NOVELSUncategorized

A GIDANA 10

Haske Writers Association馃挕

Shafi na Goma

*Excuse me a Zauren BieBie nake? Excuse me nan ne Zauren BieBie?….*
Lol kuna sani Dariya da sarar nan, wannan shafin naku ne duka wadanda ke left da wandanda ke right….One Love*********

 Kanta ne taji yana juyawa yanda yake gudu da motar, ga hanyar sam batada kyau kallansa tai tana san mai magana taga ya ja motar sun shiga wata kwana a Zaria.

 Suna yin kwanar yai parking, ya fito daga motar ya rufe sannan ya dawo titi, sai a lokacin motarsu tazo da gudu suka wuce a tunaninsu sun wucesu ne.

 Juyowa yai tare da ajiyar zuciya sannan yai dan murmushi dai kace me aikin security.

 Karasawa yai jikin mota, ya bude sannan ya shiga juyowa yai ya kalleta, itama shi take kallo tace 鈥渇ada kukai?鈥�

 Fada? Ya fada cikin mamaki sannan yace 鈥渘i da banda laifi akan me zanyi fada da wani?鈥�

 Fuska ta hade tace 鈥渄a wa kake kenan?鈥�

 Baice komai ba sannan yasa key ya tada motar, idanta ne ya dan fito tace 鈥渋n kuma basu tafi ba fa?鈥�

 Yace 鈥渟ai muji me suke so.鈥�

 Haushi ya kamata batace komai ba, juya motar yai suka koma kan titi, suna fita daga cikin garin Zaria suka tadda motar nan a gefen titi, kallansa tai tace 鈥渟une?鈥�

 鈥淢e kika musu ne haka?鈥�
 Shiru tai batace komai ba sai tsoron abinda zai faru fa take.

Khalid yana zuwa kusa dasu suka hau kan titi tare da nunamai yai parking.
Khalid ya kalleta yace 鈥渟aura hour nawa?鈥�
 A hankali tace 2

 Bude kofa yai ya fita, kusa dasu yaje yana neman mika musu hannu suyi musabaha, babba cikinsu ya buge hannunsa yace 鈥渕atarcan zaka bamu.鈥�
Cikin mamaki Khalid yace 鈥渨acc kenan?鈥�

 鈥淜arfa ka raina mana hankali ta cikin motar can, ba Zainab Aliyu Tahir bace?鈥�

 Khalid ya kallesu yanzu kam ya gane aiki su akai basu mansan ta ba.

 Murmushi yai yace 鈥渨ai dama Zainab kuke nema?鈥�

 Eh, bamu ita.

 Dariya yai yace 鈥渂a ita bace, yayarta ce wannan sunan ta Zarah, baku ganta bane? Zo ku duba ku gani.鈥�

 Cikin mamaki suka karasa jikin motar, wanda ganin an nufota yasa gaba daya hankalinta ya gama tashi.

 Gani tai Khalid ya bude kofar wanda idanunta suka firfito shikenan ya zo ya bada ita, Adam, Nabila, rayuwata……..

 Muryar Khalid taji yace 鈥渒un ganta?鈥�

 Ido suka kura mata dayan ya kalli dayan cikin yaren nufe yake mai magana wai itace? Yace kamar ita kamar ba ita ba.

 Khalid yai dariya yace 鈥渉ala bakwa kallan program dinta ne amma da kuna gani zaku ganeta.鈥�

 Shiru sukai suna kara kallanta, Zarah wai sun dauka Zainab ce ke?

 Zarah? Me mutumin nan ke shirin yi? Ta fada a ranta cikin mamaki, murmushi yai yace 鈥渕un biya ta tv station ne saboda zamu koma kaduna inda muke da zama.鈥�

 Shiru sukai suna kara kallan Zainab.

 Khalid ya rufe kofar sannan ya kallesu yace 鈥渁mma me yayarta ta muku?鈥�

 Ba mutawa ba aiko mu akai, kasan inda take? Suka fada suna kara kallan pic din da aka turo musu, amma itafa ance yau zata kaduna sannan ya akai kuka hau motar da aka nuna mana tata?鈥�

 Khalid yai dariya yace 鈥渋ta ga wuce da ragowar staff din, saboda tana sauri dan 10 zasuyi meeting din, da tare zamu taho to mu bamu shirya ba.鈥�

 Yanzu kam sun dan yarda dan dama hoton ba yanzu tayi shi ba.

