A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tace .. kawae ya barsu police babu abunda zasu iya yi a kae …su sun barsu da Allah ko su waye …
Cemata yayi zaya je ya dawo in Allah ya yarda yanzu …sannan ya mike ya tafi …..cikin kudin da ya sace ya dauko dubu dari biyar ya kawo mata ….yace tayi jari da su ……
Godiya ta dinga mashi har da kukanta ……Huda ta shigo dakin tayi saurin dukawa gurin mamarta ta …
Mamana me aka maki ….dan Allah kiyi shiru idan ma naira hamsin da zaki dinga bani kikewa kuka …wallahi na yafe ki dinga bani arba’in idan kin samu ……ta karashe maganar kamar zatayi kuka …
Huda Lauya ya bamu taimako …banda bakin gode mashi ….ku tayani godiya ….ta share hawayenta …
Mamana dama ya kawo ya sace.. kuma ya sake kawowa zai kuma sacewa ne …..ta fada tana kallonshi….
zumbur ya mike yana fadin ….Huda waye ….nan da nan zuba ta fara keto mashi ….
Da hannu ta nunashi tana fadin ...eh mana banda kai waye yasan muna da kudi ....
Mamanta tayi saurin buge mata baki tare da korata ta fice waje tana kwalla …
tana fita gurin motarshi ta nufa ….ta samu kwalba duk ta bula tayoyin gaban motar sannan ta bar unguwar …
Maman tata ta dinga ba barister shehun hakuri tana fadin …Huda yarinyarce karda maganar ta bata mashi rai ….sun gode sossae Allah ya basu abunda zasu saka mashi dashi …..Yaya Saa ta shigo har kasa ta gaidashi ….ya amsa cikin faraa da yake ita yana shiri da ita …ta mike ta fita …yabi bayanta da kallo yana wani irin murmushi …….
Sun dan taba hira da mamar sannan ya tashi ya tafi …..da yake weekend ne gurin mutanen da sukayi aiki tare ya nufa …su hudu ya basu 1m suka raba ….sannan ya tafi da saurin yana ganin yarda akawa tayar motarshi ya tabbatar da huda CE ..don ta bar mashi sheda a gurin na dankwalinta da ta yarda …kwafa yayi ya bar motar gurin …sannan ya turo mai gyara yazo ya dauka shi kuma ya haye okada……Da yake yana business din zinari …sannan duk kasuwar kano babu mai katon shagon zinari irin nashi …sae ya kaiwa wanda ke sayo mashi zinarin india kudin duka ….yace cikin satin yaje ya sawo a kara jari akan wanda suke dashi ….
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Bayanshi Abba ya dafa ..meke damunka mahmod ….
Da juyo da sauri tare da goge hawayen da suka wanke mashi fuska ….
Subhanallah …wae meke faruwa Mahmud ….ya fada tare da zama kusa dashi …
Bakomae Abbah ….ina so na aje aikine ….ya goge hawayen da suka zubo mashi a fuska ….
Kul Mahmud kar na sake jin wannan zancen a bakinka …shekaranka nawa kana karatun ? ….ka bar iyayenka tsawon takwas baka kasar …sannan yanzu ka cika man gurina kace zaka aje akan me …..
Ban cancanta ba Abba ……Wallahi ban dace da zama barister ba …a matsayina na mai kare hakkin mutane amma nayi falling akan rayuwar marayu ….
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 A DALILIN YAYATA…馃崄馃崄
馃崄
HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕
Na Feedohm馃挒
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..
11 to 12
Abba yace ...Allah ne bai baka saar karesu bane Mahmud ...karka damu kayi ta addua wata rana zaka zama jigon marayu ......tashi muje kayi breakfast kaji ko .....
Bayan sun gama breakfast din ya fita unguwarsu Huda ya je ....ya aje motarshi cikin inuwa ya haye saman motar yana kallon mutanen dake zirga zirga .....
Yaya Saa tazo wucewa janye da hannun Huda ....ganin yana kallonsu ya sakasu tsayawa ta gaisheshi sannan suka wuce ....shigarsu gida da yan mintuna kadan yaga Huda fito dauke da markade ....
