A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

A DALILIN YAYATA COMPLETE HAUSA NOVEL

 *_Assalamu Alaikum ...wadanda suka man magana da dadewa akan na bude masu GRP nace masu banda ra'ayin haka ...to Alhmd na bude maku saboda wasu  dalilai ...idan har yanzu you're interested sae Ku sake man magana????????????????_*


 *_Jaane kahan Keene pehesr zyada ..QUEEN MERMUE..NAFEE ANKER ...AMNOOR ...FEEDOH CLASSIC...AUNTY SIS ..MUM FATEEY ..SALAMATUN INNA ...AOH????_*

31 to 32

   Huda ..!!! Ya Kwala mata kira dae dae lokacin da yayi parking a bakin gidansu ...

Ta juyo tana kallonshi kafin ta koma da gudu ta janyo kofar gidansu ta saka dankwalinta ta kulle kofar ta dawo gurinshi tana hararanshi ..

“Wae kai ina zuciyarka take ?

Kirjinshi ya dafa yana murmushi …”Tana nan Huda !!

baki ta tabe tana fadin ..”ni na dauka baka da ita …banda k’wak’wa kullun yaya Saa na fada maka ka daina zuwa gidanmu amma sae ka janyo wata motarka kazo kana washe baki …”

Murmushi yayi ba tare da yace mata komae ba …

“bara kayi magana ba …to Na rantse maka da Allah duk ranar da ka kara zuwa ka saka Yayata kuka sae naje har gidanku na saka Yayarka kuka itama ….

Zagayowa tayi tare da bude Marfin motar tana fadin…”Zo ka shige ka tafi ko na maka rashin mutunci ….!!

zuwa yayi kamar zaya shiga sae kuma ya hade hannayenta guri guda ya dagata ya daurata saman motar tare da dungure mata kai yana fadin …

“Bakya da kunya ko Huda ..? ..ni zakiwa rashin mutunci ? …ya hade fuska

Daga kasan kafafuwanshi ta fara kallo har zuwa kanshi ..saman ta hadiyi miyau da kyar tana kallonshi …ganin tsoro ya bayyana a fuskarta ya sashi sake daure fuska yana kallonta …

“Ni zaki wa rashin mutunci nace maki ?

“Allahu” …ta juyar da kai kamar saliha …dariya taso bashi yarda take zare idanu ga fuskar bayin Allah da ta koma ..amma ya dake yana kallonta
.

"Oya ...yiman rashin Mutuncin nace !!

“To dan Allah idan nace kayi Hakuri fa ? …ba sae ka saukeni ba na tafi gida …sannan kullun kazo ni kuma na dinga gaidaka ….saukeni ka gani yarda zan dinga maka …”

Sake mata hannu Yaya tare da ja da baya …tsalle tayi ta dira kasa tana washe baki …sannan ta hade hannayenta guri guda ..

“Kafana ma k’aikayi take man ….bara na sosa kaji ? …ta fada tana kalloshi tare da murmushi ..

Dukawa tayi tana sosa kafar tata …ta dago a hankali ta kalleshi taga hannusa a harde kamar ba ita yake kallo ba …da sauri ta rarumi kafarshi da niyar ta kadashi kasa …amma sae ji tayi kamar icce ko alamun yasan abunda take baiyi ba ….

Ta dago tana hararenshi suna hada ido ta washe baki tana kakkabe hannu .”Har ga Allah ni bama niyar kadaka nayi ba ” …

kafin ya bata amsa ta …ta bar gurin da gudu ….dariya yayi ya bude boot din motarshi ya fito da kayan abincin da ya zo dasu …sannan yayi waya …wasu mutane guda Uku sukazo mata…ya basu kayan abincin sannan ya shiga motarshi ya tafi …

Matan suka saka yara tare da daukar masu kayan abincin suka kai cikin Gidansu Huda …yaya Saa na zaune tsakar gida taga yaran suna ta shigowa da buhunna …bude baki tayi tana mamaki …kafin tayi magana taji Huda na fadin ..

“Wallahi yaya Sa’a ko kayan waye wannan bara mu bashi ba …tashi mu kaisu Daki mu boye tun kafin maisu ya shigo nema …Dan Allah Yaya Sa’a tunda muma an taba yi mana fashi ba sae mu rama ba mu dauke kayan ….

Kafin ta rufe baki Matan sun shigo ..tsalle daya Huda tayi tare da tara hannu tana kange kayan tana fadin ..

“ba Wanda ya isa ya daukesu tunda bamu mukace a shigo mana dasu gida ba …”

Wata daga cikinsu tayi murmushi tana fadin …dama ai naku ne Diyata …daga gidan marayu muke aka baku Taimakon da ake yiwa Marayu …

Murna kamar me gurin Yaya Sa’a …godiya ta dinga masu har da kuka …bayan sun tafine Huda ke cewa …

“Yaya Sa’a mu dafashi duka idan mun ci sai mu aje sauran …yarda ko wadannan barayin sun zo bara su iya dauka ba …kinji ..”

Yaya Sa’a tace …Huda ba yarda za’ai mu dafa shi duk kinji ko …idan ma sun zo sun dauka Allah da ya bamu wannan zai sake bamu wani !!!!

