NOVELSUncategorized

A GIDANA 15

Haske Writers Association馃挕

Shafi na Goma Sha Biyar

*Ayusher Muhd*
 Juyawa tai hankalinta a kwance ta shiga makarantar, hannu tasa a jakarta ta dauko wayarta wacce na gani daga mai touch ta koma iphone, baki ma sake ina kallan ikon Allah, number ta danna sannan ta fara waya.
Kana ina?

Kazo ina jiranka a northwest.
Tana kai nan ta kashe wayarta, maimakon ta shiga ciki wucewa tai gefen inda motoci suke ajiye tana dadana waya, batai minti goma ba sai ga wata mota nan mai masifar kyau ta karaso, budewa tai ta shiga sannan yaja suka bargun.
 Kallansa tai bayan sun fara tafiya tace “ina abin?”
Nan yasa hannu gefen kujerarsa ya ciro wasu takardu ya mika mata.
Amsa tai tana dubawa sannan tai tsaki sannan tace “tsaya.”
Nan ya ja gefen titi ya tsaya, kallanta yai cikin kaguwa yace “Booboo na muje hotel din plz, am in a hurry….” ya fada yana daure hannunsa akan cinyarta.
Doke hannun tai tace “sai yaushe zance ma ka barni na gama abinda yafi komai mahimmanci a rayuwata?”

 Kallanta yai jiki a sanyaye yace “kiyi hakuri, amma ya abinda kikeyi?”

“Haushi yasa ma abin baya birgeni, I didn’t expect him to be that easy.”

 Ta kalleshi sannan tasa hannunta a saman goshita ts kwantar da kanta kan kujera, wani kwafa ta saki wanda ya sashi shan jinin jikinsa yace “muje?”
Tace “kaini naci abinci dazu na kasa ci saboda wannan yar iskar yarinyar.”

 Yace “wacce?”
Tace “Nabila take ko wa? I hate that girl.”

 Murmushi yai yace “me kikesanci?”

“Kaini Cilantro Restaurant.”
Yace okay.

********************

聽 Zainab ce ta shiga cikin gida bude kofar falo tai, wanda yasa su kallan kofar.
Zainab ce ta shigo a tare sukace Aunty?
 Zainab ta kallesu tace “wannan kiran fa? Bakuso dawowa ta bane ko laifi kukamin?”

 Dariya Nabila tai tace “munji ba alamar karar gate ne bare na mota.”

 Da gudu Nabila ta tashi ta bude kofa, ganin ba mota yasa ta juyo da sauri tace “Aunty harya tafi?” Ta fada kamar zatai kuka.
Zainab tace “eh ya wuce yanada abinyi.”

 Zama tai a kasa dabas kawai ta sa kuka, Zainab cikin mamaki tace “menene?”
 Nabila ta girgiza kai tace ” malama dan jeki waje kiyi kukan asarar ki, mu dan Allah karki cika mana kunne.”
 Haushi ya kamata ta taso ta nufo kan Nabila, da gudu Nabila ta mike tai bayan Zainab wacce ta shiga tsakiyar falan.

 Zainab ta kalli Nusaiba tace “Nusaiba menene kuma?”

 Nabila tana dariya tace ” saboda wanda take dakon sanshi baisan tanayi ba, ya tafi batamai sallama ba.”

 Zainab ta kalli Nusaiba wacce ke kokarin jawo Nabila.
 Tace “wai dama da gaske kike? Lalai.”
 Ta kalli Goggo wacce ke kallansu tana cin cincin.”

Nusaiba ta kalla tace “Nusaiba kin wuce kin zauna ko kuwa? Ke kuma in sake jin bakinki.”
Ta fada tana kallan Nabila.
Wucewa tai ta zauna, Nabila tai kitchen, Zainab ce ta kalli Goggo tace “Goggo an tashi lfy?”
“Lafiya kalau, sun tafi makarantar.”

