A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hudah kam inda hanne ta barta nan ya isketa ....ko da ya shigo sae da ya kura mata ido ..duk da tana lullube da maroon din saree hakan bai hanashi ganin kyauwun da ta yi ba ....bakin gadon ya zauna tare da yaye mata fuska yana lumshe ido ...

” Tubarakallah …Masha Allah ..Alhamdulillah ya Allah ..”!!!.ya fada tare da dago fuskarta yana kallonta …kasa tayi da idonta har sae dae ya kai bakinshi yana gogawa a dukka fuskarta ….

“Tashi kiyo Alwala” …ya fada kasan makoshi …har lokacin bakinshi na saman fuskarta idonshi a lumshe …

Ganin bata da niyar tashi ya sashi daukarta cak ya dire ta cikin toilet din tare da zuba mata ruwa har ta gama alwala sannan ya janyo hannunta ya shinfida masu darduma ….ya gyara mata zaman saree din a jikinta ta yarda baka iya ganin komae a jikinta …sannan ya jasu sallah …bayan sun ida ..ya dafa kanta Kamar Yarda Allah ya umurce mu …ya dinga kwararo mata aduu’a sanna ya janyo basket din da hanne ta shigo dashi …ya fito da foodflask da waterdesndr ….tare da plate da spoon …

Yan shila ne da sukaji kayan yaji ya juye masu .sannan ya tsiya mata lemon da aka hada da kankana,gwanda,dabino da kwakwa ya tsiya a cup ya kafa mata a baki
.

Wani bala’in kunyarshi take ji…duk da ba wannan bane first time da ya bata abinci a baki ….kin karba tayi sae da ya daure fuska sannan taci kadan tace ta koshi ….

Ledar ya janyo ya juye mata kazar dake ciki yana fadin ..”Zauna kici kinji..bana so ki man irin na meenalle kice ban kawo maki kaza ba My Hudah!! ….dan hararanshi tayi sannan ta mike …

Shima mikewa yayi …yana kwance saree dake nannade jikinta …rike kafadarta yayi yana juyata har ya gama fitar da gyalen ya barta daga ita sae siket da wata yar rika wanda iyakar jibi da karamin hannu ….Sae kwalliyar stone dake jikin rigar ….

Wani asirtaccen kamshi ke fitowa daga jikinta …bai ga bukatar saka wasu kayan bacci ba …ya dauketa cak tare da direta saman gado …sannan ya koma ya kashe wutar dakin …

Cikin dubara har ya rabata da kayan dake jikinshi …anan ne ya kusa zaucewa har bai san sadda ya kunne fitila ba yana kare mata kallon …da sauri ta rugumeshi ganin haske ya gauraye dakin tana niyar kuka …

Da kyar ya iya kai hannu ya kashe fitilan yana mayar da numfashi ..cikin kunnenta yace ..

“Allah ya ma lubna Albarka …yanzu zan gane idan abunda take ba dawa yayi amfani..don bana son wannan rakin ya tafi a banza” …ya karashe maganar cikin zolaya ….wani uban duka ta kai mashi a kirji tare da ko ma wa can karshen gado ta kwanta ..

FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????

                ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..

85 to 86

  Mirginawa yayi ya hadeta da bangon yana fadin .."Sorry na daina kinji ko "...Sannan ya janyota jikinshi yana gentling ko'ina na jikinta  

••°°••

Barister shehu kuwa bayan sun kaishi asibiti aka tabbatar masu da barin jikinshi bara ya taba amfani ba paralysis …domin faduwar da yayi ga lokacin jininshi ya hau ….Hajiya da dad kuka suka sake …yayin da take tsinewa Hudah Albarka tare da ja mata alkaba’ai kala kala …

lokacin ne maganganun hudah suka fara mata yawo …cutar Kanjamau kawae take tunawa …Dad din ta kallah taga duk yayi yaushi ga kuraje da suka fara cika mashi jiki ….

Ba tare da tayi shawara dashi ba ta je laboratory tace su mata gwajin HIV ….jininta suka diba bayan mintuna suka tambar mata positive ce tana dauke da cutar ….

Kamar mahaukacya ta koma …ta shakari wuyan Dad tana dura mashi ashar …da kyar ya kwaci kansa …

Doctor yace shima a mashi gwajin …baa dauki lokaci ba aka tabbatar mashi da shima positive ne ….

Doctor din ya basu shawara da su rufawa kansu asiri su zauna tare ba tare da wani ya sani ba …sannan ya daura su kan magani ..

Bayan shehu ya farfado ..ya tabbatar masu da ya sayar da gidan da suke zaune …amma ba Hudah ya sayar mawa ba …wani makwabcin su Hudah ne amma ba mamaki ita ta turoshi .. ….