Khalid yace 鈥渒uyi hakuri dan Allah karku ma yayarta komai, bansan meya faru daku ba………鈥�
Malam karka soma mana wa鈥檃zi whve ka bamu gu, neman halak dinmu muke.

 Khalid ya shiga mota yaja ya bar gun.

 Zainab ta kalleshi tace 鈥渕e ya faru? Naga sun barmu mun wuce.鈥�

 Shiru yai kafin yace 鈥� i just trick them hope bazasu gane ba har mu isa.鈥�

 Ajiyar zuciya tai sannan ta sauke window dinta tare fa shan iska, shiru tai tana tunanin wanda ya aiko a kamata a cikin mutane sama da 8 data kora daga gun aiki daga sanda ta fara zuwa yanzu.

 Shiru tai tana tunanin ya akai yasan gana program? Sannan ya akai yasan basu ganeta ba? Ya akai yasan bazasu fahimci ita din bace?

Tadan kuramai ido tana tunanin lamarin.


Kauda kai tai a hankali tace 鈥淭hank You.鈥�

 kallanta ya danyi ta glass amma baice komai ba, yana tunanin me tama mutane haka?


************

 Kusa da Goggo ya zauna a falo cikin rada yace 鈥渢ana ina Goggo?

Harara ta makamai tace 鈥渁ika fini sanin inda take.鈥�

 Mikewa yai ya nufi dakin goggo, Nabila ta dago ta kalleshi amma bata kawo komai ba.

 Kofar dakin ya tura, a hankali saboda yana tsoron kar ya kwankwasa su Nabila dake falo suyi tunanin wani abin.

 Tana kwance a kasan katifa daure da zani sai dai zani ya sauko kadan wanda hakan yadan bayyana saman kirjinta, da sauri ya juya baya, sannan ya juya zai fita.

 Jiyai ance waye? Ta fada tare da saurin jan bargo ta luluba.

 Yace 鈥測ahkuri bansan bacci kike ba.鈥�

 Ya Adam? Ta fada cikin alamar tambaya, juyowa yai da sauri yace 鈥測a akai kikasan sunana?kin sanni ne?鈥�

 Kai ta girgiza da sauri tace 鈥渁鈥檃 jiya a gun Goggo naji tace 鈥淎damu.鈥�

 Ajiyar zuciya yai sannan yace 鈥渄ama fada miki zanyi daga yau zamanki a gidan nan sunanki Sadiya,sannan gobe zakiji ki gama registration dinki daga nan sai ki koma gida.鈥�

 Nagode amma me yasa zan boye sunana?

 Yace 鈥渕atar gidan batasan kina nan ba sannan ba dadi taga na kawoki bayan ban sanki ba.鈥�

 A hankali tace 鈥渒ayi hakuri, sannan nagode Allah ya saka.鈥�

 Murmushi yi sannan yace an jima zansa ki fito a matsayin zuwanki kenan ku gaisa da mutan gidan.鈥�

 Kai ta daga alamar fahimta, zan shigo miki da abinci, da sauri tace nagode.

 Murmushi ya sake yi sannan ya juya ya fita.


 Yana isowa falan Goggo tamai wani kallo sannan tace 鈥渟amin kati a waya ina san kiran mai dinki.鈥�

 Ba musu yace to.

 Nabila tasa dariya tace 鈥測au basa banba, Uncle baice wai Goggo meyasa katinki ke saurin karewa? Tai maganar cikin kwaikwayon sa.

 Dariyar borin kunya yai yace haka nakeyi?
Nusaiba tace 鈥渟osai ma.鈥�

 Suka sa dariya, Goggo ta kalleshi cikin jin haushi.

********

 Sun gama meeting komai ya tafi yanda take so, suna gama sa hannu aka kawo musu abinci, kallan mai ajiye musu abincin tai tace 鈥渄an kaima driver na yana waje.鈥�

 Okay tace tana gamawa ajiye musu ta dauko take away din da juice ta fito waje, ganin batasan motar ba yasa ta koma ta sanar mata batasan waye ba.

 Zainab ta amsa ta fito dashi.

 Yana zaune cikin mota yana karanta wani littafi a hanunsa, mikamai tai yana amsa ta juya ciki.

 Cikin mamaki ya kalleta yau me ya sameta.

 鈥淓x….Ina magana.鈥�
Baisan dame zai kirata ba.

