A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hanne tace ” haba yaya me zaka saya a wannan karamin gurin dan Allah? wallahi ba girmanka bane …!!
Feedohm????
???????? A DALILIN YAYATA????????
????
HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
Na Feedohm????
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITER’S…
27 to 28
Dan juyo yayi kadan yana kallonta cike da mamaki kafin yace " banda wani girma Hanne ..sae dae ke nake tunanin girmanki yakai diyar sarki a babban kauyenku !!!
tasan magana ya fada mata sae ta kulle bakinta tayi gum ….har suka isa gida bata kara magana ba ..bareshi da ba kowa yake kulawa ba …
Gidan ya dan nunnuna mata sannan ya shige dakinshi ya barta hangame da baki …
••°°••
Da kyar Yaya Sa’a tayiwa Mama bayani ta yarda …ranar tace su tashi suje gidansu Barister Shehu ta fada ubanshi wata kila shi ya sauresu a bi masu Hakkinsu ….
Da Mama da Yaya Sa’a sae Huda suka tafi …cikin saa a harabar gidan suka iske su duka ukun tsaye da alama wani guri zasu ….sae sojojin dake tsaye cirko cirko
Hajiyar na ganinsu ta daure fuska tare da kallon Shehu ….Mama ta iso ta gaida Alhajin …tun yarda ya amsa mata gaisuwar jikinta yayi sanyi …
Tace ” Alhaji nazo na sanar dakai abunda ya faru .” ..
A wulakance yace “ina saurarenki” .
tace ” Alhaji mu talakawa bamu da komae sae Allah …ni da diyata muna zuwa aiki anan gidan …sae Shehu ya haye mata har ya mata fyad’e …shine nazo na fada maka ko akwae matakin da zaka sauka “
“Bullshit kauyawan banza da wofi!! ….matsayita!! sae uban me dan yayi Raping dinta ….kanta aka fara raping koko kanta aka kare ….? ..Kai Shehu ko yanzu kake bukatar Yarinyar nan …na yarje maka kayi abunda kake so da ita ….gidan ubanka suka shigo .,
..basu isa su wulakanta me ba har gida…!!!
"Dat my dady "....ya fada yana aika masu wani irin matsiyacin kallo ...!!
Dad din yace ..”.Guard !!….ku fitar man da wadannan matsiyatan ku bar waccen …!!! ya nuna yaya Sa’a …
Da saurin Mama ta rugumeta tare da janta da gudu zasu fita daga gidan …amma kafin su fita wani daga cikinsu ya fizge yaya Saa tare da tura mama da karfi waje ….haka ya dauki Hudar ya wurgota waje tana ihu tare da turje turje …..
Mama kuwa kwanciya tayi kasa tana birgima lokaci guda numfashinta ya fara sarke mata ….sam Huda bata lura da halin da mama take ciki ba …tana jikin Gate din tana kuka tare da buga kanta jikin karfen kamar ranta zai fita …
Yaya Saa kuwa ba shehu kadae ba harda guard din dake sae da yace duk mai bukata idan shehu ya gama ...ya bashi dama ....kadan daga cikinsu ne basu taba yaya Saa ba .....numfashinta har daukewa yake don azaba ...
sae da suka gama wulakanta ta sannan aka bude gate din aka jeho da ita kamar kayan wanki ….Huda tayi kanta ganin jikinta duk jini ..tana kuka tare da jijjigata ……
ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Huda ….fuskarta kamas babu alamun hawaye sae dae kurawa Huda ido da take tana kuka …..Inda mama take yashe ta kalla ….kafin ta ja jikinta ta isa gurin tana kallon fuskarta …
Ba tare da tace komae ba ta koma ta zauna kar ba mutun ba ….
