NOVELSUncategorized

A GIDANA 17

Inalilahi wa ina ilaihi Raji鈥檜n yanzu abinda na rubuta jiya wata tacemin irin abinda ya faru da kanwar babanta kenan, Ya Salam, mace sai tai amfani da danka ta cuceka, dan Allah mata mu gyara halayenmu, bawai dan kinasan auran namiji sai kin shiga jikin matarsa kin cutar dasu ba, mata mu yima kanmu fada dan Allah, dama namiji ansanshi da sankai da kuma tunanin ya isa da kuma yanada dama, amma mata mu dinga duba rayuwar 鈥榶a鈥檡an mu, in har mu munci riba in aka ci riba akan namu 鈥榶a鈥檡an ya zamuji?


Allah ya sa mu gane Ameen, jin kalaman yarinyar nan ya tadamin hankali, domin su a wannan lokacin kanwar baban nata na nan, abinda ta haifa ya koma ita kuma auren daga baya iyaye rabawa sukai.

 Allah ya karemu daga sharrin Zuciya…..
Ameen.


*Shafi na Sha Bakwai*


Asalin Labari…….

 Zuwaira Muhammad Kabo shine sunan mahaifiyar Zainab, mahaifanta yan garin Kabo ne sai dai aiki ya daukeshi ya kaishi garin Gombe inda ya tare da iyalansa.

 Yaransa guda shida, biyu mata uku maza, Zuwaira itace yar fari a gidansu, Zuwaira yarinyace wacce ta taso mai sanyi dan ko kananta neman raina ta sukeyi saboda sanyinta, kaninta mai bi mata a duk sanda aka mata abu shine yake zakewa ya amshi fadan, ko a gidansu bata taba neman kananta suyi aiki, harsai mamanta haushi ya kamata ta sa su yi da kansu.
 Alhaji Muhammad Kabo ba mai tulin wadara bane sai dai Allah ya bashi rufin asiri inda yake zaune cikin gidansa hankalinsu a kwance.

 A lokacin da Zuwaira ta gama secondary ta fara neman makarantar gaba da secondary Allah ya hadata da Aliyu wanda ya ganta a hanya, da farko bata amince dashi ba saboda tsananin shiru shiru da hakurinta, sai dai ganin yanda yake tsananin santa ne yasa hartake dan tankawa.

 Soyayya mai karfi ce ta shiga tsaninsu wanda duk rashin magana irin na Zuwaira sai da kowa ya fahimci tsananin san da takemai.
 Haka aka hakura da neman karatunta akan intai aure ta cigaba.
Aliyu yana aiki ne agarin Kaduna inda yake aiki a harkar wuta, wato NEPA, iyayensa yan garin Gombe ne, Aliyu nada babban family sai dai irin zuri’ar nan ne da ba ruwan wani da wani, saboda matan gidansu hudu, kowa da ‘ya’yansa, kowa nada san kansa a haka suka taso, kowa baisan taimakan dan uwansa, gashi shima mahaifin bai damu dasu ba sabods yawansu.

 Ansa bikin Zuwaira da Aliyu, anyi biki lafiya ta tare a gidanta daya kama haya a garin kaduna.
 Zama mai tsafta sukai a tsakaninsu, duk da Aliyu nada saurin fishi da fada sai dai sanyin Zuwaira da hakurinta yasa Zamansu yin tasiri, domin ko ba ita tai abu ba inya fara fada hakuri take bashi, wanda hakan yake sawa dole yai hakuri.

 Zuwaira shekararta daya ta haifi danta namiji, sai dai kafin suna Allah ya dauki abinci, ta sake samun ciki a lokacin tana shekara ta biyu da aure, sai dai kafin cikin yai girma ya bare.
 Wannan lamari ya tada hankulansu, anyi ta dirka mata magunguna na gargaji tayi tayin na asibiti dan sai datai bari uku Allah ya bata haihuwar Zainab, Zainab ta kasance yarinyar da aka samu dakyar wannan dalili yasa Zuwaira da Aliyu suka dauki san duniya suka sa mata.