 Hartayi gaba ta juyo ya nuna mata alamar na meye? Tace 鈥渁n ba kowa ne kaine ba鈥檃 gani ba.鈥�
 Ta fada ta juya ta koma.

 Sai kara jinjina ma Zainab sukeyi, suna kara nuna mata jin dadinsu nayin aikin da ita, daya daga cikin directors din yace 鈥測anda kike workaholic din nan ha mijinki yake?鈥�

 Murmushi kawai tai bata ce komai ba, dan duk yanda take da mutum indai aiki ne ya hadasu batasan harkar rayuwarta ya shigo ciki.

 Shima jin tayi shiru yasa bai sake cewa komai ba sai suka sako wani hirar…..


*Ayusher Muhd*
[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁

Haske Writers Association馃挕

Shafi na Goma Sha Daya

Wattpad/@AyusherMohd.


聽 Su Nabila na shiga daki Adam ya mike da gudu yai dakin Goggo, haushi ya turnuketa ta bishi da wata harara ta kaici tare da cewa “meye hakan?”

 Adam ya mata nuni da daki sannan ya ruga, kai ta girgiza tare da jan tsaki na takaici, kwankwasa mata yai a hankali, sannan ya tura, riga take sawa da sauri ya koma ya maida kofar ya rufe yana cewa ni bana tashi zuwa sai tana wani abin?

 Karasa sa rigar tai ta bude kofar tana kallanshi fuskarta dauke da murmushi.
 Kallanta yai yace “hakuri na bude kina shiryawa.”

 Tace “bakomai ai masan ba da saninka bane.”

 Yace “ki dauko jakarki ki fito a matsayin yanzu kika zo.”

 To tace ta juya da sauri ta dauko jakarta ta fito a gaba ya sata har zuwa falo, har kasa ta tsuguna ta gaida Goggo, Goggo ta kalleta tace “ni kin tabbatar sace miki jaka akai?”

 Kallan mamaki tama Goggo sannan ta kalli Adam, da sauri yace “Goggo wai meyasa kike haka ne? Bana fada miki ba?”

 Share hawayenta tai tace “kiyi hakuri.”

 Goggo ta kalleta a haka dai gata mutum sai dai itafa tana mamaki ace kaf garin nan ba wanda ya tausaya mata ba kuma wan……….”

 Adam ne yace “Goggo ki sake da ita kar Zainab ta gane wani abin.”
 Goggo ta maida kanta kan Tv harta fara kallo ta mike ta shiga kitchen ta dauko juice ta zauna tana sha tana kallanta.

 Da Adam da mai suna Sadiya wacce ko sunanta na asali bamu sani ba sukai shiru.

 Can Adam yace zauna.
 Zamanta ta gyara sannan ya kwallawa Nabila kira itada Nusaiba.

 Fitowa sukai gaba daya fuskarsu a hade.

 Adam yace “Rigimanmun mu ya akai?”

 Nusaiba ta turo baki tace “Dady yace gobe zai turo a daukemi.”

 Wani dadi ne y kama Goggo da Adam, wanda har Goggo bata san sanda tace “masha Allah hakan yayi dai dai.”

 Nabila ta kalleta tace “Goggo ai ba sai kin nuna murnarki a fili ba mun san dama dadi zakiji.”

 Goggo ta sa dariya tare da wayancewa tace “ba haka bane, ai zamanku a gidan yafimin dadi, ni da da nake zama ni kadai in Adamu ya fita? Yanzu kuwa kuna nan muna shan hirar mu?”

 Nabila dai bata ce komai ba, sai yanzu suka kula da budurwar dake zaune a kasa.

 Nabila cikin mamakin tace “wannan kuma fa?”

 Adam ya sa dariya yace “Sadiya ce yau tazo daga Kura.”

 Sadiya? Suka tambaya a tare

 Da sauri ya kalli Goggo yana mata nuni datai magana.

 Goggo tace “baku san Sadiya ba? Kanwar Adam ce ai mahaifinsu daya.”

 Kallan Goggo yai cikin mamaki, tace “Sadiya ga kannan Zainab ku gaisa.”

 Nusaiba ta kalleta tace “amma kinfi Uncle kyau kuma bakwa kama, da alama ke mamanki kikayo.”

 Murmushi tai, Nabila kam kallanta kawai take amma batace komai ba.

 Kallan Goggo tai tace “yau da wake zan dafa wlh.”

 Goggo tace “da dai ni kike dan kinsan bansan da wake.”

 Nabila tana dariya tace “sai kisa miya akwai ragowar ta jiya.

 Tana yin kitchen Nusaiba ta bita.

 Suna shiga Adam ya kalli Goggo yace “Goggo wani mahaifinmu daya?”

 Tace “to kana san nace mahaifinka da mahaifiyarta daya bayan bakwa ko yanayi? Sannan in tsautsayi ya kawo Sadiya nan kusa fa?”

 Sadiya tazo聽 nan tai me?

 Haka dai ka iya ko kunya ma bakaji, sau nawa tana ce ma zakato kana hanata?

 “To wai tazo tai me? Ni kinsan bansan takura.”

 Goggo tace “can kai ka sani, baka dauki na jininka ba gashi kana kinkimo da titi ai.”

 Sadiya tai kasa dakai, Adam ya kalli Goggo yace “wai Goggo meyasa kike haka ne?”

 Goggo ta dauke kai tana shan juice dinta ta cigaba da kallanta.

 Adam sai kokarin jan Sadiya da hira yake dan ta saki jikinta.


************

 Bayanta tadan buga saboda ciwon da yake mata, sannan ta mike ta musu sallama, nan kowa ya shiga jinjina mata suka fito ita da staff din da sukazo tare.

 Tana saukowa daga kan matatakalar da waje waya ta shigo wayarta, bata dauka ba saboda tana kara yin sallama dasu, suna karasa saukowa ya rage daga ita sai staff dinta ne, babban ya kalleta yace “Hajiya kinyi ba karya wlh.”

 Murmushi tai tace “sannunku da aiki kuma, thanks to you komai ya tafi normal.”

 Nan suka yi murmushin jin dadi.

 Inda motarta take suka nufa, bakowa a motar hakan yasa ta dan wawaiga, sannan tace “kuje ku hau hanya, maybe ya dan fita ne.”

 Ah Hajiya bari mu jira ki fara tafiya.

 Hira suka dan cigaba dayi jefi jefi take sa musu baki saboda bata fiya san yin hira fa na kasa da ita ba.

 Khalid ne ya hangosu daga nesa hakan yasa ya kara hanzari dan isowa, yana karasowa yace “kuyi hakuri nadan je Massalaci ne.”

 Kallansa tai cikin mamaki, yau meke kanshi harda bada hakuri?

 Zatai magana wayarta ta sake kara, nan ta dau wayar sai kuma ta kalli Khalid.

 Kallanta yai cikin mamaki, sannan ya kalli wayar hannunta wanda baya iya gani.

 Hello, ta fada tare da dan matsawa daga gun su.

 “Hajiya Zainab! Wato kin gudu ko?”

 Gabanta ne ya fadi tace “wanene?”

 Wata muguwar dariya ya saki yace “wanene? Tambaya ma kike?”

 Juyowa tai ta kalli Khalid, ganin haka yasa ya matsa kusa da ita, daurewa tai tace “mekake nema da ni ne? Koma wanene in dai har ya sanni na tabbatar yasan bana tsayawa maganar da batada amfani a waya, in kana da abin cewa ka tareni ka fadamin.”

 Tana kaiwa nan ta kashe wayarta tare da kallansa.
Are you akay?
Abinda yace mata kenan ta daga kai alamar eh, hannu ya mika mata yace muga number.

 Mikamai wayar tai ya karanta number sannan ya mika mata sawa yai a wayarsa sannan yace “ko zakibi wadancan ku wuce?”

 Cikin mamaki tace “why? Ni bana shiga motar da ba tawa ba.”

 Yace ” i think suna nan kar su kara biyo mu, sannan in mun samu mun wuce dazu yanzo ba abinda zamuce musu da zai sa su yarda.”

 Shiru tai kafin ta daure tace kai fa?

 Zan taho.

 Abinda yace mata kenan yai shiru, ganin hkan ne mafita yasa ta nufi gun staff din ta sanar dash zata bisu mamaki ne ya kamasu, duk da ba haka suka so ba dan sun san har su isa kuma bazasu sake ba.

 Harta bude mota zata shiga ta juyo ta kalli inda yake, in suka kamashi saboda ita fa?

 Anya hakan shine daidai?
Karta ja mai bayan bai san hawa ba baisan sauka ba.

 Kayanta ta ajiye a motar sannan ta dawo yana kokarin shiga motar,cikin mamaki ya kalleta.
 Tace “ba haka kawai nake korarsu ba, duk wanda na kora yayi abinda bai dace bane, wannan muryarsa tamin kama data Dauda wanda na kora shekara biyu da suka wuce, kamashi nai yana neman lalata yarinyar da tazo neman aiki.”

 Tana kaiwa nan ta juya harta isa bata juyo ba ta shige motar suka ja suka tafi.

 Shiru yai a gun kafin shima a ya shiga.


Sai wajen karfe shida suka isa garin Kano, gidsnta tace a wuce da ita, nan ta nuna musu suka ajiyeta, tana sauka sukai ajiyar zuciya a tare, sannan suka sa dariya.

 Ahhh so awkward.

********

Bala ne ya bude mata kallan sa tai bayan sun gaisa tace “Yana hanya, zai karaso.”

 To Hajiya dama na ganki ne a wata motar.”

Murmushi tai dan yanda ya kalleta dama tasan me yake nufi.

 Ciki ta shiga, Nabila da Nusaiba ne sai wata a falan.

 Mamaki me ya kamasu ganinta ta shigo, Nusaiba ta leka ta window da sauri, ganin ba mota yasa ta kalli Auntyn tata tace “Aunty ya haka?”

 Jakarta ta mika mata ta amsa Nabila ta amshi ragowar kayan hannunta, tana cema Nusaiba wato ke in zan fita ko in zan dawo ba mi kike nema ba ko?

 Dariya tai tace “ai ke Aunty tawa ce shi kuma, wanda zan aura ne”

 Nabila tasa dariya tace ” a ina zai aureki bayan baimasan kina yi ba?”

 Zainab ta karasa ciki, turus ta tsaya tana kallan abinda ta gani a falan ta, Nabila ta kalla wacce tai saurin cewa “Sadiya ce kanwar su Uncle.”

 Zainab ta kara kallanta, kasa tai dakai tare da saurin cewa “Aunty Ina wuni?”

 Zainab cikin mamaki tace “Sadiya?”

 Tace eh nice.

 Zainab tai shiru tana kallanta kafin tace “ya kura?”

 Sadiya ta kalleta tace “lfy kalau.”


 Zainab ta kara kallanta anya ita ta gani a bikinta?

Nabila ce ta kalleta tace “Aunty Menene?”

 Ciki ta shiga tana duba agoggo tare da cewa “ina Adam?”

聽 Ya kai Goggo gun mai dinki.

 Shiru tai tare da kallan agoggo, gata batada numbershi balle taji halin da suke ciki.

 Sadiya ta kara kalla tace “sai naga kamar kin rame.”

 “Na danyi rashin lafiya ne shiyasa.”

 Kai ta jinjina alamar fahimta sannan ta dau wayarta ta kira Adam.

 Yana ganin kiranta ya gyara murya yace “Honey.”

 Tace “Honey kun kusa gamawa?”

 Yace “yanzu muka iso, kinga Sadiya?”

 Tace “Eh na ganta, ka kira Abokinka kaji yana ina?”

 Ba tare kuka dawo ba?

 Eh ka kirashi in kaji ka fadamin.

 To ya ce ta kashe wayar, Nusaiba ta matso da sauri tace “ina Uncle din nawa yaje?”

 Wani uncle din naki kike nufi?
Dariya tai tace “to yayana?”

 Zainab ta girgiza kai kawai, kallan Sadiya tai wacce tai kasa da kanta.

 Taci abinci?

 Nabila tace “eh.”

 Zainab tai ciki, Nabila tabi bayanta.

 Juyowa tai tace “lafiya?”

 Nabila tace “Aunty kin tabbatar kanwar Uncle ce?”

 Zainab cikin mamaki ta kalleta tace ” me kike san cewa?”

 Nabila tace “kawai na gane basa wani hira.”

 Zainab tasa dariya tace “kinada matsala Nabila, to in ba kanwarsa bace wacece? Me kika dauki Adam?”

 Dariya tai tace “shirman nawa fa?”

 Zainab tace “da alama kam, ki cire abin nan a ranki kiyi rayuwarki yanda ya kamata.”

 Kai ta jinjina sannan tace “Dady yace gobe zamu wuce”

 Zainab tace “hutu ya kusa karewa ko?”

 Nabila tace eh.

 Murmushi sukai a tare Nabila, Zainab tace “a hakan ma na gode, dan in baku zo ba banaji zan dinga ganinki.”

Nabila ta matso ta rungume ta, Zainab tai murmushi mai tattare da ma’anoni kala kala.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button