Huda ta cakumo Yaya Saa tana fadin ..” Yaya saa me suka maki ? ….me suka yanka jikinki duk jini?….Me yasa bakya kuka ? …
Ba tare da tace mata komae ta nuna mata mama dake kwance a kasa ……gurinta ta nufa tana kiran sunanta …
Mama !!!…ga Yaya Sa’ar sun maido mana. …ki tashi ki ganta mama duk jini jikinta ban San me suka yanka ba a jikinta……ki tashi dan Allah ta dawo fa Mama ….!!! girgiza take tana kuka …amma mama ko motsi bata yi …
Liman din unguwar yazo wucewa ta gurin ya gansu haka ….yace ” Subhanallah Huda Me ya sami mamar kwance a kasa …”
“ban sani ba …taki tashine …kazo ka mata magana …yaya saa ki taso don Allah …!!!
Da sauri ya iso gurin …ya leka fuskarta tare da ja da baya …..”inna lillahi wa’inna ilaihir raju’un “…yake nanatawa …sannan ya tafi da sauri…
Jimawa kadan sae gashi da mutane ….ina suka dauki Mamar suna fadin wae ta rasu ….duk abunnan da ake Yaya Sa’a na zaune idonta na kallonsu …har sae da aka dauki mamar sannan Huda ta jata tana kuka suka tafi …
Kafin me …gidan ya cika tab da yan gaisuwa ….huda ke ta uban ihu amma yaya saa kukan ma yaki fitowa ….ita kanta so take tayi kukan amma ba dama
Feedohm????
???????? A DALILIN YAYATA????????
????
HASKE WRITERS ASSOCIATION????
( Home of Expert and perfect writers )
Na Feedohm????
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…
*_Main mera dil aurtum ho yana phir kyun ho palken ..????????..jhuka yein wahan ..???? Haske writers ..Ummy Aisha ..Hajja ..Asmy ..Ayusher ..Fatee ..Khaleesalat hydar ..Billy ..Nana diso ..Asy ..HOENPW????_*
29 to 30
Bayan sati daya ne barister Mahmoud yazo ganin jikin mamar ....Yana zuwa yaga ana addu'ar bakwae kofar gidan .. ...tambaya yayi me akeyi ...wani ya ce mashi Maman su Huda ce Allah yayiwa rasuwa sati daya kenan...
turus yayi ya kasa koda daga Kafa da k’yar ya samu ya dafa bango ya zauna a dakalin tare da tallabe kanshi da hannu biyu…
Yaya Saa kuwa ta bar magana da kowa ….Sannan duk wani namiji da yazo masu gaisuwa bata karba …sae ma ta janyo Huda jikinta ta hanata koda motsawa ….!!
••°°•••
Barister Mahmoud yana kokarin kawo masu taimako amma sam yaya Saa bata karba ….da taga yana kallon Huda zata fara kuka tare da rokanshi ya fitar masu daga gida dan Allah …!!!
Cikin dan lokaci abunda zasu ci ma ya fara gagaransu ....ganin basu da madafa yasa yaya saa fara wanki da guga da kuma dakau idan ta samu ...duk kokarinta na nemawa Huda kudin makaranta da abinci ...zata iya kwana biyu bata ci abinci ba ...amma bata barin Huda da yunwa ko ta mintu Biyu....duk wani aikin wahala da zatayi bata kashe ko sisi a jikinta sae dae ta kashewa Huda .....duk wani gurinta na duniya yana ga Huda !!.....ta dauki son duniya ta kara daura mata ...
Lokacin da cikinta ya fara girma sae ta fara fuskantar wulakanci gurin yaran Unguwa ..da Huda ta fita sae yaran su dinga tsokanarta wae yayarya tayi cikin shege …!!
Haka itama yaya saa da ta fita an dinga zind’enta ana gulmarta ….sae ma ta daina fita kwata kwata ….duk tayi bak’i ta rame …don Ma Huda ba kanwar lasa bace …duk wanda ya taba yaya saa bata kyaleshi sae ta bishi har bayan uwarshi ta duka …idan matar aurece bata kyaleta .. kan yaranta kanana take fanshewa don da sun fito waje zata kamasu ta doka ..yaran basu kara sukuni har sae matar ta zo har gida ta bawa yaya Sa’a hakuri…..
