A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sae da yayi addu’a sannan ya shiga dakin …cikin fara’a ta mika mashi hannu ..tana ganin fura ta bata fuska zatayi kuka …
Dukawa yayi gabanta tare da dafa guiwarta ..”
“sorry Hudah …wallahi da zan iya tuno yarda na dafa maki ita babu abunda zai hanani kare rayuwata a matsayin kukunki …Kin sani duk wani abunda zai sakaki farinciki nima shi nake so Hudah …Kiyi Hakuri kinji ko ..ki sha furar kafin naje kitchen din na dafa har Allah yasa zanyi wadda zata maki dadi kinji ko …!!
Hannunta ta kai ta karbi furan tare da rike hannunshi da cup din guri guda …sannan ta saka gudan hannun tana shafa sumar kanshi ..tare da kissing din goshinshi …
“Nagode Uncle .!!….ta fada cikin kunnen shi tare da hura mashi iska a hankali ..
” Zan sha wannan din ka ji uncle dina …wallahi indomie din ma ta fita raina karka damu …kayi hakuri idan na bata maka rai …!!.
°°••°°.
Cikinta na cika wata tara ta haihu santaleliyar diyarta mai kama da Babanta ….Murna gurin family din ba’a magana …kudi kuwa kamar suke nomansu …
Ranar suna diya taci Sunan Sa’adatu …ana kiranta da MUNIFFAH ( Sabon farinciki.. ) …ita kanta Hudah bata san sunan Mahmoud zaya saka ba …sae daga baya take ji gurin wanda suka shigo ….
Tana zaune tana bawa babyn mama ya shigo cikin mayan kaya yayi mata masifar kyau ….dagowa tayi ta zuba mashi ido har ya iso kusa da ita …tare da dukawa ya sumbacin babyn sannan ya kai lips dinshi saman na Hudah yana kallon cikin idonta
Lumshe ido yayi yana fadinn ..”Wannan kallon fa? …baki san kin haihu ba ? ko so kike ki ja man aiki !!!
Dan murmushi tayi mai sauti kafin ta zame daga kan gadon ta koma kasa tare da rike kafafuwanshi …
“Uncle …ban da wani bakin da zan iya gode maka ..Illa iyaka na barwa Allah ya saka maka da mafificin Alkhairi ….Tabbas kai haskene daga lokacin da Allah ya hada ni da kai na tabbata na cika mai sa’a ga dukkanin rayuwata ….Uncle duk yarda kake tunani ka wuce anan arayuwata …ka zama wani jigo babba gareni …ka katangeman duk wani bataccen lamari a rayuwata …Tabbas ban da kamarka Uncle ..sae dae ina tabbata maka da ana bautawa wani babu abunda zai hana Hudah dawwama tana bauta maka …Sae dai Alhamdulillah Allah kadae muke bautamawa kuma shine zai saka maka da abunda kaman …Na maka alkawarin Uncle zan dauwama ina faranta maka har na koma ga mahaliccina ……
Dagota yayi a hankali ya rungumesu tare da babyn a kirjinshi …….
Rabbana aamannaa bimaa ‘anzalta wat-taba’nar’rasuula faktubnaa ma’ash shaahidiin….????????
Bhoti munkje abta neyza pyaza wutebin photah nahi myezida boti…
Nagode sossae da kaunarku …08066598868.. Fiddausi Musa aka Feedohm????.. Sai mun hadu a littafi na gaba…????????????????
FEEDOHM????