A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsaye tayi tana kallonshi kafin ta juya ta shige gida ba tare da ta karbi kudin ba ….ya dade tsaye yana tunanin ko zata sake fitowa amma sam babu dalilinta ……

Ko da ta shiga cikin gida ta iske yaya saa tana wanki …da yake yanzu ita kewa yan gidansu barister shehu wanki suna biyansu ….

Yaya Saa kawo na dauraye maki ….ta janyo bucket din da kayan wankin ke ciki ta fara daurayewadaurayewa

Da sauri ta rike hannunta tana dariya …barshi Huda karki jika jikinki ….

Baran jika ba Yaya Saa ki bari na tayaki ….ke kullun mutun zaya maki abun kirki sae kice bakya so ….ta karashe maganar kamar zatayi kuka …..

Bana so ki wahala ne Huda kinji ko ….zan maki komae a rayuwarki in Allah ya yarda ba zaki wahala kamar ni ba ….karba ….ta fito da naira goma dake daure a zaninta ta mika mata ….

Jiya kince kina so ki sayi dankalin gidan Lado ko ….ga kudin na samu kije ki sayo sae kici kinji ko ….karki toni kuwa saman hanya ba ruwanki da kowa ….kinji ko …

Kallonta tayi tare da kura mata ido ba tare da ta amshi kudin ba …ita tama manta ta tayi maganar jiya …amma yaya saa tana rike da abun bata manta ba …..

Karba kanwata …ta katse mata tunani tare da janyo hannunta ta aza mata kudin ta turata waje tana murmushi …..

Har lokacin Motar mahmoud na kofar gidan …..ta kalleshi da idanuwanta da suka ciko da kwallah sannan ta kauda kai taci gaba da tafiyarta …..

Feedohm馃挒
鈥⑩€⒙奥�
馃挧馃挧 A DALILIN YAYATA馃崄馃崄

                   馃崄

HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕

Na Feedohm馃挒

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…

Gaisuwa mai yawa ga haske writers Allah ya kara basira da daukaka..

15 to 16

     Saadatu bakya wankewa su hajiya kaya suna fitane sossae ....Mama ta fada lokacin da ta kai lomar tuwo a bakinta ...

Da Sauri Yaya saa tace …wallahi mama ina wankewa sossae …cewa sukeyi basa fitane

Aa cewa sukayi wae sae dae kije can ki dinga wankewa zasu fi fita acan …..amma gaskia ni bana son wannan yawon Saadatu …ni ina fita aikatau kema ace kina wankau …Sae dae suyi hakuri

Aa mama zanje ….don Allah ki bari naje ….idan har na bar wankinnan ban san inda zaa sami kudin da zaa kai huda secondary ba …dan Allah karki hanani …bana so Huda ta wahala kamarni ..ina son ta samu ilmin mai yawa …dan Allah ki bari na nemawa Huda kudin makaranta da karfina …dan Allah mama …..hawayen dake cike da idonta suka samu damar gangarowa saman kumatunta …..

Huda ta matso kusa da ita saka hannu tana goge mata ….Dan Allah yaya saa kar kiyi kuka kinji …ta tabe baki hawaye na sauka saman fuskarta …

Nan da nan yaya Saa ta maida hawayenta tana lallashin Huda …Mama na zaune ta zuba masu ido …..

鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�

Table din dake gaban Barister Mahmoud ya buga da karfi yana fadin ….Meye dalinlinka na bincikar shaguna na

Idan table din ya amsa to barister mahmoud ya amsa masa ….

Wallahi Mahmoud ka kuskura maganar nan ta fasu na rantse maka da girman Allah sae na watsa ka a duniya …sai na saka ubanka da kake takama dashi ya tsaneka da ka shi zai koreka ka fitar mashi da gida …Don wallahi bani kadae zan dauki laifinka har da kai …sannan ka sani inda kyakykyawar hujjar da kai akayi fashin …….

Then So what idan ka fadawa duniya har dani akayi fashin ….kai duniya ta dama amma ina tabbatar maka wallahi asirinka yana gab da tonuwa..

掳掳鈥⑩€⒙奥�

Dady wani abokin aikinmu ne ke cikin matsala wallahi ..

Dady ya kalleshi tare da fadin ..
Subhannallah meke faruwa dashi ….

Lumshe ido yayi sannan yace …Wae wasu sukayi forcing dinshi yayi fashi a wani gida ….

Ya so ne Mahmoud ….sam bai kyautawa aikinshi ba da iyayenshi …

Dady dole ba aka mashi ….

Mahmoud na san idan kaine ko zaa daura maka bindiga bara kayi ba ….kabar wannan maganar ….Allah ya kyauta ..

Ameen amma dady …

hannu ya daga mashi ….akul Mahmoud ….gobe ka shirya zamu je kauye akwae diyar Kawu Nalado da yace ya baka ka aura ….

Aure dady ….ya fada a firgice ….

Nima umarni aka bada Mahmoud Allah yasa Alkhairi ce …..

Ba tare da yace komae ba ya sadda kai …kirjinsa ke dakan uku uku ….addua yake karantuwa har ya samu natsuwa sannan ya mike ya fice falon….

鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�

Kamar yarda Yaya saa ta fadawa mama haka take zuwa kullun gidansu barister shehu tana wanki sannan ta dawo ta baro mama gidan …..A lokacinne Huda tayi jarabawar fita daga primary school …..bayan jarabawar ta fito ta samu Government day dake kusa dasu …..