Ranar da Huda akayi masu hutu ta dawo daga makaranta ta iske yaya saa kwance bata lafiya …
” Yaya Sa ‘a ki tashi muje asibiti kinji ko …sannu ..ki ta masu Allah ya isa har su mutu ….!!!
Ganin ciwon ya dameta ne ya sakata tashi ta shirya suka tafi asibiti …
Bayan sunje ne aka mata aune aune sannan aka ce su jira result …suna zaune sae uban surutu Huda keyi ..nurse ta fito da result din tare da kiran yaya Saa office din …
banda “Inna lillahi wa inna ilaihir raju’un” babu abunda yaya Saa ke furtawa …wae HIV ni Sa’a …. ….Juyar da kanta take ta rasa inda zata sakashi …
tun likitan na kokarin mata bayani har ya fuskanci sam bata cikin hayyacinta …Huda ta fado office din da gudu …tana fadin ..
“Yaya Sa’a ki fito mu tafi mana ….kin zauna sae surutu suke maki wae Har da fadin kina da HIV ..dan Allah ba sae ki godewa Allah ba …ni da ko ABC ban dashi ya to zanyi …ki tashi mutafi …dan Allah” ..
Zuba mata ido doctor din yayi tare da fadin “Sister baraka …ki fita da wannan yarinyar mu karasa maganar tukun”…
Yaya Sa’a tace ” kubarta …itace rayuwa duk abunda ya sameni tare muke bakinciki …na sani ko batayi yanzu ba gaba sae tayi bakincikin da yafi wanda nayi yanzu…ku kyale ta …ku kyale man Hudata …!! …idonta ya ciko da kwallah ..
Da sauri Huda ta kalli doctor din tare da zabga mashi harara tana fadin .." ku mazan nan mugayene ..me yayata ta maku da duk lokacin da ta ganku sae tayi kuka ...ba ku sonta ne? ....tashi muje Yaya sa'a ki bar kuka kinji ko .. Ni kadae ke sonki yayata kuma duk wanda ya cuceki baran taba kyaleshi idan na girma ...!!! ..hannu ta saka ta share mata hawayen tana kallon likitan ...
Hannu Yaya Sa'a ta fizga da karfi suka bar office din ...yarda take jan Yaya Sa'a sae ka dauka itace yayarta ....
Yaya Sa’a in tsaida mana Okoda mu hau ?…
Cikin Kuka tace ..Huda banda kudi okoda.. ….kin gaji da tafiyar ne ? …
Daga kafarta tayi tare da nunawa Yaya sa’a tana fadin..
” lokacin da kika shiga gurin likita na taka kwalba …ban iya tafiya Sossae Yaya Sa’ata …
kanta ta dafa tana fadin …”Sannu kinji Huda ….”.
kafin Huda ta amsa Yaya Sa'a ta sab'eta ...duk da uban nauyin Huda ga kuma ciki sannan bata lafiya haka ta kaita gida ...sannan ta shinfideta saman katifarsu ...
Nan da nan ta hada wuta ta zuba ruwan zafi ta dafa…ta gasawa Huda Kafa ….Duk irin rakin Huda Shiru tayi ganin Hankalin Yaya Sa’a ya tashi sossae …..
Tunda akace Yaya Sa’a nada HIV sauran farincikinta da ya rage mata ya tafi ….bata da aiki sae kuka ….sannan bata gaza ba gurin neman kudin da zata biyawa Huda Makaranta ba ….
Barister Mahmoud kuwa kullun kokarinshi na yarda zai taimaka masu amma duk a banza …don da Yaya saa ta ganshi zata tura Huda daki ta rufo ta dawo tana hadashi da Allah ya tafi ya barsu ….bama shi kadae ba duk wani namiji bata kaunar taga ko kallon Huda yanayi …
••°°••
Feedohm????
???????? A DALILIN YAYATA????????
????
HASKE WRITER’S ASSO????
( Home of expert & perfect writers )
Na Feedohm????
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS..