saa …

Saa tayi shiru tana jinjina rashin wayau na Huda …bawae kudin suka dameta ba …aa hamsin din da zaa bata takewa wannan ihun dama ….share mata hawayen tayi tana fadin …Allah zai kawo wasu Huda kinji ..

Karfe 9:30 na safe barister shehu yazo gidan karbar kudin wae zaa kaiwa wadanda zaa sayi gidan gurinsu ….

tunda ya fara magana …maman huda ke kuka har sae da ya dasa aya …..sannan ta fada mashi duk abunda ya faru …..

Salati ya fara yana dafe kai …..har da hawaye ..yana nuna yama fisu damuwa da dauke kudin da akayi …..don cewa yayi daga gidan police station ya nufa zai kai report dole a nemo wadanda suka sace kudin ……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button