A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mama ta shigo ta iskesu haka ...tambayarsu take meke faruwa amma babu wanda ya bata amsa ...da taga abun bana karewa bane ta zauna ta zagesu tsaf tace su mata shiru ko su fitar mata daga daki ...idan bara su fada mata damuwarsu ba ......Yaya Saa ta fara shiru sannan ta lallashi Huda da kyar ta samu tayi shiru ...
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Karfe 3 na rana su Barister Mahmoud suka isa kauyen ....Kawu ya masu tarba mai kyau aka kawo masu madarar shanu da dambu ....Mahmoud kasa ci yayi sae dae yasha madarar kadae ...
shi kuwa dady zama yayi yaci ya koshi. …Inno ta shigo suka gaisa sannan ta fita
..Kawu yace “a kira Hanne “…
Feedohm馃挒
???????? A DALILIN YAYATA????????
????
HASKE WRITERS ASSOCIATION????
Na Feedohm????
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS
Nagode sossae da addu’o’in Ku Allah ya saka da Khairan????
19 to 20
Kaninta ya fita da gudu ya kirata dandali.....Ko minti 10 baayi ba sae gata da tawwagar Yara sunzo ga nin mijin da zata aura daga birni ....
Gaban Mahmoud din ta zube tare da kura mashi ido tana dariya ..
sannan ta juya gurin kawayen tana fadin ....Kun ganshi nan irin mutumin nan na jikin Rigar dan mai gari ....!!..Wohoho no Hanne Duk kauyen nan albarka !!
Hanne diyar kawu nalado …irin mutanan nan ne masu shegiyar karya da iyayi …..bata cin abincin gidansu ta gwammace ta sayi malak’i ….saboda inno bata sanya masu kayan miya kamar yarda gidan maigari suke nasu girkin .!!…Irin yaran nan ne masu hange hange ..baka da gashin wacce kace sae kayi kitson wance ….!!
Doguwace Jawur tana da kugu sossae da tsawon gashi ...amma kirjinta ba wani cikakke bane ....tun lokacin da kawu nalado ya fadawa Hanne cewa zata auri Mahmoud take ta murna don bata kaunar rayuwar kauye duk da acikinta ta tashi .....!!
Sae ma ta daina hudd’a da yaran da take hudd’a dasu ya’yan talakawa kalarta… ta koma sae Ya’yan gidan Maigari da masu kudin kauyen take hudda …!!
Su Mahmoud basu tafi kauyen ba sae da aka daura aurenshi da Hanne .!!…duk da dama ba da shirin aure suka zo ba …amma kawu Nalado yace ba abunda zasu jira ayi komae a gama su tafi da ita ….nan take suka bada sadaki aka daura ….su hanne sae murna ake ….Bangaran Mahmous kuwa tunda ya sadda kai bai kuma dagowa ba …zufa ke biyo mashi ta ko ‘ina …”Innalillahi wa inna illaihir raji’un” kawae yake …”Allahumma Ajir ni fi musibati “…kuwa ya furta ta tafi dari.!! …
wannan wace irin masifa ce ..!!!.abunda yake fada a ranshi kenan …..har aka gama daurin auren ….!!
Ko a mota bai iya furta koda kalma daya ba …sae Hanne dake ta karadi Abbah na biye mata ….!!
Gidansu Mahmoud din ta zauna kafin ya ida gyara nashi ….Momy ba ta iya cewa komae ba sae fatan alkhairi data mashi ….
••°°••
Tunda Shehu ya ma Yaya Saa fyad’e bata kuma zuwa gidan ba …haka mamanta kuma bata takura mata…sae dae tayi tambayar duniyar nan ta fada mata me ke damunta …..!
Bayan wata daya ne Yaya Saa ta fahimci tana da ciki ...domin har lokacin menstruation din yazo bata ganshi ba ...sannan ga wani canji da take ji a jikinta ....
