NOVELSUncategorized

A GIDANA 11

Haske Writers Association馃挕

Shafi na Goma Sha Biyu
聽 Tana tsaye a dakinta rike da wayarta, tana duba agoggo, anya ta zauna anan bayan abinda yake kokarin faruwa a dalilinta ne?


Sadiya na zaune a falo duk motsin datai idan Nabila akanta, wanda har ta daure tace “Lafiya?”

 Nabila tace “lafiya kalau tunani nakeyi.”

 Sadiya ta dauke kai, yanda tai da kanta ne yasa Nabila ta kalleta har zatai magana sai ta fasa, jin an bude gate ne yasa Zainab ta fito daga dakinta.

 Muryar Nusaiba taji tace “ashe Uncle ne.”

 Nabila tace wani uncle din tunda ke Uncle din naki biyu ne? 
Nusaiba ta harareta tare da juyawa ta dawo ta zauna.
 Nabila tasa dariya tace “Uncle din Aunty ne kenan, da dayan ne da munga fuskarki tafi haka.”

 Zainab kam Adam na shigowa bakin kofa tace “Honey dan zo.”

 Gabansa ne ya fadi, gaban Goggo ma ya fadi, a tare suka kalli Sadiya wacce ke zaune yanda suka barta, kallan Goggo yai wacce ta bugamai kallo ta mai alama da ka gani ko?

 Adam ya kalleta yace “inzo?”

 Tace “eh”

 Sadiya ya kara kallo sannan ya nufi daki, a tsaye take hankalinta a tshe, a bakin kofa ya tsaya tace “shigo mana.”

 Gabansa na faduwa ya maida kofar sannan ya kalleta yace “lafiya?”

 Yi maganar cikinsanhin jiki, kallansa tai tace “meya cema? Yana ina?”

 Ajiyar zuciya yai yace “na kira bai dauka ba, amma wai lafiya?”

 Tace “sake kira.”

 Kallanta yai sannan ya hau kiran Khalid, sai data katse ya sake kira sannan Khalid ya daga.

 Alama ya mata da an daga sannan yace “Khalid kana ina ne haka? Zai……”

Hannunta ga harde tamai alamar X kenan karya fada, Khalid daga can yace ” yanzu zan karaso, ina kan babban layi.”

 Adam ya kashe tare da kallanta yace “yana hanya, wai meke faruwa ne?”

 Kallansa tai kamar zata fadamai sai kuma tai shiru, tace bakomai.

 Shiru tai tana kallanshi a ranta tana cewa “honey am sorry, banso kaima ka shiga fargabar da nake ciki, in na san abinda ke faruwa na sanar maka.”

聽 Menene?

 Murmushi tai tace “Honey sai naga Sadiya?”
Yace “eh wlh dazu kin fita sai gata, kinsan ta dade tana damuna akan tana san zuwa.”

 Zainab tace ta kyauta, dama su Nabila zasu tafi gobe da safe sai ta koma dakinsu.”

 Da sauri yace “ai itama jibi zata tafi, ta zauna agun Goggo.”

 Fuskarta dauke da mamaki tace “jibi kuma?”

 Yace “eh makaranta ta samu anan Northwest ne ko Buk? Shine tazo registration.”

 Hannu tasa tadan bigi kafadarsa cikin wasa tace “ko kunya wai kake cewa ko nan ko nan, gobe zata registration din kenan?”

 Yana dariya yace “eh.”

 Tace “kuje tare zan turo ma kudi, ka tambayeta nawane kudin.”

 Kallanta yai cikin jin dadi sannan ya jawota jikinsa yace “Honey na gode sosai.”

 Murmushi tai tace “Kanwarka ce, da ita da su Nabila daya suke.”

 Dan huce yai kadan sannan yace “nagode Honey.”

 Dagowa tai t kalleshi sannan tace ” naga bata saki jiki ba, ko dan farkon zuwanta ne?”

 Yace “ai dama ita magana bata dameta ba sosai.”

 Tace “wa?” Sadiyan taka da kake cewa tana damunka da tsinaniyar magana?”

 Wata dariya yasa sannan yace “Sadiya kam akwai surutu kila dan bata taba zuwa bane”

 Jin karar bude gate ne yasa ta fito daga dakin, Adam ya biyota.

 Goggo ce ta kalleshi da sauri dan tana zaune a falo ko kayanta data anso bata je ta ajiye ba data anso.

