NOVELSUncategorized

A GIDANA 18

Page 18

Yau watansa biyu kenan bai tako cikin gidan ba sai dai yana aiko kudi yana kuma sawa akai musu kayan abinci.

 Yau Ummy ta tashi da wani irin zazzabi sai amai take kwarawa, da alama dadewar datai bata samu ciki na ga girma shiyasa cikin ke
wahalar da ita, tana zaune a falo, dauriya kawai takeyi saboda taga gaba daya hankalin Zainab ya tashi, jin sallama ne yasa Zainab tai tunanin driver ne datace inya dawo zai kai Ummy asibiti.
Tana budewa taga Dadynta, samun kanta tai kawai da fashewa da wani irin kuka.
Tausayinta ne ya kamashi don yana tsananin santa, juyawa tai da sauri ta shiga ciki.
Ya biyota shima cikin hanzari, cikin falo ta tsaya tace “Dady akai Ummy asibiti batada lafiya.”

 Kallan Ummy yai wacce jin sunan Dady yasata kokartawa ta mike ta kalleshi, nan Dady ya ga duk ta rame ta canza kamani, a hanzarce ya dauketa sukai asibiti su duka.
Anan ne yaji cewar Zuwaira nada juna biyu, aka bata gado akasa mata drip.
Sai dai me? Yana fitowa daga office din dr aka kirashi a waya, Zainab dake tsaye tana jiransa yazo taga yayi hanyar kofa cikin hanzari.
Kafin tai yunkuri har ya fice.
Da gudu ta fito amma ko motarsa babu, haka suka zauna a asibiti har aka sallamesu Dady bai kara ko lekowa ba.
Ummy ganin ta samu sauki ta cire komai a ranta saboda yar ta.
Sosai suke zama suyi hira in ta tafi skul ta zauna taita tunani, gashi ta kasa fada a gidansu, Zainab tun daga wannan rana bata sake daukan waya ta nemi Dady ba haka kuma bata karayima Ummy zancen ta kirashi ko baizo ba.

 Haka suka cigaba da rayuwarsu har cikin Ummy ya girma, Zainab murna kamar me akan Ummy zata haifar masu baby.
Zainab na shekara goma sha daya Ummy na wata tara.
Wannan rana ita tafi ko wace rana ciwo a tattare da Zainab, taje makaranta, tana dawowa ta tarada Ummy a yashe a kasan beni gaba daya kasanta jini ne ya mamaye da alama ciwo ne ya kamata tana hanyar saukowa ta mirgina, dan har gefen goshinta a fashe yake.

 Gaba daya jikin Zainab rawa ya fara, tama rasa me ya kamata tai, a hankali Ummy ta nemi data kira waya.
Jitai kanta na juyawa ganin jinin dake kasa, sai da Ummy dakyar ta kamo hannunta, firgita tai sannan  ta dauko wayar a falo ta kira Dady, gaba daya ba a hayyacinta take ba, mai makon ya dauka muryar mace taji tace “hello.”
Da sauri ta kalli Wayar sannan tace “Dady dady yazo Ummy…..”
Kashe wayar akai, ganin yanda Ummy ke numfashi yasa ta fita da gudu ta kora driver dinsu.
Haka aka dau Ummy akai asibiti, ana zuwa aka kaita dakin tiyata, sai dai an cire baby amma jini yaki daina zuba duk yanda sukai yaki tsayuwa.
Ummy tai murmushi dakyar tace a kira Zainab.
Zainab ta shigo gaba daya haryanzu bata hayyacinta, Ummy ta kamo hannunta, Allah ne sai Zainab kadai sukasan me tace mata a wannan lokacin.

Mati driver wanda tsoro ya kamashi yasa yana kaisu asibiti ya nufi saban gidan Dady ya sanar dashi sune suka shigo dakin.

Ganin Ummy a kwance yasa dady ya nufeta jikinsa na bari, Zainab baya kawai tai ta sulale agun.