Hankalinta yayi bala’in tashi sam bata da sukuni duk ta bi ta rame kullun cikin kuka take …ga bala’in tashin zuciya da take …abun kadan zaya sakata amai …
Tana tsugunne a kewaye tana amai gidan ba kowa ….Taji an dafa mata baya …ta juyo a firgice tana kallonta …ganin Huda ce ya saka ta sake a jiyar zuciya tare da janyo buta ta wanke bakinta ta mike …
Daki suka shiga Huda na rike da hannunta ta zauna saman gado tare da kara janyo Hannunta tana fadin ..!
“Me ya sameki Yaya Saa …sannu kinji” …cikinki ya kumbura ?….ta fada tare da kura mata ido…
Hawayen dake fuskar yaya saa suka samu damar gangarowa ….tana girgixa kai …
“Kiyi Shiru mana Yaya Saa …me kika ci ya kumbura maki ciki…bara naje gidansu Fatse na karbo maki maganin kumburin cikin kinji ko …sannu” …..ta mike da niyar fita …!
Yaya Saa tayi saurin kamo hannunta tana fadin …”Hudallah ! …
” Na’am Yaya saa” …menene ko tafasar jiya ta bata maki ciki …?.
Girgiza mata kai tayi tace …”Huda maganin da kike kokarin karbowa bara ya iya man magani ba !!…
Dariya tayi …”haka zaki ce Yaya saa bawae ki rikeni ba ! ..”to bara na kira mama gidansu lauya sae mu kaiko asibiti su baki magani …sae su rubuta sunana idan na gama makaranta na fara aiki sae na biyasu ko? ….ta mike da sauri …
“Tsaya Hudallah “….ta fada a hankali …”karki fadawa Mama hankalinta zai tashi kinji ko …ki barshi tsakaninmu karki fadawa kowa ina amai” ..
“Sirri Yaya Saa ..!!….ta fada tare da dafe baki tana waro ido …!
“Sirri Hudallah!! …ta bata amsa..
“”Sirrin Amai !!!…ta kara tambaya cike da mamaki …!
“Bara ki iya rike sirrin yayarki ba Huda ?…
“Zan iya mana Yaya Saa …ko mama baran fada mawa ba ..sae ma nacewa mutane Yaya Yar baiwa ce bata amai ….Sannu kinji Yaya saa ..Allah ya baki lafiya …Allah ya isarmu mai tafasar nan da ta sayar mana …muguwa shi yasa naga tana kallona …kila ma ni taso cikin nawa ya kumbura.”..!!
Bata ce mata komae ba ta mike …surfen da aka kawo mata ne …ta dauka tayi …sannan ta bawa Huda kudin ta saka Jikkarta ta makaranta gobe tayi kudin Tara…!!
Feedohm????
???????? A DALILIN YAAYATA????????
????
HASKE WRITERS ASSOCIATION????
Na Feedohm????
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..
21 to 22
Hanne!!!...irin matannanne masu shegen kilbibi da karya ....watanta biyu gidansu Mahmoud ta waye ta goge kamar ba ita ba ...kafin kace me tayi kawa makobtan gidan ....mai suna Saly ...haduwarta da Saly sae idonta ya sake budewa ...don kullun saly na gidansu Mahmoud tana kara budewa Hanne Ido ...kadan kadan sae ta fara zabgawa Maman Mahmoud Rashin kunya ....sannan idan an dafa abinci bai mata ba sae ta saka a sake dafa wani a zubar da wancan ...
Abun ya fara damun Momy gashi bata son ta fara kai karar Hanne gurin Abba …sae yaga kamar bata son zama da ita ….
Momy na zaune ta rabka uban Tagumi …Abba ya shigo tare da Mahmoud suna fira kadan kadan ….Hanne ta sauko daga upstair ta tsuke da riga da wando three quarter …..tana ganin Mahmoud ta sake fuska tare da tahowa tana murmushi
..
Babu kunya tayi niyar fadawa jikinshi …wani kallon ya sake mata babu shiri ta sulale kasa tana gaida Abba ….