 Ganin yanda ya fito fuska a sake ne yasa tasan ba abinda ya faru, nan ta mike ta nufi daki.

 Sadiya Adam ya kalla yace “Sadiya kiyi godiya Auntynki ta biya miki kudin makaranta.”

 Sadiya ta kalleta tace “Aunty nagode Allah ya saka da alkairi…….” hawaye ne suka zubo mata, Zainab zatai magana Nusaiba tai tsale tace “My yaya ya dawo.”

 Zainab ce ta wuce waje, Adam ya kalleta kawai sannan ya kalli Sadiya dake hawaye ya xauna akan kujerar dake kusa da ita yace “kukan na meye?”

 Kallansa tai tana share hawaye tace “na rasa me zance ne.”

 Murmushi yai yace “to kinyi ya isa haka nan, kai ta daga alamar to.

 Duk maganar a hankali yakeyi, dan dama Nabila bata falan yanzu da alama ta shiga daki, ita kuma Nusaiba na jikin window tana kallan Khalid.

 Zainab ce ta fito ya rufe motar kenan ya goya jakarsa, juyowar da zaiyi taga gefen bakinshi na jini.

 Idanu ta zaro hankali a tashe ta matsa tace “lafiya?”

 Kallanta yai,tace “su sukama?”

 “No ba wani abun, zan wuce sai gobe da safe in Allah ya kaimu.”

 Ya mata sallama yana neman wucewa, da sauri tace “meyasa suka dakika bayan ba kaine da kaifi ba?”

 Baisan sanda ya juyo ba, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa har ya juya kuma sai ya kara juyowa yace “Ko am sake kiranki karki daga, inso samune ma kiyi blocking din number.”

 Batace komai ba, sannan yadan murmusa kadan yace “sannan ba dukana akai ba, sai da safe.”

 Ya fita, yana tafe yana cewa wai ka bari aka dakeka sai kace wani yaro, shiru yai yana tuno abinda ya faru.

 Ko garin Zaria bai kai ba ya fahimci suna binshi a baya, hakan yasa ya gangara gefen titi yai parking din motarsa, suka karaso sukai parking kusa dashi.

 Fitowa sukai suka zagayeshi ganin ba kowa a motar yasa ransu ya baci.

 Babba ne ya kalli Khalid yace “ina take?”

 Khalid yace “wa kenan?”

 Cikin masifa yace ” ina take?”

 Khalid yace “wanda ya turoku bai fada muku ba a wannan motar ta taho ba?”

 Wannan kalma ta hasala su hakan yasa bai an kara ba yaji an makeshi wanda yasa shi ya fadi, har gefen bakinsa ya fashe.

Dagowa yai rai a bace yace “me kenan?” Wnda ya nausheshin yace “kana tunanin tsoranka mukeyi?”

 khalid ya goge gefen bakinsa sannan ya make wanda ya bugeshin, shima gefen bakinsa ya fashe, hannunsa dayamai zafi gun naushin yadan yarfe sannan ya kallesu yace ” na kira police na tabbatar sun kusa isowa yanzu, in munje police station ma karasa maganar acan.”


 Jin zancen police ne ya sa suka kalli hanya da sauri, babban yace “mu zaka rainawa hankali?”

 Khalid yai murmushi yace “dan Allah kar ku tafi, dan nafiso muje police station din a dau mataki akan ku.”

 Cikin yaran nupe dayan ya fara mai magana, anya ma tsaya? In aka kamamu fa an kama
Banza?”

 Khalid ya kalli Ogan yace “bani wanda ya aikoku a waya muyi magana dan daga yanda wayarka ke kara tun dazj nasan shine”

 Ogan ya kalli Khalid sannan ya zaro wayar yana neman dagawa Khalid ya warce.

 Dayake jin ogan yai sanyi yasa bai kwace ba, sai leka titi suke.

 Khalid ya daga wayar yana ji akace “kun biya bukatar taku? Na fada muku ai xsku sha romo gans kudi ga na can ciki.”

聽 Khalid yayi mamakin jin wannan kalamai, yace “ohhhh am really sorry amma abinda kake neman yiwa matar aure bazai taba faruwa ba.”

 Jin haka ne yasa yace “waye kai?”

 Khalid yace “wanda yasan daraja da mutuncin mace!”

 Waye kai? Uban waye kai?”

“Ka shirya zuwa police station dan yanzu za’a tafi da yaranka, kaga lalatar daka nemi yiwa yarinya sai ya bayyana a idan duniya.”