 Dady hankalinsa yai masifar tashi, ya nufi Ummy cikin sauri ya kamo hannunta, wasu hawaye ne suka zubo mai, murmushi tamai da kyar daga wannan murmushin ciwo ya rikice, nan ya shiga kokarin sa mata kalmar shahada, ganin yanayinta yasa ya fita da sauri.
Dr ya kira, sai dai kafin suzo Ummy ta cika…..
Allah yai mana cikawa mai kyau Ameen ya Allah.

Haka Basma ta dawo gidan Ummy da gatan cikinta, kannen Ummy sunzo gaisuwa aka bar kanwar Ummy a gidan wato Sauda, nan ta zauna har akai arba’in itama ta koma saboda iyalanta.

 Ansama Yarinyar suna Nabila, satin Ummy biyu da rasuwa Basma ta haifi Nusaiba.
Itama Basma tai kuka sai dai Allah ne kadai yasan kukan da takeyi.
Dady kam sai dayai sati ko kofa bai fita ba.

Haka Zainab ta taso, magana wannan inba ta zama dole ba bata yinta, duk yanda dady yaso su daidaita amma inaaa Zainab gaisuwa kadai ke hadata dashi.
In bata makaranta daki take daukan Nabila ta kula da ita.
Tundaga wannan lokaci Zainab tasa a ranta bazata taba bari Namiji ya zama shine yake da komai ba balle har yai tunanin dole ta zauna dashi, ba kuma zata taba bari mijinta ya wulakantata ba, a da auran ma tace bazatai ba.
Tayi karatu kamar zata kashe kanta dan a makaranta babu ko yarinya daya da take kawatar, saboda taga butulcin dake tattare da yarda da mutum.

Tundaga nan ta zama selfish kanta kawai ta sani bata tunanin kowa, abu in bai shafeta ba ko Nabila ba bata shigarshi.
Zama bai mata dadi ba a gida saboda ko ganin Basma tai da mahaifinta hango mahaifiyarta take a cikin jini.
 Haka zainab ta gama karatu na nemi aiki a kano saboda ta bar kusa dasu.

 Dady yaso hanata sai dai ba yadda zaiyi dan yasan bai isa ya hanata abinda tai niyya ba, Zainab ta dawo kamo gidan Aunty Saudah wato kanwar mamanta.
Anan ta fara aiki har takai matsayin da take a yanzu.
 Ta hadu da Adam ne a wata rana lokacin sunji daukan rahoto, tana sauri saboda bata mata ran da akai, tana parking din mota tazo fita shi kuma ya taho zai wuce.
 Bata sani ba ta budo kofar ta bigeshi, Adam wanda yake tafe yana waya ya danyi kara tare da kallanta.
Wani banzan kallo tamai tace “idan zakai wayar soyayya ka dinga kallan gabanka.”
Ta rufe mota ta fara tafiya, baki ya saki da sauri yace “Baby zan kiraki.”
Gabanta yasha yace “me kikace?”
Kallansa tai tace “kunne biyu gareka sannan baki daya ne dakai, ya kamata jinka yafi maganarka yawa, dan matsa ina sauri ne.”

 Tafiya tai wanda tabai Adam da baki a bude, kallanta yai sannan ya kalli zabgegiyar motarta a ransa yace “ah kin rika ne, ni ina nan na saki baki ina neman yanda zanyi ga wata wacce da alama ta jiku.”

 Juyawa yai ya tafi.
Washe gari yana zaune ya saka kwanan shinkafa da wake a gaba, takaicin cin shinkafar ya kamashi yace “Goggo wai dan Allah yaushe zaki mana yar dagedage nifa Allah na gaji dacin fara damai.”

 Radio dinta ta kashe tace “wato Allah wadan naka ya lalace, kana kwance kamar tsuma sai dai na baka kaci sannan har wai abincin ma sai ka zaba? Bayan duk ka cinye mana dan gadon mu agun dan islan karatun da kake.”
Adam yai dariya yace “karki damu na kusa samun aiki ina daga cikin office ina shan sanyin AC mai dadi, gefe kuma ga lemo nan in kurba inci naman kaza.”