 Sati biyu da haihuwar Zainab aka karama Aliyu matsayi sannan aka mai transfer zuwa Abuja.
Wannan kamari ya kara musu dadi, farinciki haryana neman yi musu yawa.
Sun koma garin Abuja cikin ni’ima da daukaka, abin al’ajabi shine tunda suka koma Abuja matsayin Aliyu ke karuwa, tun suna gida mai daki biyu suka sai gida makeke mai hawa biyu.

 Aliyu na tsananin jin dadin wannan rayuwa da suka tsinci kansu a ciki, sai dai Zuwaira a hankali damuwa ta fara mamayeta ganin har yanzu ko bari bata sake ba ga Zainab har ta shiga primary.

 Tunda Zuwaira tazo garin Abuja batada takaimai mai kawa saboda ita dama bamai shige shige bace.
 Kamar yadda ta saba in Zainab ta tafi makaranta tagama gyaran gida sai ta daura abinci, tanayi tana dan kallanta ko kuma tana jin radio, wannan rana haka tana girki gefenta dan radio ne tanajin labarai, ganin abincin ya kamalu ne yasa ta kashe miyar sannan ta kwashe shinkafar.
Tana cikin hada cucumber salad wanda aka gama koyawa yanzu a radio taji motsin mota, murmushi tai dan tasan an dawo da Zainab kenan.
 Zainab ce ta shigo da gudu har tana neman faduwa, da sauri Zuwaira ta dagata tace “yar gidan Ummy karkije ki fadi.”

 Cikin tsananin zumudi tace “Ummy an bamu sabuwar Teacher.”
“Haba? Yaushe?”

“Hmmm yau din nan.”
Dariya Zuwaira tai tace “lalai da alama Zainab na san sabuwar teacher din nan?”

 Cikin jin dadi tace “eh sosai sosai, Ummy kizo gobe na nuna miki ita.”
Dariya Zuwaira tai tace ” abin harya kai haka?”

 Tace “eh tana dariya.”

 Kayanta ta canja taci abinci ta wuce islamiya, tana dawowa Dady na nan, tana shigowa gida kafin tai ko sallama ta ruga tana cewa “Dady yau an banu sabuwar Aunty.”
Dady ya kalleta da gudu ta karaso ta hau cinyarsa tana cewa “Dady an bamu sabuwar Aunty.”

 Dady yasa dariya yace “Ummy ta fadamin, lalai Zainab naji da wannan Auntyn.”

 Dariya tai tace “gobe kazo muje na kaika ka ganta.”
 Ummy ta kalleta tace “sankai, akace ni za’a fara kaiwa?”
Dariya sukai nan suka shiga hira har dare yai.

 Da safe Zainab ana shiryata ta tubure akan lalai itafa sai Ummy da Dady sun kaita makaranta sunga Auntynta, duk yanda Ummy ke lalabata bata bar kuka ba.
Dady ya dauketa yace “yi shiru yar gidana muje muga Auntyn nan.”

 Ummy ta zura Hijab dinta suka shiga mota tare, driver ya taho shi kadai dan ya maida Ummy, tunda daga makarantar Dady zai wuce.
 Suna isa tana sauka daga cikin taxi, tsallako titi tai Zainab na fitowa cikin murna tace “Ummy gatacan.”

Taci gayu sosai kai bakace malamar makaranta bace,聽 sanye take da doguwar rigar atamfa fitted gown wacce ta zauna mata tsam a jiki, mayafi ta yafa a saman kanta tana rike da takardun ta, ta rataya hand bag dinta.

聽 Ummy ta kalli Zainab tace “ya isa haka nan inta iso sai ki mata magana.”

 Dady ne ya karasa fitowa daga mota, daidainan ta karaso, fuskarta a sake take sosai harta karaso gun, cikin fara’a tace “Zee.”
Da gudu Zainab ta karasa ta rike hannunta, tare suka karaso gun.
 Dady ta kalla sannan ta kalli Ummy, cikin fara’a ta gaisheta, Ummy ta amsa cikin nuna farinciki.
Dady ta gaisar, ya amsa yana cewa “shikenan hankali ya kwanta?”
Fuskarta dauke da tambaya ta kalli Ummy tace me?
Ummy tai dariya tace “tun jiya aka dage sai munzo munga sabuwar Aunty.”
Fara’arta ce ta karu sosai ta kalli Zainab, Dady yace “tanada san mutane, sannan da alama kinada saukin kai hakan yasa take sanki sosai.”