Abba yace ” Hanne ki shirya zamuje kauye an kirani babanki baya jin dadi ..”
Ta hade Fuska tana Fadin “ni gaskia Abba baran je …idan kunje ku gaidashi ..”
Akan me? …Abba ya tambaya cike da Mamaki …
Gaskia Abba yanzu lokacin damina ne …nasan gidan duk ya kazance da kashin goat da cow da chickenks …kuma inno ba iya gyarawa zatayi ba …ni kuma baran je wari ya isheni ba …
daga Momy har Mahmoud sakin baki sukayi suna kallonta …Abba kuwa dariya ta bashi ..wae Goat da cow da chickenks .
..
Hanne Manya...!! ...ya fada lokacin da yake kallonta ...
Mahmoud yace ” Abba da yaushe zaa tafi ?…fuska daure
Gobe Mahmoud ….ya bashi amsa …
Ke !! …ki shirya gobe da safe zamuje kauyenku!!!,…ya mike ba tare da ha sauri kowa ba ya shige daki …
Momy kuwa cewa tayi .” Allah ya kyauta ..” ..sannan ta mike ta fada kitchen itama …
••°°••
Maman Huda na tsaye tana goge goge .. Barister Shehu ya fito daga daki fuska daure ….ya zauna bisa kujeran da take kallonta …
Malama …daga yau karki kuma zuwa aiki nan gidan an sallameki !!!!…ya fada tare da daukar remote yana latsawa ..
Maman Huda tayi sararo tana kallonshi cike da mamaki kafin ta danyi murmushi tace .,.” Lauya wani abu ya faru kuma ?…
Lokacin da nace kizo ki dinga taimakawa Hajiya kin tambayeni dalili? …ya bata amsa yana kallonta …
"To ....Me yayi zafi Haka lauya ? ..."bara na samu Hajiyar idan wani abu nayi mata sae na bata Hakuri "...
Ba sai kinzo ba …!!..gani nan fitowa ….hajiya ta fada lokacin da take fitowa da part dinta …
Sannan ta ci gaba …” Da kike son zuwa gurina …dama ni daukeki aikin ? …ina jin Shehu ne .. kuma yace ya sallameki to meye na sauran magana ? …
Maman Huda tayi tsaye rike da tsumma tana kallonsu …a iya saninta babu wani abun da ta aikata ba dae dae ba …ta ko don Saadatu ta daina zuwa ne? …ta tambayi kanta arai…
Tace “Kuyi Hakuri Hajiya idan dan saadatu ne wallahi har ga Allah bani na hanata zuwa ba ..!! …
Wake maganar sakaran yarinyarki yar iska…!!! …Hajiya ta katseta tare da zabga mata uwar harara …
Yar iska ….?…ta fada lokacin da idonta ya ciko da kwalla …
Eh Yar ‘iska matsiyata …barister Shehu ya bata amsa …
Wallahi diyata ba yar’iska bace sae dae kaine dan iska …arziki da talauci duk na Allah ne …!!!ta basu amsa a fusace …
Bata rufe baki ba Hajiya ta dauketa da Mari tana fadin ..”Allah ya mana katanga da talauci …fice mana daga gida tun kafin na saka a futa dake …bara kizo har gida ba kina kiran dana dan’iska na zuba maki ido ba ….kama hanyar akurkunki tun kafin na sakashi ya maki shegen duka gurinnan…
Allah ya baku Hakuri …Abunda ta fada kenan tare da fitowa daga gidan ….ko gabanta bata gani sossae har ta isa gida …
Ganin yanayinta ya saka Yaya Saa tayi saurin kamota tana tambayarta lafiya..
Lafiya mama …me ya faru ?..me suka maki..?…ta tambaya a rude …
bata boye mata komae ba ta fada mata duk irin wulakancin da Barister Shehu da hajiyarshi suka mata …daga saa har Maman kuka suke kamar ransu zai fita ..