••°°••

Huda na JS2 ..cikin Yaya Sa’a ya cika wata tara …ranar kasa bacci sukayi …Tun cikin dare take nakuda ..Huda ke ta mata fita tare da Sannu ….ana kiran asuba ta fita da gudu ta kira liman tace yayanta bata lafiya …

Tare suka dawo cikin gidan ..lokacin Yata Sa’a ta wahala sossae ko Bude ido bata yi ….Banda Kuka babu abunda Huda ke yi …har aka dauketa aka tafi da ita asibiti …

Basu isa asibitin ba Yaya Sa’a ta rasu saboda deep labour din da tayi sannan jininta duk ya fita sossae …

Tana ganin an juyo zaa dawo ta rike hannun liman din tana fadin

“Dan Allah karmu koma …bata lafiya sossae ko magana bata iya man …duba liman yayata idonta ya rufe …dan Allah mu tafi asibiti …ina sonta …karmu koma liman ..wallahi da munje asibiti zan fita nayi bara na samo kudin sae na bayar da kudin …ni bana so tasha wahala .!!!…ta fada jikin yaya saa tare da fashewa da kuka …

Duk wanda ke motar sae da yayi mata kuka …ko da suka isa zaa fitar da yaya saa daga mota kin sauka tayi daga jikinta sae dae aka daukesu tare …

Bayan an aje ta ne Zaa Mata wanka liman ya rugumota jikinsa …ya ma rasa me zai ce mata …ya tabbata duk wanda ya hana Huda kuka ya cuceta !!!

Tana jin wani na fadin Ta Rasu ne …tayi sauri fizge kanta daga jikin liman tana fadin …Ta rasu kamar Mamata????..Barata dawo ba?.

Da Sauri Liman din yace ...bata rasu ba Huda !!! ..

Hannushi ta kama tare da daurawa jikin Yaya Saa tana fadin …

“Yauwa Liman …to tadata …kace mata Hudanta na kuka..bata son kukana fa …nasan zata tashi .liman ka tadata Dan Alllah !!…yaya Sa’a tace fa …kace ta tashi’ ko kukan ta ma naji zanji dadi …Dan Allah ki tashi …!!

Da kyar liman din ya fita da ita daga dakin yana kuka …..babban tashin Hankalinsu yarda zasu fitar da gawar daga gidan ba tare da Huda ta gani ba …!!! …

NO WAY OUT …Haka suka dauko gawar Yaya sa’a ..lokacin Huda na jikin Liman a waje tana kuka…kowa ya tabbata da tayi rashi …RASHI BABBA !! …wanda babu wani mahalukin da zai maye mata gurbin Yaya Sa’arta !!!!

Ganin tana kokarin tashi ya saka liman din riketa gam a jikinshi ….

Kamar mai bacci take fadin.. “kace kar su tafi man da yayata!!…ina sonta ita kadae gareni …Liman kaga ko Lauya shine ya ma Yaya Sa’ata Hard’e! …mukaje gurinsu suka kara yankar naman jikinta …sannan suka wullota …Mamana ta rasu saboda Hard’e …yaya Sa’ata ma ta rasu sabodashi …Liman nima din ina so in masu Hard’e …da lauya da babanshi da hajiyarshi ..zaka rakani ?

Ganin ba cikin Hankalinta take ba …sannan idonta a rufe yake ! ya sashi ..cewa “Zan rakaki kinji Huda !! ..”Yaushe zamuje ..?

Yanzu !!!…ta bashi amsa tare da rufe idonta ..bai kara ce mata komae ba sae addu’a da ya dinga tofa mata…

*_JUST THE BEGINNING....????_*

Feedohm????

???????? A DALILIN YAYATA????????

               ????

HASKE WRITER’S ASSO …????
( Home of expert & perfect writers )

Na Feedohm????

DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITERS…

33 to 34

      Tun daga lokacin Huda bata kuma magana ba ...kukan da takeyi ma ya tsaya cak ...sae ajiyar zuciya da take saki lokaci zuwa lokaci ...da marece Liman ya tafi da ita gidansu bayan kowa ya watse ....

Bata iya bacci ba .. ta riga ta saba a jikin yaya Sa’a take bacci kulun amma yau ita kadae bisa katifa …juyi ta dinga yi …da ta rufe idonta barister Shehu take gani yana kallonta …sae ta kai hannu zata kamashi sae ya sille mata …

Ranar ta Hudu ce bayan an dawo daga masallacin juma’a aka tsaya za’ayi addu’ar bakwae …

Lokacin Barister Mahmoud shima daga masallacin ya biyo ta gidansu Huda yaga yarda suke ….mutane sun taro sae addu’a ake ..

Huda kuwa na zaune gefe guda ta daura kanta saman guiwarta …yana gama parking ko fitowa baiyi ba ya kura mata ido tare da kiran sunanta ..

Hudallah!!!!!

Hankalinta baya duniyar gaba daya bata man san da zuwanshi ba bare ta san yana kiranta …..ganin bata da niyar kallonshi yada shi fitowa daga motar . ..

Har yazo gabanta ya tsugunna bata sani ba …sae da ya tallabo kanta sannan takalleshi da idanuwanta da sukayi jawur …

" Hudah ....menene ? ..idonki ke ciwo?...ya tambayeta a hankali ..

Kamar jira take ta fada jikinshi tare da sakin kuka ….duk ya rude yana tambayarta …

Lafiya Huda? …menene? fada man kinji ?…wani abu ya sami yayarki ?…Shiii yi shiru mana ki man magana please ..!!..ya fada a rude …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Leave a Reply

Back to top button