 Goggo ta tabe baki tace “sai ka tashi daga mafarkin da kake ko wallahi tinkiyar can ta cinye.”
 Da sauri yaja kwanansa gabansa yace “in ta cinye ince me?”
“Ina na sani kaci kazar mana.”

 Haka ya fito bayan ya gama cin abinci suka tafi gidan abokinsa Ziyad inda suke kallo.

 Ana switching din tashar Muryar Arewa Adam ya ganta tana labarai( a lokacin labaran dare take)

 Ruwan dayake sha ya feso waje ya zuba mata ido, Ziyad yace “Masoyin Baby soyayyar ta motsa ne?”
Adam ya zuba wa Zainab ido ba tare da yace komai ba.
Haka ya kwana yana juya abin a ransa, ai kam washe gari ya nufi cikin kano, sai dai inda suka hadu jiya bai ganta ba.
Tambayar Station dinsu yai yaje.

 Tana tsaye cikin fada tanawa staff din gun fada akan聽 laifin daukan rahoto yanda ya kamata ta hangoshi ta glass, daga waje ya daga mata hannu.
Fitowa tai cikin mamaki tace “me kake anan?”
“Zuwa nai aban hakurin da ba’a bani ba jiya.”

Mamaki ne ya kamata, tace “hakuri?”
Yace “eh in baza’a bani ba aban number waya.”
Wani kallan banza tamai ta juya.

 Tundaga wannan rana kullum sai Adam yazo station dinsu, tun bata kulashi har yanda yake neman magana yake sata murmusawa.
A hankali ta fara fahimtarsa, ga saukin kai komai tace zaice to, a lokacin Zainab ta fara tunanin wannan ne? Dan dama so take ta samu mijin daya dace ta dawo da Nabila gunta.

 Adam yana santa so sosai a iya saninta, wanda har tausayin halin da yake ciki yake damunta, hakan yasa ta nunamai aiki zai samu tunda ko wata biyar basuyi da gama karatu ba.

 Soyayya mai karfi ce ta shiga tsakaninsu, Adam kanwarsa daya sunanta Sadiya kamar yadda muka sani, wacce ke zaune agun kanin Goggo, ganin Zainab ta samu wanda takeso yasa ta fara ginin gida.
Adam da kanshi ya dinga zama akan aikin har aka kammala….

 Tausayin mahaifiyar sa da za’a bari ita kadai sannan da tunanin aikinta yasa ta nemi su tafi da Goggo.

 Haka akai auransu dan ta fadamai abubuwa kadan daga rayuwarta, ya kuma nuna shi zai share mata hawaye.
Ta yarda da Adam tana kuma ganin duk duniya idan har akwai namiji daya dayake santa to lalai Adam ne.
Dady kam gaba daya yai sanyi dan tun mutuwar Ummy gaba daya ya canza, sai dai ba yanda zaiyi ya maida hannun agoggo baya, sosai yake san su dawo daidai da Zainab sai dai itakam inaaa matarsa ma kallo bata isheta ba.

 Ta nemi a bata Nabila amma Dady ya bata hakuri akan ta barta anan, sannan Nabilan itama tace tafisa nan saboda Nusaiba.

 Ganin karta sawa kannenta rayuwar kuncin da take binne dashi a ranta yasa bata taba tada zancen Ummy ba, Nusaiba da Nabila aka barsu a matsayin duka yayan Basma ne wacce itama dana sani da wulakancin da Dady ya fara mata ya dawo da ita hankalinta.

 Haka Zainab ta bar gidan sai dai ko waya bata taba hadata da mahaifinta, sai dai ta tambayeshi a gun Nabila, shima yana tambayar Nabila ya Zainab.

 Haka rayuwarsu take Zainab tunda ta fara aiki har wannan rana bata taka ko kofar gidansu ba.


Wannan kenan……….

{Mata wandanda suka sanar dani ta Pc da wadanda suki magana a grp akan auren cin amana da rabasu da mazajensu da akai suma, Allah ubangiji ya kara muku hakuri, ya ba mijinku ikon yin adalci a tsakaninku, ya kuma kareku da karewarsa Ameen.}

Allah yasa mu dace……….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button