Mekake kallo tun dazu .....ta katse mashi tunani tare da kura mashi ido ...
Murmushin yake ya sakar mata yana fadin ...zo nan ina zaki ...
Harara ta watsa mashi ...inda ka aikeni .....
Zo dan Allah Hudallah ….kinji ko …wani abu zan tambayeki ….ya mika mata hannu
Kaini yanzu an bar hadani da Allah na yarda ….nima jiya ina ta hada wasu da Allah amma sukaki bar mana kudinmu ….kaje kayiwa Mamana jaje kuwa ….ko baka sani ba ….
Yaya Saa ta leko tana nemanta ....tayi sauri boyewa bayan motarshi tana fadin ....Dan Allah kace mata ka ganni nayi nan da gudu tun dazu ....
Dan murmushi yayi sannan yace ….ki fito ta koma ….sae da ta dan leko sannan ta fito …..da gudu ta tafi ….kafin ta bar layin bokitin markaden ya kife kasa ……
Da Sauri ya isa gurin ya dagota yana kakkabe mata jiki tare da sannu ….sannan ya tsince mata wanda bai taba kasa ba sossae yace ta koma gida a wanke mata….
Ido ta waro tana fadin …ka dauka banda hankali …so kake mamana ta daman dukan tsiya….baka gani tun dazu na fito ka tsayar dani da surutu …
Ta dauke bokitin ta sake kwasawa da gudu ….gidan markaden aka wanke mata sannan aka markada …..
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Malan Ibrahim Headmaster ne na primary ta gwamnati …mutun ne da yake da kyakyawar dangantaka da mutanen da yake muaamula dasu ….tun yana yaro bai cika kwarabniya ba ….su biyu ne gurin mahaifiyarsu sae daga shi sae Yayarshi hanne …yana da yan uwa wadanda suke uba daya su shidda hudu mata sae biyu maza ….tun da suka taso basa kaunarsu Ibrahim har suka girma suka zama ware …wadancan kuma suka hada kansu tare ….Hanne nada ya’ya biyu ciwon daji ya kamata ….bata dade tana jinya ba Allah ya dauki ranta ….ta bar Malan ibrahim shi kadae cikinsu …yaso yaga sun hada kansu amma sam suka nuna basa kaunar dangantaka da su …daga karshe ma suka ce sun yanke zumunci da shi gaba daya ….haka ya barsu ba dan yaso ba ….ya dawo cikin garin katsina da zama unguwar kofar marusa inda yake aiki a matsayin headmaster tare da matarshi guda daya …Fatima da ya yansu biyu …Saadatu sae Huda ……
Suna zaune cikin rufin asirin Allah ...duk da Huda bata jin magana hakan bai dameshi ba kullun addu ar da yake Allah ya shiryata .....Yaya Saadatu kuwa bata cika magana ba ...sannan ba ruwanta da kowa bata da abokin fada duk unguwar shi yasa mutane ke mugun ganin girmanta ....Sae ta dauki son duniya ta daurawa Huda ...bata kaunar taga koda digon hawaye a idon Huda .....don lokacin da Hudar ke karama ....kullun tana makale da yaya saa duk abunda ta samu to zata bawa huda shi ...idan kudib tara aka bata naira biyar to bara ta kashe ko naira ba sae dae tayowa Huda tsaraba da su ....tana dawowa zakaga Hudar tana tsalle ko hannun wa take tare da washe baki tana mikawa Yaya Saar hannu ....to har dare bara ta kara yarda da kowa ba sae yaya Saar ......idan kaga Yaya saa na kuka ta Huda ce take kuka ...sannan idan har tana dariya ta Huda ce ke dariya....Har mamakin Soyayyarsu ake ...zaa iya cewa Yaya Saa tafi son Huda Akan iyayenta ....
