A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gwalo ya mata tare da mayar da kudinshi aljihu ….

“Wallahi Uncle sai ka bayar dasu …tun da bani nace ka sa kudin ba” …

Ta fado jikinshi tana kokarin karbar kudin …fito dasu yayi tare da yin sama da hannunshi yana mata dariya ….

Kokowa sossae take sae ta karbi kudin …hannuwanta duka biyun ya hade tare da matseta a kirjinshi yana mata cakul kula …

Zuciyar ta ji tana tashi …ta fara kokarin fita daga jikinshi saboda bata son kamshin turaren dake jikin kayanshi ….bai lura da yarda take ba …ya rike ta gam ..

Ganin ta fara kakarin amai ne, ya sashi dagota da sauri …kafin yayi wani kokari ta wanke mashi jikinshi tsaf da amai …

Sam Aman bai dameshi ba …”sorry” kawae yake fada tare da rike fuskarta da duka hannuwanshi …

Sae da Aman ya lafa sannan ya dauketa ya shigar da ita toilet din dakinshi ya wanke mata jikinta tare da mata wanka sannan ya fito da ita ya zaunar da ita gefen gado …ya koma yayi wanka ya canzo kaya …

“Sorry Hudah …..” ya fada a hankali kamar zaiyi kuka ….

daga mashi kai tayi a hankali …sam bata kaunar kamshin turarenshi amma barata iya gwada mashi ba …rungumeta ya sakeyi sossae …yana shafa fuskarta …

A hankali hawaye suka fara bi mata fuska …lokacin da yake kokarin kwantar da ita sossae a jikinshi lokacin zuciyarta ke kara tashi ….cikin dubara ta zame jikinta tana mashi murmushin yake …

FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????

            ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..

89 to 90

Da daddare ta kwashe duka turarukanshi ta boye ....da ya tambayeta sae cewa tayi  "ta gyara dakin ne ta manta inda ta ajesu" .....

da yake ranar ba gurinta zai kwanta ba …sae tayi baccinta lafiya …..

Ranar da ya dawo dakinta kuwa …kwana tayi tana amai gashi ta kasa fada mashi shine silar aman nata …tun da safe ya kaita asibiti …

Doctor ya tabbatar mashi da matarshi tana da ciki wata 2 …farinciki sossae ya nuna …shi kanshi doctor din sae da ya sami kyauta ta musamman …

Kasa Hakuri yayi ya wuce da ita gidansu …acan yake gayawa Mamanshi wae Ya kusa zama Abbah …dariya maman tayi cike da kunya ta barshi ….Haka Hudah kasa ko da motsi tayi saboda kunya …..

Tun da suka shiga Mota taki ko da kulashi ..ya sani sarae fushi take dashi …..Hannunta ya kamo ya rike tare da kallon Fuskarta …ganin sam hankalinshi ba ga hanya yake ba ya sata kwace hannunta tana hararanshi …

” Uncle ka kalli gabanka mana “..ta fada tana hararanshi ..

“Taya zan kalli gabana bayan kina fushi dani Hudah .?…to naji nayi laifi kinji ko …kiyi hakuri, farincikin da nake cikine bara ya boyi ba ba …!!

Turo baki tayi tana kallon taga ba tare da tace komae ba …hannunta ya sake kamowa ya hade da sitiyarin motar yana murzawa a hankali …

Dan satar kallonshi tayi taga yarda duk ya damu da fushin nata ….kwantar da kanta tayi saman kafadarshi tana shafa gefen fuskarshi …

“is ok Uncle ..Hudah barata taba fushi da Uncle dinta ba ….!! …ta fada cikin kunnenshi

"Are you sure !...ya fada a hankali tare da parking motar kasan wani icce ...

Daga mashi kai tayi tare da sake mashi murmushi ….”Me zamuyi nan Uncle?

"Na gaji ne nake so na kwanta bisa k'ashin matata na huta for some minutes ...!!

Turo baki tayi ..”Lallae Uncle ni ce k’ashin ? …wallahi zaka maimaita …!! Ta fada tare da girgiza kai..

" Oho dae ...Lokaci da zaki bukaci na maimata ke kanki rokona kike na barki .."..ya fada tare da kwantar da kanshi saman cinyarta ...

Wani uban ihu ta sake jin kamshin turaren nashi ya cika mata hanci ..ga har zuciyarta ta fara tashi ….yayi saurin tashi zaune yana tallabo fuskarta …

“Menene Hudah “..,.Ya fada a rude …

“Uncle Kaza …Ji Uncle dan Allah ka sayar man zanyi kiwo ko guda Daya ce please”,..ta fada don bata so ya fahimci wani abu … a tunaninta duk yarda na miji ya kai ga sonka bara ya ji dadi ba kace baka son wani abu daya dangance shi

“Ohoo Hudah Wae meke damunki ..?..duk wannan ihun na kaza ne …?..Allah ya shiryeki !! ….ya fada tare da bude motar ya fita …

Gurin da yaga kejin kaji ya nufa …ya iske saura kaza daya da zakara …kudin ya biya aka saka mashi su cikin kwali sannan ya sayar masu buhun abincisu daya ….