Yaya saa tace bara tayi government ta tara kudin da zata kaita makarantar kudi ….ita da kanta ta kaita makarantar ta mata registration da kudin da take tarawa……

Ranar da ta kaita makarantar ta juya zata tafi taga discipline dinsu ya daga bulala zaya daki Huda ….tayi saurin dawowa ta rungumeta tana rokanshi kar ya daketa sabuwar zuwa ce …..

Huda kuwa girgije girgije take tana fadin …yaya saa barshi ya tabani bai san Hudalliya bace …yaro kaje unguwarmu ka tambayi yarda nake kada katti kasa ina duka …

Yaya Saa tacewa malamin …dan girman Allah kayi hakuri ka barta tana da matsalar aljanu ne shiyasa bata ji..

Ido ta waro tana karkade kunne ….zuki ….Kai yaya saa dan dae kece da sae ince …Mamanki ta saka man su ….amma kiyi hakuri kinji ko …

Bata ce mata komae ba taci gaba da bawa malamin hakuri wanda yace …idan duk duniyace gatanta sae ya daketa tunda bata da kunya…..

Ganin yaya saa na kuka ya saka malamin kyale Hudar ….

Feedohm馃挒
馃挧馃挧 A DALILIN YAYATA馃崄馃崄

                     馃崄

HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕

Na Feedohm馃挒

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..

   _*Thank you so much sweet HAJJA....YAS鉂�..komae naki daban yake da na saura .....!..I Hhp am the first to wish you Happy birthday ASMY馃憚 ....WULLNP.....!..Best wishes UMMI A'YSHA..Kdeey ..Ayusher..Kubrieh CIE...billy galadanchi..Maman Khadija ...Asy darling ...khadeeja chafe ...Khadija candy ...jeedah Aliyu ..Billy BB...Nafee Anker.. Amnoor ... Queen Mermue ...IRSY馃槝*_

17 to 18

  Zaman Yaya saa gidansu barister Shehu ...Sae ya fara kawo mata salo daban daban ..

Idan tana zaune inda take wanki sae barister shehu ya dinga zuwar mata da zancen banza ….tun bata kula shi har ta fara jin tsoronshi …don tana zaune sae taji mutun ya shafa bayanta ……

bata taba fadawa kowa ba sae dae tayi ta kuka ….don kwata kwata bata jin dadin aikin yanzu …Sae tana zaune sae Shehu ya dinga kokarin taba mata kirji ….Sae tayi niyar Barin aikin sae ta tuna da Huda dake makaranta ….

Yau ma bayan ta gama wankin tana tsaye tana shanya kayan …Shehu yazo ta bayanta ya rungumeta ….ta fara kokarin kwace kanta tana kuka …yaki sakinta sae ma kokarin sakamata hannu yayi a cikin riga ….hajiyarshi ta leko tana fadin …

“Shehu wane irin shashanci ne wannan”…!

ya juyo a firgice yana kallonta ….Yaya saa kuwa wani sanyi taji a ranta ta saka bayan hannunta zata goge hawayen ….cak ! ta tsaya lokacin da hajiyar ke fadin …!

"Idan sha'awarta kake bara ka jata daki ba sae ka tsaya waje salan uwarta ta fito ta ganka kuma ka ja mana tsegumi ".....!


Bai jira komae ba ya fizgeta da karfi ya shiga da ita dakin dake kusa dashi ...wani ihu ta saki tana turje turje tare da hadashi da Allah ya barta amma sam yaki barinta ...sae da ya rabata da darajarta ta ya mace ....sannan ya janyota kamar kayan wanki ya wurgota waje inda take wankin ya koma daki.....

Hajiyarshi kuwa tana shiga ta iske mamarsu Huda na goge goge ….tace mata..” ta tafi gida zata fita unguwa”…..

Mama tace mata ….”To bara na kira Saadatu tana baya tana wanki “….

Hajiya tace …”aa ki barta na aiketa nan makwabta ta karbo man sako” …

Mama tace …”to Na tafi hajiya Allah ya kiyaye “…..!

Yaya Saa lokacin da hankalinta ya dawo ta hade kai da guiwa tana kuka kamar ranta zai fita ….ga uban radadin da ke damunta ….haka ta ja jikinta ta fice daga gidan tana kuka ……

Zata shiga gida ta ga Huda ta dawo daga makaranta rataye da jikka …..baya ta koma ta lafe jikin bango gudun kada Hudar ta ganta tana kuka hankalinta ya tashi …har sae da hudar ta shige gida sannan itama ta share hawayenta ta shiga gidan …

 Bata bari Mama ta gane halin da take ciki ba ...sae dae Huda da ta kamata tana kuka bayan ta gama sallah isha'i ...!

” Yaya Saa me aka maki .”…ta tabe baki …nan da nan idonta ya kawo ruwa …

Jikin Hudar ta fada tare da sakin kuka ….Hudar ke girgizata tana kuka ….”Yaya Saa dan Allah kiyu shiru …me aka maki dan Allah ….waya tabaki Yaya …Yaya Saa dan Allah ki fada man “.

Girgiza mata kai take tana kokarin tsaida kukan amma sam ta kasa ….ita da Hudar ke kuka kamar ransu zai fita ….Yaya Saa ta kasa fadawa Hudar asalin damuwarta ….tama rasa bakin da zata mata magana …bata so Hudar taji abunda ya faru da ita saboda tasan Huda sarae zata iya rike abun a ranta har abada …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button