 Murmushi tai tace “bakomai ai da na kowa ne.”

Ganin yara duk wanda yazo indai a class dinsu yake zai nufota ne yasa sukai sallama suka tafi.

Ummy ta koma gida shikuma ya wuce gun aiki.

Da daddare suna kwance a daki kamar masu bacci Ummy tace “da ace matar nan zata yadda da ita ta taimakama Zainab da lesson din, naga sam basa shiri da Auntyn da take zuwa yanzu.”
Dady ya juyo yace “nayi wannan tunanin dazu nima, toko zaki bita ko zuwa karshen satin nan ne ki tambayeta?”

 Ummy cikin gamsuwa tace to.

 Sati na zuwa Ummy taje da kanta, ba wani dogon nazari ta amince da hakan wanda yasa Ummy jin dadi.

 Sai ya kasance duk asabar da lahadi Aunty Basma na zuwa gida tana koyama Zainab karatu.

 Lokacin da abu ya fara faruwa.
A koda yaushe Dady yana zama a gida ranar asabar da lahadi, yana hutawa saboda hidmomi.
 Yanda yake jiyo dariyar Zainab daga sama ne yasashi kallan Ummy yace “da alama wannan matar tana san Zainab dayawa.”
Ummy tai murmushi tace kana ganin nima yanzu nayi kawa bayan malamar Zainab?

 Mikewa yai yace “bari naje naga yanda ake karatun.

 Ummy batare da wani abu ba tace ya kamata, mikewa yai ya sauko kasa, bangaren da yake na Zainab ne knda take wasa da kuma inda ake koya mata karatu ya nufa.

 Kofar a bude take, yana lekawa yana suna wasan hide and seek, Zainab ta dage tana nemanta.

 Tsayawa yai yana kallan ta yana murmushi, Aunty Basma ce tamai alama dayai shiru, Zainab tana neman Aunty ta cafko Dady.”

 Tana bude ido taga Dady shagwabe fuska tai tace “dady kuma?”
Dariya yai yace “nidin ne sai akai me?”
Dariya sukasa gaba daya, ido ya zubawa Basma wacce ke sanye da riga da skirt na material silk ya kamata dam, ga kanta ba dankwali, maida kallansa yai kan Zainab yace “ayi karatu.”
Ya juya, wajen magrib tai sallama akan zata tafi.
Dady yace “bari na saukeki dan zan fita nima.”
Ummy tace “Basma ki tsaya ya saukeki.”
Kallan Ummy tai tace “ina fita zan samu taxi.”

 Ummy tace “ga sauki hankali a kwance?”
 Godiya tawa Ummy wacce ta dauko mata turare da man shafawa ta bata, tare suka fito dukansu suka mata sallama Dady da Basma suka tafi.

 Suna tafe a hanya ake ta famar damunta a waya, kallanta yai yace “ki amsa mana!”
Kallansa tai tace “in amsa ince me?”
Yace “in bakyasan amsawa sai ki kashe wayar.”
Juyowa tai ta zubamai ido, yanda take kallansa ne yasa ya gangara gefen titi, kallanta yai yace “menene?”
Tace “bakomai.”
Kallan na menene to? 
Tace “kawai ina tunanin yanda zanji in nai aurene? Saboda wannan zamanin daga zarar mace ta girma an dinga magana kenan.”

 “Kinada kyanki ba masoya kika rasa ba meye naki na damuwa?”
Shiru tai batace komai ba…………
Tin daga wannan rana lamari ya fara baci tsakanin Dady da Basma, Ummy har ta fara tunanin kamar yanda yake kallanta bai dace ba, sannan irin shigar da takeyi ta fara damun Ummy.

 Sai dai taya zatai magana? Matar da bata iya magana duk yanda aka muzguna mata?

 Yanda take nunawa Zainab so kuwa inka ganta sai a dauka itace mahaifiyar tata.

 Kwatsam wata rana Basma tazo ta dauke kafa, a makaranta ma ta ajiye aikinta, Ummy ta fara damuwa saboda a lokacin kawayene su duk da daurewa take.