 Hankalinsa ya tashi, wanda Khalid ya mikawa Ogan wayar da gudu suka shige mota suka arta a guje.


Ran Khalid ya baci dayaga haryanzu ba alamun yan sandan daya kira, idanu ya rufe tare da yin karamin ajiyar zuciya, nigeria kasata abinda ya fada a fili kenan tare da murmusawa, yanzu da itace aka kama har a gama lahanta mata rayuwa ba wanda zaizo cetanta.

 Ransa ba karamin baci yai ba ganin ya dade a gun yan sandan basuzo ba yasa ya juya ya bar gun.

 Yana tafe kalaman mutumin nan namai yawo, wani irin rashin imanine wannan? Kai laifi dan an hukuntaka sai ka nemi hanya mafi muni kace dashi zaka rama.

聽 Wayarsa ce聽 ta hau kara wanda ya dawo dashi daga tunanin dayai, ganin Adam ne yasa ya daga dan dama so yake ya kirashi.

 Adam yace “Khalid ka wuce ne?”

 Yace “yanzu zan hau mota naga magrib tayi.”

 Adam ya kalli Zainab da ta wasie tana dadana tablet dinta yace “ka dawo ka kwana anan dan Allah kaga dare yayi.”

 Khalid yace “karka damu yanzun nan zakaga na isa gida.”

 Adam yace “yau dai kadai yanda kasha doguwar tafiyar nan ka zo ka kwana anan.”

 Yace “to zan wuce gidan kawuna na kwana acan.”

 Adam yace “shikenan.”

 Har zasuyi sallama yace “Adam.”

 Adam yace “naam”

 Yadanyi shiru saboda baisan yanda zaiyi yace mai karyabar matarsa ta dinga fita ita kadai ba, daurewa yai yace “ai kun shiga gida kenan ko?”

 Dariya tambayar taba Adam yace “eh.”

 Khalid yace “to shikenan sai da safe.”

 Nan sukai sallama ya dan sosa kansa na jin haushin yanda yai tambayar.********

Kallan Zainab Adam yai yace “yace a’a”

 Tace “me?”

 Yace “kikace wannan abokin naka ya kwana anan mana tunda tafiya mukai doguwa.”

 Ta sa dariya tace “wai dan nace haka ne ka kirashi? Tab lalai Honey kaima.”

 Tana kaiwa nan ta mike ta shiga toilet.

 Tana rufe kofar tace dan an tausaya ma shine zaka wulakanta mutane? Kai ta tafiya din kafi ruwa gudu…..Harya kwanta yaji kishir ruwa ta dameshi, mikewa yai ya fito a hankali ya nufi kitchen.

 Ruwa ya dauko a fridge ya fara sha, daga gefe yaji kamar a na nufo kitchen din, da yake fitilar wayarsa ya kunna kawai ya haske wanda ke tahowa.

 Sanye take da vest dinta sai zani data daura, ganin shigarta ne yasa yai saurin sauke fitilar tare da maida fridge din ya rufe.

 Nabila dan haskamin hanys zan fadi dan Allah.

 Abinda ta fada kenan cikin sanyin murya.

 Adam ya haska mata hanya sai dai bai san sanda yake kara kallanta ba, harta karaso.

 Kusa dashi ta tsaya wanda hakan yasa ya haska kansa yace “nine ba nabila ba.”

 Tace “Yaya baka kwanta ba?”

 Yace “na kwanta ruwa naji ina san sha na taso.”

 Amma ki dinga sa hijab in zaki fito, ko bakiga da maza a gidan ba?

 Ta kallesh tace “kai kadaine a gidan yaya, sannan bansan zan ganka ba, ga zafi nakeji, na kuma san kai ba masu halin banza bane.”

 Murmushi yai yace “hakane.”

 Sha ruwan zan tafi na kwanta.

 Tace to nan ga fara shan ruwa, a zabure tai tsale ta matsa inda yake ta kankameshi kam jikinta na kyarma.

 Hankalinsa a tashe yace “Sadiya Sadiya menene?”

 Kyarma jikinta kawai yakeyi gashi ta matseshi tsam, da kyar ya banbareta yana jijigata, har yana neman kunna wuta ne yasa ta farfado.

 A tsorace yace “lafiya?”

 Tace “abu nai?”

 Yace “eh yanzu kika kankameni.”

 Hawaye ne suka shiga zubo mata wanda tausayinta ya kara rufemai zuciyaaaaaaa

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button