Lokacin da suka fara girma …aka saka Huda makaranta ….idan suka makara to yaya saa zata tara hannu ayi mata dukanta dana Hudar sannan ta raka hudar Aji itama ta tashiga nata …da yake Lokacin Huda na Aji Daya …ita kuma yaya Saa na aji shiddah ……
Barister Shehu makwabtan gidansu Malan Ibrahim ne …ya yarda dashi matuka ..duk wani abunda ya shafi gidan Malan ibrahim Barister Shehu yake fada mawa …da yake ya daukeshi kamar kaninshi tunda baya da wasu yan uwa da zaya nuna yace nashine …
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 A DALILIN YAYATA馃崄馃崄
馃崄
HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕
Na Feedohm馃挒
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..
13 to 14
Huda na aji Uku Malan Ibrahim sunje wani taro da suke na oldboys daura mai adu'a...sukayi hadari motar ta kama da wuta ...su shidda cikin motar babu wanda ya fita cikinsu ....a ranar sunga tashin hankali unguwar don ba karamin rashi sukayi ba ......Sam Huda bata san me ake ba ...ana zaman gaisuwa ita kuma ta tara yara suna carafke .....kowa kallonta yake ...
Bayan kwana goma ne da taga ta rabu da ganin babanta sae ta fara tambayar Yaya Saa …ina babanmu
Sae dae tace mata …Huda bayana nan …zaya dawo kinji ko …
Daga bayane ta fahimta sosaae ….shima batayi kuka ba sossae …ta danyi yan hawaye da akace mata bara ya dawo ba …daga baya kuma ta share hawayen tacigaba da wasanta ….
Barister Shehu sae ya koma shi ke kula da duk dan abinda malan Ibrahim ya bar masu …mutane sun dan tara masu taimako…sannan duk abunda ta samu sae ta sanarwa da Barister Shehun …Daga baya sae komae ya tsaya masu abincin da zasuci ma sae ya fara gagarar su daga baya ma Sae mamarsu Huda ta koma tana zuwa ta dan taya mamarsu Barister Shehun aiki duk wata ta dan bata abunda zasuci abinci …Da yake masu kudine …
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Wae lafiya barister two weeks baka zo office ba .....
Dariya ya sake da rafu kuka ciwo sannan yace ….Normal Shehu kawae har yanzu ban sake da lamarin munafikin mutun kamarka bane ….ya karashe maganar yana dafa kafadarshi …..
Munafukan mutane dae guda biyu ….ya bashi amsa tare da fashewa da dariya …..
Meye Ribarka ciki Shehu ka cutar da marayu wadanda kae ya dace ka taimaka masu .karamar yarinya tana rokonku amma ka kasa tausaya mata….Ya tambayeshi a sanyaye …
DALILIN YAYARTA nake komae shi yasa na tsani yarinyar don na lura duk abunda bata so to yayarta ma bata so ….saboda yarinyar yayarta take kina duk da bata fada man ba …..Barister Mahmoud ina tsananin son Saa …amma Huda bata sona .saboda hakan Saar ma bata kaunata …har gida naje na kaiwa saadatu kudi ta bar awarar amma taki karba tace suna da abunda zasu rufawa kansu asiri ….idan suka talauce ba …ita da kanta zata zo ta rokeni ni kuma lokacin zanyi amfani da damata …….
Ba tare da ya bashi amsa ba ya bar office din don baya bukatar zama tare dashi ………
Gidansu Huda ya nufa cikin saa ya ganta ta fito tana cin goriba ......kwala mata kira yayi ....
Daga bakin kofar gidansu ta tsaya tana watsa mashi harara tare da fadin….wallahi yaro ka mayyar garinnan ta yayeka bara ka ci goribar nan ba …..
Lumshe ido yayi ya matsa kusa da ita yana fadin …baci zanyi ba Huda ….ki shiga kicewa Mamanki ina son magana da ita kinji ko …
Lah bata nan ….tana gidansu lauya tana aiki sae da marece zata dawo ….ta bashi amsa tana kallonshi …
five thousand ya ciro ya mika mata yana fadin …ki kaiwa Yayarki …kice tayi maku cefane kinji ko …