 Ganin ba labarinta yasa Ummy da Zainab wacce ta dameta da zancen Aunty sukaje har gidanta, a lokacin Dady yayi tafiya saudiya.
Sanda sukaje akace ai batanan tayi tafiya.
Ummy suka fito suka koma gida, Dady na dawowa daga saudiya ya canza gaba daya, ko zama a gida bayayi bare yai wasa da Zainab balle har suyi yar hira da Ummy.”

 Wannan hali daya tsira ya tada hankalin Ummy gashi a lokacin Allah yaima mahaifiyarta rasuwa, dakyar ya barta taje gombe tai kwana uku, sam yanzu zaman nan baya mata dadi, komai ta tambaya da fada yake amsa mata gashi sai sunyi bacci ma yake dawowa

Rana kwatsam Basma ta aiko mata da katin bikinta.
Ummy tai ta murna ta kirata a waya tana tayata farin ciki.
Ansa biki wata shida a wannan lokaci Zainab tana shekara tara.
Har gida Ummy taje ta tadda anata gyara musu gidansu, ga kayan lefe nan na gani na fada, Basma yanda ta karbesu ne yasa jikin Ummy yai sanyi, yau ko yanda ta saba jan Zainab a jiki batai ba.

 Sai dai Ummy ta mata uzuri akan bakin dake gidan ne.

 Haka suka koma gida su biyu wanda yanzu haka suke yininshi.

 Ana sauran kwana biyu biki Dady ya shigo gida da wuri, murna Ummy tai tayi, sukaci abinci tare y zauna yana duba homework din zainab har lokacin baccinta yai.
Kallan Zuwaira yai fuska a tsuke yace “dama fada miki zan na sai gida a can kusa da gun aiki na.”

 Cikin farin ciki tace masha Allah, kai Allah ya sanya alheri.
Jibi zan kara aure.
Kafin ta gama rufe baki wannan kalmar ta daki kunnenta.

 Kallansa tai da sauri tace “me?”
Yace “aure zanyi sannan nan da kwana biyu za’a daura.”

 Sake baki tai ta kalleshi, mikewa yai zai wuve daki, da sauri tasa hannu ta riko rigarshi tace “haka ya dace miji ya sanar da matarsa zai kara aure? Haka addini ya koyar? Meyasa wani sa’in san zuciya ke neman mantawa da abinda ya dace?”

 Hawaye ne suka zubo mata, ta dago ta kalleshi tace “zan hanaka aure ne bayan kayi niyya? Amma haka ya dace………”

 Zuciyarsa ce tadan raunana, da sauri ya dagota ya rungume yace “kiyi hakuri.”

 Hawaye ne suka shiga zubo mata, sai dai san zuciya irin na namiji wai sai ce mata yai yaje gun wacce zai aura tundazu yakejin sha’awa, haka ya biya bukatarsa tana hawaye……

 Dady y canza gaba daya ta kasa gane kanshi har tunani takeyi anya shine mutumin data sani da??????

A ranar bikin basma ya kasance ranar bikinsa hakan yasa Ummy ta aika mata da sako a waya akan bazata samu damar zuwa ba.

 Haka ta zauna ita kadai a gida babu mai mata tausar kirji, Zainab a wannan lokaci itama duk ta canza saboda ganin yanda mahaifiyarta take cikin damuwa, ga gida ita kadai.

 Tunda aka daura auren Dady bai taka kafa yazo gidansu ba har sai dayai wata biyu, a lokacin Ummy tanata fama da rashin lafiya saboda ciki, wanda ita kanta bata sani ba, ta dauka damuwarta ce yasata shiga wannan hali.

 Gaba daya Ummy ta zabge, Zainab duk ta canza itama, inta dawo gida sai dai ta zauna kusa da mahaifiyarta, anan take cin abinci suyi bacci tare, Ummy na kokarin daurewa dan ta nunawa Zainab ba abinda ke damunta.

Sai dai Zainab tun tana daukan wayar Ummy ta kira Dady ana kashewa harma ta hakura ta daina.

 Ummy kam ganin amai yaki karewa gashi intai abinci dakyar take iyaci yasa tai tunanin zuwa asibiti.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button