 Zainab tace “oh nama dan sha’afa.”
Ta fada tare da wucewa daki, tana bude kofar dakin tace “Nabila.”
Nabila data sha ruwa ta taho da sauri ta bita dakin.

 Zainab na zaune a bakin gado ta shiga.
 Zama tai kusa da ita tace “Aunty!”
Zainab ta juyo gaba daya ta kalleta yanayin fuskarta ne ya canzs zuwa tausayi, Nabila tace “Aunty daina, daina kallo na haka.”

 Zainab ta kamo hannunta sannan tadanyi murmushi tace “Nabila nagode.”

 Idanunta ne suka ciko amma fuskarta na kokarin bayyana murmushi tace “karki damu Aunty kedai kiyi kokari ki cigaba da zama cikin farinciki, shikedai ne abinda nake nema kuma na tabbatar Mama da tanada rai abinda zata nema kenan.”

 Zainab ce tai murmushi tace “sai kace kece babba.”
Nabila tai dariya tace “in na nuna miki na girma sai hankalinki yafi kwanciya.”

 Zainab ta jawota ta rungumeta tace “in wani abu ya faru ki kirani kinji?”

 Nabila ta goge kwallarta tace “To Aunty.”
Zainab ta dagota tace “Dady fa? Yana nuna miki banbanci?”
Kai ta girgiza tace “bansa a kaina ba bare na gani.”
 Zainab tai dan ajiyar zuciya tace “in an kusa visiting kimin magana zanzo muku.”

 “Kin tabbatar? Kinsan zaku hadu da Dady da maman Nusaiba?”
Wannan damuwarsu ce insun gani sa tafi, inata kin zuwa miki saboda banasan kisan meke faruwa amma tunda kinsani banga abinda zai hanani ganinki ba.”

 Nabila tai dariya tace “Shikenan zan kiraki.”

 Jakarta ta zuge ta dauko kudi, mika mata tai dubu goma tace ke biyar Nusaiba biyar, Nabila ta amsa tace “mungode.”
 Zainab tace “in kara miki?”

 Nabila tace “a’a abubuwa sun miki yawa, Aunty wai haka zaki cigaba da zama komai kece keyi?”

 Murmushi tai tace “yana neman aiki, sannan banajin wani abin dan nayi komai, na tabbatar saboda hallarcin danamai bazai taba cin amana ta ba kamar wani wanda baisan hallacci ba.”

 Nabila ta sake dariya tace “dukda bansani ba nasan da Dady kike, wai dan Allah meya faru takamaimai.” 

 Zainab ta mike tace ” zan fada miki amma ba yanzu ba.”

 Nabila tadan turo baki tace “shikenan.”

 Dariya Zainab tai tace “borin ya motsa ne?

 Nabila tai dariya itama tace “Aunty Allah ki dinga rufe kitchen dinki lamarin ciye ciyen goggo yayi yawa, ke kina can kina aiki danta na tsinanen bacci da jin dadi ita kuma sai ci da tsinanen kallo.”

 Zainab ta dan bige kanta kadan tace “wayace miki ana maganar manya haka? Kuma mamar Adam kamar mahaifiyata take.”

 Nabila tadan tabe baki.

 Zainab ce ta mike ta bude drawer dinta, agamfa ta dako irindaya guda biyu da mayafinsu, tace gashi, sannan ta dauko jaka guda biyu suma iri daya.

 Nabila tace “yaushe kika siya?”
Dariya tadanyi tace “duk sanda na samu naje siyayya ina siyowa saboda nasan zakuzo.”

 Nabila cikin jin dadi tace mungode.
 Da gudu ta bude kofa tana kiran Nusaiba, man Nusaiba ta zo sukaga kaya suka hau murna…….


 Adam kam tun bayan daya ajiyeta jikinsa a sanyaye ya dawo gida, shikansa baisan meya sameshi ba.

********


Gudu yake harya isa Danbatta, yana zuwa ya tada Abba a kwance akan gado a Er amma ba kowa a gunsa sai wata nurse, hankalin Khalid a tashe ya nemi number nan ya kira, Sabir ya dauka ya sanar dashi Zee ce ta bashi number din.
 Nan ya ce gashinan zuwa, Umma kuka kawai takeyi, Asiya ma haka, shikam Abba gaba daya da alama baisan waye a kanshi ba sosai, sai jini dake zuba a ta kasan inda akamai aikin, Sabir na zuwa ya sallamesu waje, nan ya fara aikinsa na ganin ya daidaita abinda ke faruwa.

 Shikam Khalid na zaune kusa da Umma, Asiya na gefensa.

 Salmanu ne yace 鈥渂ari naje na dawo Khalid.鈥�

 Khalid ya mike yace nagode Salmanu.
 Nan ya wuce, Umma ce ta kalleshi tace 鈥渁 ina ka sanshi?鈥�
Yace 鈥渨acce nakewa aiki ne taban numbersa ta sanshi ne.鈥�

 Umma tace 鈥渁mma mungode mata da alama mutumiyar arziki ce, Allah ya biyata.鈥�

 Khalid yai murmushi a kasan ransa yace 鈥渄a alama kam.鈥�

 Sun dade kafin Dr Sabir ya fito, sanar dasu yai ba matsala sai dai ya samu barci abashi ya huta.鈥�

 *********

 Shigowa Adam yai Gogo ce kadai a falan tana ta cin cincin dinta, Adam ya kalleta ya zauna a kusa da ita, kallansa tai tace 鈥淪allamar kenan?鈥�

 Yace 鈥渘ayi kina ta kallo ina zakiji.鈥�
Harara ta maka mai tace 鈥渒ai ka sani, ka kaitan?鈥�
Yace 鈥渆h sai ta gama zata kirani.鈥�

 鈥淶adai ta gama yau ta kama gabanta ko?鈥�

 鈥淓h gobe zata tafi.鈥�
Tace 鈥渁h to dan ni bansan bikin nan ya tashi tana gidan nan.鈥�
Meyasa?
Tace 鈥渢ambaya kake? Wayasan me zata sata in ba kowa a gidan? Ita waccen tana aiki, ni ina hidimar biki kai kuma kana can kana uban bacci.鈥�

Dariya yai yace 鈥淕oggo kenan.鈥�
Karar shigowar mota sukaji yace 鈥淶ainab ce?鈥�
Tace 鈥渋ta tana daki da yara sai dai mai daukan nasu ne kila.鈥�

 Adam ya leka yace 鈥渙h shine kuwa.鈥�

 Nan ya wuce daki ya sanar dash.

 Kayan suka nunamai ya tayasu murna sannan suka fita dan kara shiryawa.
Zainab ta kalleshi, karasowa yai ya rungumeta tsam a jikinsa.
Murmushi tai tace 鈥淗oney.鈥�
Yace 鈥淚na sanki Honey harbansan yawan adadinsa ba, nagode da kasancewarki cikin rayuwata.鈥�

 Murmushi tai ta dago ta sumbaceshi tace 鈥渘ima nagode da shigowarka cikin rayuwata.鈥�

 Tare suka fito, Zainab tai kitchen, gani tai anyi abinci, murmushi tai ta deba ta zuba ma wanda zai kaisu sannan ta kira Nusaiba ta mikamai, itama ta zuba kadan taci.

 Nan su Nabila sukai sallama, suka shiga mota.

 Nabila tace 鈥淕oggo asha biki lafiya.鈥�
Goggo tai dariya tace 鈥渢o, kuma kusha makafanta lfy.鈥�

 Nan suka kara sallama suka tafi tare da fatan Allah ya saukesu lafiya.

 Zainab ta bisu da kallo kafin tace 鈥淗oney ajiyeni a office.鈥�
Yace to.
Nan ta shiga suka tafi………..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button