Harde Hannayenta tayi tana watsa washi wani wahalallen kallo …”He’s such a cring person ….!! ..ta fada a hankali tare da bude mashi motar ya shiga …suka saki murmushi lokaci guda …

Duk lokacin da Uncle dinta zai kwana dakinta sae ta sami kerosine ta shafa a wani hanky ta riga sinsinawa ba tare da ya lura ba …hakan da take yi ya mata rage yawan aman da take …

••°°••

Kamar yarda ta fadawa su barister Shehu …wanda ya sayi gidan a hannunsu yaje yace su fitar mashi daga gida..daga farko dad din yace bai yarda ba …sae da mutumin ya nuna mashi takardun gidan tare da shaida …sannan ya kalli Shehun cikin bacin rai zaiyi magana…

FEEDOHM????
???????? A DALILIN YAYATA????????

                ????

HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..

*_BONJEN muyitda bueda...Aunty sis , Jeedah Aliyu,Ummi A'isha, Asy khaleel , Pherty ,Khaleesa ,Afra ,Hajja ce , Queen Mermue ,Nafee Anker, Asmy B, Billy B ,Billy G, Candy, Classic, Aisha Muhammad ,Maman khadija ,????????????_*



  *END...*

Sae yayi shiru ganin ba amfanin maganar domin shehu kamar gawa yake sae tarda akayi dashi ….haka suka tattara kayansu suka bar gidan …Allah ma ya soshi guest house dinshi yana nan ….suka koma can …

Cikin Yan watanni kudin magani suka fara cinye duk wani abu da ya mallaka…ga shehu akwance paralysis ya gama dashi kullun abun karuwa yake ..sannan shi da Hajiyar kullun suna neman magani amma abun ba saa

••°°••

Hudah kuwa Uncle Mahmoud soyayya yake nuna mata kamar ba gobe ..sannan shi da kanshi yace ta bari ta haihu sae ya maidata makaranta …

 Suna zaune cikin garden  lokacin ta daina jin warin turaren da yake sawa  ....lafe take a kirjinshi yana karanta mata wani novel .. _Tears drop at the sunset_ Zakaran da ya sayar mata ya biyo kazarta tibi tibi ...suka zo suka wuce ta shinfidarsu da gudu ...

Kallonta yayi yana fadin …”Umhum …dama barewa zarayi gudu ne danta yayi rarrafe …”

Sam bata fahimci inda zancenasa ya dosa ba …ta dago tana kallon kajin tare da fadin ..”Uncle sun yi girma ko?

“Dole suyi girma man …tun da mamansu ma ta kara girma …sae dae ya kazar ya mamanta …!!

” Uncle ban gane ba ?…ta fada tare turo da baki …don ta fara gane magana ya fada mata …

Huh …yarda kazar ke gudun zakara haka mamanta ma ke guduna…kin fahimta sossae ko ?

Dan duka ta kai nashi a kirji tare da fadin … “Kai uncle !!

” Ba haka bane ? …ya fada tare da kafeta da ido …

Kara shigar da kanta tayi a kirjinsa … “to yi Hakuri ai kaga bana lafiya ne ?

Ko ? ….Ya tambaya tare da saka hannu a yana shafa jikinta …

Bata ce komae ba sae turashi da tayi ya kwanta ta daura kanta saman cikinshi tare da lumshe ido …

••°°••

Tun safe ta sakashi gaba tana masa kuka …tambayar duniya ba wadda bai mata ba amma taki bashi amsa …

wajen sha biyu ya fito daga wanka ya iske still inda ya barta tana sharan hawaye …

Hannu ya mika yana fadin ..”.Haba Hudalliyar Yaya Sa’a zo nan ki fada man me kike so kinji ko .!!…ya mikar da ita tare da zagaye kugunta da hannunsa …

Turo baki tayi tana fadin …

“Uncle ina indomie din da ka dafa man ranar da ka daukoni daga gidanmu ? ..

Ido ya waro …”duk da dai ya manta amma Bai isa yace bai tuna ba …sae cewa yayi ” Na ma isa na manta ta Hudah ..ya akai ?

” Ita nake so ka sake dafa man yanzu ” …ta fada tare da kwantar da kanta a kirjinsa …

"   Hudah!! ....ya fada da sauri .."Over 6 years fa kenan ? 

" Bara ka tuna yarda ka hada ta ba ? ..ta tambaya a hankali ..

” Haba Hudah ..taya zan manta …bani 30mints yanzu na kawo maki kinji ko ….? ..ya fada tare da shafa kanta

Peck ta mashi a kumatu cikin jin dadi….har ga Allah bawai don ta bashi wahala ba …aa ta tashine kawae tana son cin irin indomie din …duk da itama ta manta koda kalar taste din bare shi da ya dafa …

Kitchen ya shiga kasancewar Hanne bata ban …tana gurin kasuwancinta …rasa abunda zaiyi yayi …Hudah ta riga ta shagwabashi in banda yankan albasa da zuba maggi a abinci babu abunda ya iya ..hana rantsuwar tana bashi ya mata taste yaji idan abincin yayi dadi da kuma zubawa a coler ….

Lumshe ido yayi a hankali ya bude fridge dauke da addu’a …ya fito da fura da youghurt da inibi da kwakwa ya zuba a blender ya dama mata …sannan ya saka kankara kadan …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button