Dad din yace bai yarda ba wallahi zai shigar da ita kara …amma sae barister Shehu yace …babu wata kotu da zata karbi gidan daga hannun Hudah tun da “ka sayar ya rabaka da abunka” ..sannan takardun gidan ma na gurinsu ….Ba karamar nadama barister shehu yayi ba a ranar ….gashi a kwance rabin jiki a mace …sannan har lokacin akwai soyayyar Hudah a ranshi ….wanda ya tabbata bara ta taba gushewa ba ….

••°°••

A hankali ya kai fuskarshi tare da kissing lips dinta …sannan ya sake murmushi …bai taba tunanin rakin huda ya kai haka ba ….Ihu ta dinga mashi kamar ita kadaece macen aure a unguwar ….

Blanket ya ja mata ya mike ya fada toilet yayo wanka tare alwala ..
har sae da ya gama sallah sannan Hudah ta bude rinannun idonta tare da dallah mashi harara …

Murmushi ya sake mata tare da fadin …”Ni kike harara” …

Kafarta ta sauko zata mike tsaye ta koma da sauri…tana fadin …”Allah ya isa wallahi .Lubna..ban yafe ba ..kema zaki samu wanda zai maki irin hakan …Shegiya kawae !!! ..ta saka bayan hannu tare da share kwallah ..

Dariya sossae ta bashi …bafa Lubnar ta tsareta ba tace dole sae tayi amfani da abunda ta bata …aa itane har da boyewarta ma dan kar wani ya ganta ….amma kuma zata zagi yar baiwar Allah tana can gida tana bacci abunta…

Cikin zolaya yace ..”Wae Hudah me lubna ta maki tun jiya kike mata Allah ya isa ..? ..Gaskia ina neman mata gafara kinji …!!

Harara ta balla masa tana fadin “…Ban sani ba …ka shafa kaji …”..

Tasowa yayi yana dariya ..

“Abu mai sauki ..muje toilet idan na hada maki ruwan wanka sae na shafa da kyau naji ….!!

Daukarta yayi tana harbe harbe ya direta cikin ruwan zafi yana mata dariya ….sae sa ya tabbatar ruwan zafin sun ratsata sannan ya canza mata wasu ruwan zafin yace “Kiyi wankan tsarkk kinji Hudah …bara na gyara dakin kafin ki gama ko!! “…ya barota cikin ruwan tana lumshe ido..

Kusan Minti Talatin yana jiran ta fito amma shiru ko motsinta baya ji ….toilet din ya leka tare da sakin murmushi ganinta kwance cikin ruwan zafi tana bacci hankalinta kwance …..

FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????

               ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..

87 to 88

   Girgiza kai yayi ..sannan ya dauko katon towel ya nadeta ciki ya kwantar da ita saman gado tare da shafa mata cream kadan ....

Cikin kayanta ya dauko wata doguwar riga mara nauyi ya saka mata…sannan ya shafa mata powder …wasa wasa kwalliya ya mata sosaae tana baccinta don lallabata yake kamar kwae ….

Fita yayi ya leka part din hanne ga mamakin shi ya tarad da ita kitchen tana hada masu break ….sai da ya tayata suka hada komae sannan ya koma dakin Hudah ….

Lokacin ta tashi amma tana kwance idonta na kallon sama ….Tana jin shigowarshi ta maida idonta ta rufe ..

"Hudah ....baki tashi ba har yanzu ....!!ya fada tare da shafa wuyanta  ...

Da sauri ya janye hannunshi …yana kallon fuskarta ….”Subhanallah …Hudallah…ba dae baki lafiya ba ? …ya fada a rude …

Dagota yayi tare da rungumeta yana mata sannu ……

Sae da taji duk ya rude sannan ta bude ido tana hararanshi ta kasan ido …

“Bakya lafiya ne Hudah .?..sorry fada man kinji …!! ya sake tambayarta a rude ..

Banza ta mashi na tsawon lokaci sannan tace …”Lafiya na lau “

“Amma jikinki zafi Hudah “…ya fada tare da dago fuskarta ..

Haka jikina yake fa Uncle …!

“Kin tabbata lafiyarki lau ? …

daga mashi kai tayi tare da mikewa a hankali ta bar dakin …ba tare da yace mata komae ba ya bita da kallo har ta bar dakin ….

4 month

"Uncle wallahi wannan rito ne ...kuma baran  yarda ba .."..ta fada tare da rike guiwar kafarta  ..

“Ga Auntynki nan ta mana shari’a …ai ta gani tsabar rigima ne irin naki …kuma kema kin san ni nayi winning ba ke ba…..”

Kusa da hanne ta koma tare da dafa kafadarta ..”.Aunty hanne dan Allah ba sae da ya’yan wasana suka shiga ba sannan ya saka nashi? …

Cikin dariya Hanne tace ..”kinga Hudah ba ruwana da rigimarki …kufi kusa…idan kin gama kya sameni kitchen ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button